✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sukar Buhari: Obasanjo ya dauko Dala ba gammo

‘Yan Najeriya sun ragargaje shi Mun karbi shawararsa da zuciya daya – Gwamnati Sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya…

  • ‘Yan Najeriya sun ragargaje shi
  • Mun karbi shawararsa da zuciya daya – Gwamnati


Sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi a wata wasika da ya fitar a ranar Litinin tare da shawartarsa da kada ya tsaya takara a zaben badi ta jawo muhawara mai zafi a tsakanin al’ummar kasar nan.

A cikin wasikar wacce Obasanjo ya aike wa manema labarai, ya caccaki Shugaba Buhari, sannan ya ce kamata ya yi ya bar mulki a 2019 ya je ya huta saboda yawan shekaru da yanayin lafiyarsa. Kuma ya lissafo wasu abubuwa da ya kira nakasu da kasar ke fuskanta wadanda ya ce a dalilinsu ne a zaben shekarar 2015 mutane suka fita kwai da kwarkwata suka zabi Buhari bisa yakinin zai magance wadannan matsaloli, “amma sai ga shi ba ta sake zane ba,” inji Obasanjo.

Cif Olusegun Obasanjo ya ce ’yan Najeriya sun yi tururuwar zaben Shugaba Buhari ne a 2015 saboda gazawar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta bangarori da dama, sai dai ya ce har yanzu ana fama da matsalolin da aka yi fama da su lokacin mulkin Jonathan ba tare da samun sauyi ba. Matsalolin da ya lissafo sun hada da rashin taka rawar gani wajen gudanar da al’amuran gwamnati da talauci da rashin tsaro da gazawa a fannin tattalin arziki, da bai wa na kusa da shi mukamai da sakaci wajen tafiyar da aiki. Sai kawar da kai yayin da ake aikata ba daidai ba da rashin hadin kan kasa da rashin tafiyar da siyasar cikin gida yadda ya dace da kuma karuwar bambance-bambance a tsakanin masu hali da marasa galihu.


Martanin jam’iyyun siyasa da kungiyoyi

A martanin babbar jam’iyyar adawa PDP cewa ta yi Obasanjo ya tabbatar da matsayin da ta dade a kansa cewa gwamnatin Buhari da APC sun gaza a kowane fanni. Sai dai ta ki amincewa da bukatar Obasanjo ta a kirkiro wata kungiyar siyasa inda ta ce: “Muna kira ga mutane da kada su yarda da kirkiro wata sabuwar kungiyar siyasa kamar yadda ake ta kira, maimakon haka gara su mara wa PDP baya don ta ceto su.”

Shugaban Jam’iyyar APGA ta kasa, Dpkta bictor Oye, kuwa cewa ya yi “Dokta Obasanjo bai cancanci shawartar Buhari kan kada ya sake tsayawa takara ba, kuma ya daina tayar da kura ba gaira ba dalili.”

A martanin Jam’iyyar APC ta ce har yanzu ita ce zabin da ya fi dacewa a wannan lokaci ga dukan al’ummar Najeriya kuma ta sadaukar da kanta wajen kawo ci gaba da bunkasar Najeriya.

Kakakin Jam’iyyar ta kasa Malam Bolaji Abdullahi ya fadi a martaninsa cewa, “yayin da ba mu amince da wasu batutuwa da tsohon Shugaban ya gabatar ba, musamman game da jam’iyyarmu da kuma gwamnati, mun lura da wasu kuma muna jin ya yi ne da kyakkyawar niyya.”  Ya  ce sai da ba daidai ba ne yadda tsohon Shugaban ya yi watsi da tsarin jam’iyyun kasar duka.

kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) ma cewa ta yi Cif Obasanjo ba ya da ikon da zai ce ga abin da Buhari zai yi game da tsayawa takara a zaben na badi.

Wata sanarwa da Kakakin kungiyar Muhammad Biu ya fitar, ta ce Shugaba Buhari ne kawai yake da damar yanke shawarar sake tsayawa takararsa a zaben na badi.

ACF ta soki Obasanjo da son sanya bakinsa a kowane al’amari har da wanda bai shafe shi ba.

Ita kuwa kungiyar Fulani Makiyaya ta Meyatti Allah (MACBAN) ta Jihar Nasarawa ta fadi ta bakin Shugabanta Muhammed Hussaini cewa, Obasanjo yana so ne ya maye gurbin Buhari da yaron gidansa da zai rika juya shi yadda yake so, don haka Shugaba Buhari ya yi watsi da shi ya sake tsayawa takara a badi.

dan Majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa kuwa cewa ya yi, muguwar manufar Obasanjo a kan Buhari ba za ta samu nasara ba. Ado Doguwa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce “Kalaman na Obasanjo na nunawa a fili yadda almundahana ke kokarin dawowa da karfinta, domin tsohon Shugaban kasar dan almundahana ne, ni na fadi haka.”

Sai dai wani mai sharhi kan harkokin siyasar Najeriya Dokta Abubakar Kari ya ce ya kamata a duba wasikar ta Obasanjo da idon basira musamman kan kura-kuran da ya ambata.

Ya shaida wa BBC cewa misali “Akwai mukamai da dama da aka bai wa wadansu da ake ganin suna da dangantaka ta jini ko auratayya misali Ministan Albarkatun Ruwa, ”

Ya ce yawancin masu fada-a-ji a Fadar Shugaban kasa suna da alaka da shi, sannan masu magana da yawunsa suna yawan dora laifi ga gwamnatocin da suka gabata. Ya ce saboda ana tunanin Buhari zai iya kawo gyara, wannan ya sa jama’a kin gamsuwa da uzurin gwamnatinsa.

Dokta Kari ya ce “cin hanci ya ragu amma kuma ba a daina ba.” Ya kuma ce “Ba a daina daukar ma’aikata ta bayan gida ba. Na kusa da shi suna cin karensu ba babbaka kuma ba abin da ake yi, ko abin ya fito fili ba ya daukar wani mataki. Hakan ya sa wadansu ke ganin anya Buharin ne kuwa?”


Buhari ya yi kokari

Sai dai Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce Buhari ya yi kokari idan aka auna matsalolin da ya iske da nasarorin da ya samu, kuma maganar sake tsayawa takara ba ita ce a gabansa. Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya aiko wa Aminiya shekaranjiya Laraba, don mayar da martani kan wasikara ta Obasanjo.

Ministan ya ce Obasanjo ya ce gwamnatin Buhari ba ta samu nasara a fannin tattalin arziki ba wanda shi ne na uku cikin jerin alkawurran da ta yayin kamfe. Ya ce, kila Ayyuka ne suka yi yawa wa Obasanjo “ya zamo ba ya  da sukunin fahimtar dimbin ayyukan ci gaban da gwamnatin Buhari take gudanarwa a yanzu musamman a fannin bunkasa tattalin arziki.”

Ministan ya ce dukan alkaluman da ake amfani da su wajen bayyana karfin tattalin arziki sun nuna cewa Najeriya tana samun ci gaba, kuma ta fice daga matsin tattalin arziki ne ta hanyar amfani da shawarwarin da wadansu ’yan kasar nan suke ba ta “Kuma hauhawar farashin kayayyaki ta ragu da kashi 15 cikin 100 a watanni 11 a jere,” inji shi.

Game da batun tazarcen Shugaban kasa kuwa, Minista Lai ya ce da gaske wadansu ’yan Najeriya suna kiraye-kirayen ya sake tsayawa takara, yayin da wadansu ke nuna adawarsu. “Muna ganin wannan batun zai iya raba hankalin Shugaban kasa a yanzu saboda ya dukufa a kowace sa’a don ganin ya magance dimbin matsalolin da suke ci wa kasa tuwo a kwarya kuma galibinsu gadonsu ya yi daga tgwamnatocin da suka gabata,” inji shi.

Sai dai ya ce ba su tunanin cewa Obasanjo yana da wata mummunar manufa kan wasikar sai dai ci gaban kasa. “Mun karbi shawarwarinsa da zuciya daya kuma muna gode masa kan yadda ya samu lokaci duk da dimbin ayyukan da ke gabansa ya rubuta mana wannan doguwar wasikar,” inji Ministan.

Cif Obasanjo ya taba aikewa da irin wannan wasika ga tsohon Shugaba Goodluck Jonathan cewa kada ya yi tazarce a 2015.

Sai dai kuma ba Cif Obasanjo ne kawai ya taba fitowa karara ya bayyana gazawar gwamnatin Buhari ba, an sha samun na kusa da shi da suka soke shi kan salon mulkinsa da suka hada da Fasto Tunde Bakare da Buba Galadima wadanda suna cikin jigogin da aka kafa Jam;iyyar APC da su, kuma na gaba-gaba wajen fafutukar ganin Shugaba Buhari ya samu mulkin Najeriya.

Matarsa A’isha Buhari ma a karshen shekarar 2016 a hira da BBC Hausa <http://www.bbc.com/hausa> ta ce, wadansu ’yan tsirarin mutane sun mamaye gwamnatin mijinta, inda suke hana ruwa gudu.