✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sterling Bank ya bullo da tsarin tallafin karatu da aiki

Bankin Sterling Bank ya kirkiro da tsarin hada aiki da karatu ga dalibai da suka kammala sakandare ta hanyar bayar da tallafin kashi 65%. A…

Bankin Sterling Bank ya kirkiro da tsarin hada aiki da karatu ga dalibai da suka kammala sakandare ta hanyar bayar da tallafin kashi 65%.

A matsayinsa na cibiyar hada-hadar kudi da ta daje wajen samar da arziki da kyautata rayuwar al’umma, Banking Sterling, jagora kuma nagartaccen banki, na kara kafa harsashin samar da dama ga rukuni daban-daban na al’umma.

A ci gaba da kokarinmu na samar da da ilimi domin rayuwa ta gaba mai fannoni iri-iri, Sterling Bank ya kaddamar da tsarin “Grow With Sterling”.

Tsarin ya samo asali ne daga wani bangare na Sterlin HEART Sectors-Education, na da nufin bayar da gudunmuwa domin bunkasa ilimin matasa masu kammala makarantar sakandare.

Yakininmu na  cewa samar da ilimi shi ne jari mafi riba ya sa muka kulla yarjejeniya da Jami’ar Nexford da ke birnin Washington DC na Kasar Amurka domin daukar nauyin karatun daliban da suka kammala sakandare su samu digiri daga kasar waje cikin shekara uku.

Domin samun kwarewa a aikace kuma, daliban za su rika yin aiki a matsayi daban-daban a Sterling Bank a karkashin tsarin na hada karatu da yin aiki.

Sanarwar da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Sterling Bank Plc, Temi Dalley ta fitar ta ce, shirin na daga cikin tsarin bankin na samar wa ’yan Najeriya masu tasowa damar yin aiki da samun ingantaccen ilimi mai rahusa da kuma kwarewar aiki a aikace a lokaci guda.

Bankin zai biya akalla kashi 65% na kudin karatun daliban da ke cikin tsarin wanda hakan babban jari ne a ilimin ’yan Najeriya masu tasowa.

Dalley ta ce “tsarin Grow With Sterling’ tsari ne na hadakar tallafi da zai ba yara da suka kammala sakandare damar karo ilimi karkashin hadin gwiwar bankin Sterling da zai dauki nauyin karatun da kuma Jami’ar Nexford da za ta koyar da su”.

Wasu fa’idojin tsarin da ta zayyano sun hada da yi musu karin sauki na kashi 20% a kudin karatunsu, sai kuma yin rajista kyauta na halartar darussa ta intanet da dai sauransu.