Da Dumi Dumi

Suu Kyi ta soki dokar kayyade ’ya’ya biyu ga kabilar Rohingya

Jagorar fafutikar kafuwar dimokuradiyya a kasr Myammar, Aung San Suu Kyi, ta nuna adawarta ga dokar kayyade ’ya’ya biyu ga kabilar Rohingya, don a shawo kan yawan yaduwarsu.
Aung San Suu Kyi ta gabatar da jawabi a gaban babban kwamitin jam’iyyarta ta NLDP, a dakin taro na Royal Rose da ke Yangon.
Dokar kayyade ’ya’ya biyu ta faro ne a shekarar 1994, amma aka hana aiwatar da ita, sai kwatsam a wannan makon aka tursasata akan Musulmi kabilar Rohingya.
Al’ummar Rohingya da ke zaune a Jihar Rakhine, yawansu ya kai dubu 800. Mafi yawan al’ummar kasar mabiya addinin Buddha ne, kuma sun dauki ’yan kabilar Rohingya a matsayin bakin haure da suka yi hijira daga kasar Bangladesh.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya