✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sulhun da gwamnoni ke yi da barayin shanu bai dace ba – Shehu Aljan

Shahararrar mai kama barayin shanun nan Alhaji Shehu Musa Aljan ya ce sulhun da wadansu gwamnonin Arewa ke yi da barayin shanu ko masu garkuwa…

Shahararrar mai kama barayin shanun nan Alhaji Shehu Musa Aljan ya ce sulhun da wadansu gwamnonin Arewa ke yi da barayin shanu ko masu garkuwa da mutane bai dace ba.

Alhaji Shehu Aljan ya bayyana wa Aminiya haka ne a yayin da ya yada zango a garin Zariya tare da wasu dubban shanu da tumaki da awaki da bindigogi da wadansu mutane da ake zarginsu da satar shanu da kuma garkuwa da mutane da ya kama.

Alhaji Shehu Aljan ya ce sulhu da barayin bai dace ba domin, “Ba a sulhu da barawo, domin wadansu gwamnoni sun gwada sun gani.”

Aljan ya ce idan sulhu na gaskiya ne to wadanda aka yi sulhu da su dole su bi ka’ida yadda sulhu yake kamar dawo da dukkan wani makami nasu da duk wata saniya da suka sata tare da sako mutanen da suke garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba, “Duk sulhun da ake yi a ina ka ga an yi haka? Kuma an fasa aikata abin da ake aikatawa? Ka ga dai abin ya faru a Katsina da Zamfara, don haka abin da ya dace shi ne a karfafa wa jami’an tsaro a samar da masu amana masu kishin kasa da kuma mu ’yan sa kai,” inji shi.

Shehu Aljan ya yi kira ga masu rike da sarautun gargajiya su daina sa kansu a cikin badakalar masu satar shanu domin kare mutuncinsu. Ya ce kusan duk inda suke gudanar da aiki sai ka ga irin wadanda aka kama ake zargin da satar wadansu iyayen kasa ke zuwa don a ba da belinsu.

Shehu Aljan ya ce ya kamata gwamnati ta dauki matakai wajen sa ido a kan makiyaya da ke ketarowa daga kasashe da suke makwabtaka da Najeriya, inda ya ce rufe kan iyakoki ya yi matukar tasiri wajen takaita shigo da makamai a kasar nan, don haka ya ce ya zama wajibi a sa ido a kan duk wani makiyayi da ke shigowa don yin kiwo a Najeriya.