✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Stephen Keshi na bin Hukumar NFF albashin wata bakwai

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta tabbatar kocin Super Eagles Stephen Keshi yana binta albashin wata bakwai.Shugaban Hukumar, Alhaji Aminu Maigari ya tabbatar…

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta tabbatar kocin Super Eagles Stephen Keshi yana binta albashin wata bakwai.
Shugaban Hukumar, Alhaji Aminu Maigari ya tabbatar da haka a karshen makon jiya a lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Haka su ma mataimakan kocin al’amarin rashin biyan albashin na tsawon wata bakwai ya shafe su.
Kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta fitar ta nuna cewa saboda matsalar kudi da hukumar take fuskanta a halin yanzu, hatta ’yan kwallon kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles abin ya shafe su don  an zaftare alawus din da ake ba su idan sun samu nasara a wasa daga Dala dubu goma zuwa Dala dubu biyar.
Sai dai hukumar ta ce tana yin duk mai yiwuwa ta ga ta faranta wa Keshi rai wajen biyan kudin Otel dinsa da kuma na abinci a kan kari.  Haka kuma hukumar ta ce ta samar masa da motar da yake zirga-zirga don tabbatar da harkokinsa na yau da kullum ba su tsaya ba.
“Ina so na tabbatar muku da cewa da yawa daga cikin ma’aikatan hukumar NFF yau kimanin shekara guda kenan ba su karbi albashi ba, don haka matsalar ba a kan Keshi kadai ta tsaya ba, kuma ma’aikatan sun cigaba da aiki don sun san halin da hukumar ke ciki.
Sai dai ya bayar da tabbacin nan gaba kadan idan abubuwa sun daidaita a hukumar za a biya kowa hakkinsa ba tare da bata lokaci ba.