✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sun sha alwashin bunkasa kananan hukumomin Ngaske da Yawuri

Sabon Shugaban karamar Hukumar Ngaske da ke Jihar Kebbi, Alhaji Mamuda Muhammad Warra, ya ce zai mayar da hankali wajen samar da ingantattun hanyoyi tare…

Sabon Shugaban karamar Hukumar Ngaske da ke Jihar Kebbi, Alhaji Mamuda Muhammad Warra, ya ce zai mayar da hankali wajen samar da ingantattun hanyoyi tare da ruwan sha da ilimi da kiwon lafiya da kuma yakar cututtukan da ke halaka yara.
Alhaji Mamuda Warra, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa a garin Warra a makon jiya.
Ya ce duk da cewa wannan ne karo na farko da ya zama zababben shugaban karamar hukumar, ya yi alwashin samar da isasshen takin zamani da gyara asibitoci da samar musu da magani da gyara makarantu da samar musu da kayan aiki.
Shugaban ya ce zai kara inganta kasuwannin da ke karamar hukumar domin samar mata da karin kudin shiga don gudanar da ayyukan ci gaba ga yankin.
Shi ma sabon Shugaban karamar Hukumar Yawuri, Alhaji Bala Mohmmed Horse, ya ce sun dukufa don kwashe duk wata shara a hedikwatar karamar hukumar da ke garin Yawuri, domin magance yaduwar cututtuka. Shugaban ya bayyana haka ne ga manema labarai a ofishinsa a Yawuri, inda ya ce za su dauki wannan mataki ne ganin yadda magudanun ruwa suka cushe da shara. Sai ya nemi magidanta a yankin su rika tsabtace ciki da wajen gidajensu domin kauce wa bullar cututtukan da ke yaduwa.
Shugaban ya ba da tabbacin cewa samar da kujerun zama ga duk makarantar firamaren yankin da ba ta da kujeru da kuma sauran kayan karatu, domin bunkasa ilimi.