Aminiya

Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Brazil

Ana sa ran a ranar 13 ga watan gobe (Oktoba) ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da kungiyar kwallon kafa ta kasar Brazil.

Rahoton da kafar watsa labarai ta Information Nigeria ta kalato, ya ce tuni Brazil ta amince da wasan kuma zai gudana ne a babban filin wasa na kasar Singapore.

ADVERTISEMENT

An shirya wasan ne a kokarin da Eagles ke yi na tunkarar wasannin share- fagen zuwa gasar cin Kofin Afirka da za a yi a 2021 a Kamaru, yayin da Brazil kuma take shirin tunkarar wasannin share fage na zuwa cin Kofin Duniya da za a yi a 2022.

Wannan ne karo na biyu da kasashen biyu za su hadu a wasan sada zumunta.  Na farko shi ne wanda suka yi a shekarar 2003 kimanin shekara 16 da suka wuce inda Brazil ta lallasa Eagles da ci 3-0.

ADVERTISEMENT

Idan za a tuna kimanin makonni biyu da suka wuce ne Super Eagles ta yi kunnen doki 2-2 da Ukraine a wasan sada zumunta.