Da Dumi Dumi

Susan Rice ta zama Mai bayar da shawara kan harkokin tsaron Amurka

Gwamnatin Obama ta nada Susan Rice a matsayin Mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa. Shugaba Obama ya yanke wannan amatsayar saboda yawan hantarar da ya sha daga ’yan jam’iyyar adawa ta Republican, don haka nan da farkon watan Yuli Susan Rice za ta maye gurbin Tom Donilon.
A da an ruwaito cewa, Shugaba Obama ya so a ce Susan Rice ta maye gurbin Misis Hillary Clinton a matsayin Sakatariyar Harkokin Wajen kasarsa. Sai daia matsayinta na jakadar kasar a Majalisar dinkin Duniya, Rice na shan caccaka daga ’yan Jam’iyyar Republican, musamman ganin yadda ta bayyana rikicin Benghazi da ya ci rayuwar Jakadan Amurka, al’amarin da ta bayyana da cewa wani faifan bidiyo ne da aka yi wa lakabi da “The Innocent Muslims,” sabanin danganta al’amarin da ta’addanci. Ita da kanta ta janye daga neman mukamin, ta bar wa John Kerry.
Shi kuwa mukamin Mai bayar da Shawara kan tsaron kasa, ba ya bukatar amincewar majalisar dattijai, don haka ba za su damu da ita ba. Kuma shi kansa Shugaba Obam bai da mu da abin da ’yan majlisar dattijai ke tunani game da Susan Rice ba.
Wannan mukami da aka bai wa Susan Rice daukaka darajarta aka yi, kuma babu abin da ’yan majalisar dattijai za su iya yi. An dai samu dan majalisa daya da ya nuna rashin amincewarsa ta hanyar aikewa da sako ta kafar sadarwar twitter. dan majalisar kuwa shi ne, Jason Chaffetz dan Republic, mai wakiltar Jihar Utah.