Subscribe
 • facebook
 • twitter
 • whatsapp
 • linkedin
Sunayen Sarakuna 60 da suka mulki Daura

Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Faruq Umar Faruq

Sunayen Sarakuna 60 da suka mulki Daura

Tun farkon kafuwar masarautar Daura zuwa yau, ta yi sarakuna 60, tun daga kan Abduldari, mutumin da ya taso daga Gabas ta Tsakiya ya fara kafa ita masarautar ta Daura a wani dausayi da ake kira ‘Gigiɗo’ kamar yadda ya zo a Littafin Taƙaitaccen Tarihin Daura wanda Fadar Mai martaba Sarkin Daura ta wallafa. Sai dai, akwai wata matsala babba ta rashin samun cikakken jerin sunayen sarakunan na Daura tun daga dauri zuwa yau. Saboda ko shi ma wakilin Tarihi Malam Mamman Siya Abubakar cewa ya yi “…Ba mu da cikakken tarihin Daura daga lokacin kafuwar mulki, sai bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo da ya auku a farkon ƙarni na goma sha tara…” Saboda haka ga ɗan abin da ya samu dangane da jerin sunayen sarakunan Daura.

Rukunin Sarakunan Farko

 1. Abduldari
 2. Kufuru.
 3. Gino
 4. Yakumo
 5. Yakunya
 6. Walzamu
 7. Yanbamu
 8. Gizirgizir
 9. Innagari
 10. Daurama
 11. Gamata
 12. Shata
 13. Batatuma
 14. Sandamata
 15. Jamatu
 16. Hamata
 17. Zama
 18. Shawa
 19. Bawo

Rukunin Sarakuna na Biyu Sarakunan Fulani

 1. Malam Isiyaku
 2. Malam Yusufu
 3. Malam Muhammadu Sani
 4. Malam Zubairu
 5. Malam Muhammadu Bello
 6. Malam Muhammadu Altine
 7. Malam Muhammadu Mai Gardo
 8. Buntarawa Sogiji
 9. Magajiya Murnai

Rukunin Sarakunan Haɓe: Daga masu gudun hijira zuwa yau

 1. Sarkin Gwari Abdu (Abdullahi)
 2. Sarki Lukudi ɗan Tsoho
 3. Sarki Nuhu ɗan Lukudi
 4. Sarki Mamman Sha ɗan Sarkin Gwari Abdu
 5. Sarki Haruna ɗan Sarki Lukudi
 6. Sarki Ɗan’aro ɗan Sarkin Gwari Abdu
 7. Sarki Tafida ɗan Sarki Nuhu
 8. Sarki Sulaiman ɗan Sarkin Gwari Abdu
 9. Sarki Yusufu ɗan Sarki Lukudi
 10. Sarki Tafida ɗan Sarki Nuhu (a Karo na biyu)
 11. Sarki Musa ɗan Sarki Nuhu
 12. Sarki Abdurrahman ɗan Sarki Musa
 13. Sarki Muhammadu Bashar
 14. Sarki Umar Faruk Umar

Mun ciro wannan tarihi ne daga littafin: Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.