✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sudan za ta rataye ’yan sandan leken asiri 27 kan kisan malamin makaranta

Wata kotu a Sudan ta yanke hukuncin kisa kan wadansu ’yan sandan leken asirin kasar 27 da aka samu da hannu wajen kisa da azabtar…

Wata kotu a Sudan ta yanke hukuncin kisa kan wadansu ’yan sandan leken asirin kasar 27 da aka samu da hannu wajen kisa da azabtar da wani malamin makaranta da daya ne daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnati a bara.

Kotun a karkashin Mai shari’a Sadok Albdelrahman ta ce jami’an an same su da hannu dumu-dumu wajen azabtarwa baya ga kisan wadansu fararen hula ciki har da kisan malamin makarantar, Ahmed al-Kheir, wanda jami’an hukumar suka kama cikin watan Janairun da ya gabata suka kuma hallaka shi a hedkwatarsu.

Kotun ta bukaci a aiwatar da kisa kan jami’an 27 ta hanyar rataya bayan hujjoji sun nuna yadda suka azabtar da tarin jama’ar kasar ta Sudan lokacin zanga-zangar wadda ta faro daga watan Disamban 2018.

Akalla mutum 177 aka tabbatar da rasuwarsu a hannun jami’an tsaron kasar Sudan yayin da wasu aka harbe su da harsashi a dandalin zanga-zangar bayan da tsohon Shugaban Kasar Omar Hasan al-Bashir ya bai wa jami’an tsaro cikakken ikon ladabtar da masu zanga-zangar.

Wasu majiyoyi na daban sun ce adadin mutanen da suka rasu a zanga-zangar sun haura 250.