✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sunderland ta kori kocinta Di Canio

Jim kadan bayan da kulob din West Brom Albion ya lallasa na Sunderland da ci 3-0 a gasar rukuni-rukuni na Premier na Ingila a karshen…

Jim kadan bayan da kulob din West Brom Albion ya lallasa na Sunderland da ci 3-0 a gasar rukuni-rukuni na Premier na Ingila a karshen makon jiya, kulob din ya bayar da sanarwar yin hannun riga da kocinsa Paolo Di Canio.
Ya zuwa wannan lokaci kulob din ya hada maki daya ne kacal daga wasanni biyar da ya buga a gasar rukunin Premier ta bana, da hakan ta sa kulob din ne yake kasan tebur a jadawalin kungiyoyin da suke fafatawa a gasar.
Ya zuwa yanzu kulob din ya bayar da sanarwar mataimakin Di Canio Kevin Ball ne zia cigaba da horar da ’yan kwallon kafin a nada sabon koci.
Tuni kulob din ya aika da sakon fatan alheri ga Di Canio da hakan ta tabbatar sun yi hannun-riga da shi.