Search
Subscribe
Su wa ke son wargaza Najeriya?

Su wa ke son wargaza Najeriya?

A 2015, shekaru hudu da suka gabata, GIZAGO (08065576011) ya gabatar da wannan tsokacin dangane da rikice-rikicen da suka yi wa Najeriya cacukwi. Daga dukkan alamu, al’amura ba su sauya ba, ana nan dai ’yar gidan jiya. Bari mu kara nazarin batun nan:

Tare da alhini da takaici nake bude wannan tsokaci mai take na sama. Tun ma kafin in gabatar da maudu’in wannan tsokaci, duk wani da ya kwana ya tashi, zai iya kirdadon abin da ya saka ni cikin takaici da alhini, musamman ganin cewa tatsuniyar gizo dai ba za ta wuce koki ba. A takaice dai kowa ya san yadda Najeiya ta zama wani dandali na zubar da jinin talakawa, wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Tun daga Jihohin Borno da Yobe, zuwa Filato da Kano da Kaduna. A shekarun baya kadan ma, har da wasu sassa na Jihar Neja, uwa uba da Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, kullum sai zubar da jini ake.

Kullum tambayoyin da ke kara-kaina a kwakwalen mabambantan mutane su ne, shin su wane ne ke samun farin ciki da nishadi wajen hallaka jama’a? Su wane ne kanwa uwar gamin da ke haddasa wannan ta’addanci? Shin me ke manufarsu da suka zabi su ruguza rayuwar mayawaitan al’ummar kasar nan? Ya zama dole ga mutanen da suke tofa wadannan mabambantan tambayoyi, domin kuwa barnar ta yi yawa.

Domin neman gamsassun amsoshin wadannan tambayoyi, masu tunani sun yi, masu hasashe sun yi, haka ma masu ba da amsa kai-tsaye sun ba da, amma duk da haka, har yanzu abin bai gamsar ba, ganin cewa har yanzu tu’annatin sai kara aukuwa take. Jami’an tsaro kuwa sai suka kasance cikin tsoro da kara haddasa tsoro ga al’umma, maimakon su ba da kariya da tsaro, kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Bari mu duba amsa ta farko, wadda ke ta’allaka wannan tu’annati ga dakarun Boko Haram da sauransu. Wannan kuwa a fili yake, musamman ganin cewa da zarar an samu tashin bam, musamman a Arewa, sai Kakakin Rundunar ’Yan sanda ya ba da sanarwar cewa kungiyar ce ke da ruwa a ciki, musamman ma a lokacin mulkin Jonathan. Idan muka fara lissafin tashin bama-bamai a Maiduguri da Damaturu da wanda ya faru a Hedikwatar ’Yan sanda da ke Abuja da wanda ya faru a ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja da wanda ya faru a garin Madalla a 2011, duk kungiyar ce ta dauki alhakin faruwarsu. Yanzu kuma da aka samu canjin gwamnati, ga shi nan an kai munanan hare-haren bama-bamai a jihohin Borno da Yobe da garuruwan Jos da Kano da Zariya.

Abin tambayar shi ne, to su wane ne ainihin ’yan Boko Haram? Domin kuwa har yanzu babu wanda ya fito fili ya ce sunansa wane dan wane, kuma shi ne jagoran kungiyar, tun bayan kisan gillar da aka yi wa shugabansu na farko, Muhammad Yusuf. Hatta shi kansa Shekau, akwai shakku sosai a kansa, musamman yadda a can baya hukumomin tsaro suka yi ta cewa ya mutu. Ke nan akwai yiwuwar cewa wadansu ne ke fakewa da kungiyar suna son cimma wata boyayyiyar manufa.

A wasu nazarce-nazarce da na gudanar, na ci karo da bayanai masu dimbin yawa, wadanda ke ba da amsa karara ga wannan abu da ke faruwa a Najeriya. A wannan nazari na gano wadanda suke gudanar da wannan tu’annati da wadanda suka daure gindi ake gudanar da shi. Ka fadi da karfi, ba wadansu ne masu wannan karkatacciyar akida da mugun nufi ba sai azzaluman duniya. Game da abin da suke nufin cimmawa kuwa, na gano cewa babban burinsu shi ne, su tarwatsa Najeriya, ya zamanto nan gaba an share sunanta daga doron kasa. Za mu ga karin bayani nan gaba kadan.

A wani littafi mai suna ‘Dajjal: The AntiChrist’ wanda wani kwararren malamin Musulunci na duniya, Ahmad Thomson ya rubuta. Ya tona asirin makiya al’umma, makiya Musulunci, azzaluman duniya. Haka kuma ya kira su da sunan ‘Masu Bautar Shaidan,’ wadanda ba su son ganin duk wata akida ko al’ada ta kirki tana gudana a duniya. Babu abin da suka sanya gaba sai duniya da bautar abin duniya. Domin cimma manufarsu, za su iya yin duk wani abu komai muninsa, kama daga tsafi, kisan kai da sauransu.

Wadannan karkatattun mutane, masu siffar shaidanu, sun yi sansani a manyan kasashen duniya. Su ne ummul haba’isin duk wata ja’iba da ke faruwa a sassan duniya. Tashin-tashina da bala’o’in da suke addabar kasashen Musulmi, kamar Iraki da Pakistan da Libya da Siriya da Masar da Afghanistan da sauransu, duk aika-aikar wadannan karkatattun azzaluman duniya ne.

Wani dalili da ya sanya na yanke hukuncin cewa wadannan azzalumai ne ke da alhakin tashe-tashen hankulan da suke faruwa a Najeriya shi ne, a can baya, wani daga cikin jami’an wadannan azzaluman duniya, ya taba fitowa baro-baro ya ce, Najeriya za ta wargaje, zuwa shekarar 2015. Tun daga wancan lokaci abubuwa rikitattu suka yi ta faruwa, wadanda suka hada da tashe-tashen hankali masu yoyo da kabilanci, siyasa ko addini da sauransu.

Ban gama fahimtar haka ba, sai da na karanta wata makala da wani kwararren dan jarida na duniya, mai suna Gordon Duff ya rubuta kuma aka wallafa a wasu jaridun kasar nan a 2011. A makalar tasa, wacce ya yi wa taken: ‘An Durfafi Tarwatsa Najeriya’ kamar yadda ya ce, ya rubuta ta ce a matsayin gargadi ga shugabannin Najeriya domin su dauki matakan da suka dace, don hana aukuwar wannan mugun kudiri na azzaluman duniya.

Idan mun dubi yadda a cikin kwanaki uku kacal, aka kai hari Jos, wurin wa’azin Musulunci da majami’a da yadda aka kai hari a masallaci a Kano, da yadda aka kai hari a Zariya wajen tantance ma’aikata (a lokacin), wannan ya isa ya nuna cewa al’ummar kasar nan kawai ake son hallakawa, Musulmi da Kirista.

Manufar wannan aika-aika ita ce, a haddasa gaba da kiyayya tsakanin al’ummar Najeriya, kamar yadda ake son raba mutane da ibada.

Har yanzu wadannan karkatattu fa ba su hakura ba, suna nan suna ta yi wa kasar nan kulle-kulle ta hanyoyi daban-daban don wargaza ta.

Muna rokon Allah, Ya kawo mana dauki a kasar nan, Ya yi mana maganin wadannan mutane da ke hallaka bayinSa. Allah Ya yafe mana zunubbanmu, Ya tausaya mana ba don halayenmu ba, sai don rahamarSa da jinkanSa. Allah Ka kawo mana dauki!

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin