Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sun koka da tsarin shugabancin kungiyarsu

Wasu daga cikin mambobin qungiyar

Wasu jiga-jigai da mambobin kungiyar masu cinikin kayan gwangwan na kasa sun koka da salon tsarin shugabancin kungiyar, inda suka nemi shugaban kungiyar tasu, John Egaji da ya yi murabus suka kuma yi kira ga daukacin mambobin da su tsayar da bada kudaden shiga na kungiyar har sai an kai ga nada sabbin kwamitin amintattu na riko, wadanda zasu jagoranci shirya zaben sabbin shugabannin kungiyar.

Babban Sakataren Kungiyar na Kasa, Steben Johanna ne ya shaidawa ‘yan jaridu hakan, bayan taron da ‘ya’yan kungiyar suka yi a ofishinsu dake Kasuwar Kwali a Ojota na Legas.

ADVERTISEMENT

A cewar sakataren, mambobin kungiyar sun kosa da tsarin mulkin kama-karya na shugaban nasu John Egaji wanda ya shafe shekaru 17 yana jagoranci, “ya yi shekaru 17 yana jagorancinmu ba tare da ya tsinanawa kungiya ko masu sana’ar gwangwan da komai ba, sai dai handame kudaden shiga na kungiya, sannan ya tattaro ‘yan uwansa da iyalan gidansa ya ba su manyan mukamai a kungiyar, wannan ne yasa muka bi duk hanyoyin da doka ta tanada domin mu dakatar da shi, mun shigar da kokenmu ga ma’ikatar dake kula da kungiyoyi da ma’aikata wadanda suka tura masa sammaci tare da hana shi shirya zabe, amma ya bijire wa umarnin ma’aikatar ya shirya kwarya-kwaryar zabensa a karshen watan da ya gabata, yanzu haka mun shigar da kara a kotu, kuma muna shawartar dukkan mambobinmu da su dakatar da baiwa wannan kungiya haraji har sai an kafa kwamitin riko na amintattu,” inji shi.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar, Alhaji Auwalu Soja Sarkin ‘yan gwangwan na Yamma, ya shaidawa Aminiya cewa sun dauki duk matakin da doka ta yarda da shi wajen kawo karshen mulkin kama-karyar, “don haka muke kira ga jama’armu masu cinikin gwangwan da su daina baiwa kungiyar kudin shiga har sai an kai ga yin zaben sabbin shugabanni. Sannan muna kira ga John Egaji ya nuna dattako ya sauka ya baiwa doka damar yin aikinta,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta tuntubi shugaban kungiyar wanda ‘yan kungiyar ke korafi a kansa wanda ya bayyana cewa shine asalin wanda ya kafa kungiyar  wacce ta samu takardunta a cikin shekaru 6 da suka gabata, “mun yi zabe a karo na farko na kammala zango na na farko, sannan mun sake shirya zabe a ranar 31 ga watan da ya gabata, inda na sake lashe zaben. Saboda haka ma’aikatar dake kula da kungiyoyi ba ta da ikon dakatar da wannan zabe, domin kotu ta sahale mana shirya wannan zabe tun da farko,” inji shi.

Ya kara da cewa, ‘yan kungiyar dake hamayya da shi su jira hukuncin da kotu zata yanke, tunda maganar na gaban kotu a halin yanzu, ya ce kuma a shirye yake ya zauna da mambobin kungiyar domin lalubo bakin zaren lamarin a warware shi.