Da Dumi Dumi

Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Ukraine

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa, Super Eagles za ta kece raini da takwararta ta kasar Ukraine a wasan sada zumunta a ranar Talata 10 ga Satumba mai zuwa. Kafar labaran wasanni ta  Brila.net ta kalato a ranar Litinin da ta wuce cewa tuni kocin Super Eagles, Gernot Rohr dan asalin Faransa da Jamus ya mika sunayen ’yan kwallon da zai yi amfani da su a wasan ga Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) don ta amince. In za a tuna Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta bayyana Najeriya a matsayin ta 33 a iya kwallon kafa a watan jiya, yayin da Ukraine ke matsayi na 25. Sai dai kawo yanzu ba a bayyana fili da lokacin da wasan zai gudana ba. A ranar 11 ga Nuwamban bana ne Super Eagles za ta fara wasan neman gurbi a gasar cin Kofin Afirka na shekarar 2021 da Jamhuriyyar Benin.Sauran kasashen da za su fafata a rukunin sun hada da Lesotho da Sierra Leone.  Kasashe biyu da suka fi nuna kwazo a rukunin ne za su haye gasar Kofin Afirka da za ta gudana a Kamaru a shekarar 2021.

 

 

 

ADVERTISEMENT
Share