✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Ukraine

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa, Super Eagles za ta kece raini da takwararta ta kasar Ukraine a wasan sada zumunta a ranar Talata 10 ga…

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa, Super Eagles za ta kece raini da takwararta ta kasar Ukraine a wasan sada zumunta a ranar Talata 10 ga Satumba mai zuwa. Kafar labaran wasanni ta  Brila.net ta kalato a ranar Litinin da ta wuce cewa tuni kocin Super Eagles, Gernot Rohr dan asalin Faransa da Jamus ya mika sunayen ’yan kwallon da zai yi amfani da su a wasan ga Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) don ta amince. In za a tuna Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta bayyana Najeriya a matsayin ta 33 a iya kwallon kafa a watan jiya, yayin da Ukraine ke matsayi na 25. Sai dai kawo yanzu ba a bayyana fili da lokacin da wasan zai gudana ba. A ranar 11 ga Nuwamban bana ne Super Eagles za ta fara wasan neman gurbi a gasar cin Kofin Afirka na shekarar 2021 da Jamhuriyyar Benin.Sauran kasashen da za su fafata a rukunin sun hada da Lesotho da Sierra Leone.  Kasashe biyu da suka fi nuna kwazo a rukunin ne za su haye gasar Kofin Afirka da za ta gudana a Kamaru a shekarar 2021.