Da Dumi Dumi

Ta haifi tagwaye a sansanin gudun hijira

Hadiza matar da ta haifi tagwaye a sansanin gudun hijira
Hadiza matar da ta haifi tagwaye a sansanin gudun hijira

Wata mata mai Suna Hadiza Sulaiman wadda daya ce daga cikin mazauna kauyuka 16 da ’yan bindiga suka tarwatsa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna ta haifi tagwaye a sansanin ’yan gudun hijira.

Matar wacce aka fi sani da Dije a kauyansu na Dallatu ta kamu da nakuda ce a kan hanyarsu ta zuwa sansanin da ke Birnin Yero domin guje wa ’yan bindiga.

Mijin matar mai suna Sulaiman Bala ya ce sun kwashe kwana uku suna tafiya a kasa kafin su isa sansanin da ke makarantar firamare ta Birnin Yero a kan titin Kaduna zuwa Zariya.

Ya ce doguwar tafiyar da suka yi daga kauyansu na Dallatu zuwa Birnin Yero ta tayar mata da nakudar inda tilas suka dauke ta zuwa gidan wata ungozoma kasancewar babu asibiti kusa da inda suke.

“Gaskiya mun gode wa Allah tunda ta sauka lafiya, sai dai tana fama da karancin jini kuma ga shi ba mu da kudi saboda mu ba ’yan garin nan ba ne. Saboda haka muke neman tallafin jama’a,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Wakilin Aminiya ya ziyarci gidan ungozomar mai suna Ladi inda mai jegon, Hadiza ta bayyana murnarta na haifuwar tagwayen lafiya.

“Tun lokacin da muka baro kauyenmu na fara jin nakuda kuma ga doguwar tafiyar da muka yi a kasa. Amma dai ina cikin farin ciki tunda na haihu lafiya kuma mace da namiji na haifa,” inji ta.

Wadda ta karbi haihuwar, Ladi Ungozoma ta bayyana halin da aka kawo mai jigon a ranar da cewa: “Gaskiya da suka kawo ta babu yadda zan yi in ce ba zan karbe ta ba, saboda su baki ne ga kuma halin da suke ciki. Kuma saboda a cece rai, mun gode wa Allah da ta haihu lafiya sai dai tana bukatar jini,” inji ta.

Ta ce abin da ya sa ta ci gaba da ajiye su a gidanta shi ne saboda babu inda za su kuma har yanzu jikin mai jigon bai yi karfi ba sosai.

Akwai bayanan da ke nuna cewa wadansu mata ma sun haihu a kan hanyarsu ta zuwa Birnin Yero.

A wani labarin kuma, Hukumar Tallafa wa Wadanda Bala’i ya Shafa ta Kasa ta ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar inda ta rarraba musu tabarmi da kwanukan girki da sauran kayayyaki domin rage musu radadi.

Shugaban Hukumar Sanata Bashir Muhammad ya jajanta wa mutanen kan abin da ya same su inda ya shaida musu cewa Shugaba Buhari na kokari wajen magance matsalar tsaro da ke addabar al’ummar kasar nan.

Ya kara da cewa hukumarsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukanta na taimakom wadanda bala’i ya shafa duk da cewa ba fatarsu ba ce hakan ya rika faruwa a kan mutane.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya