✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta haifi ’yan hudu bayan ta shekara 17 da aure ba haihuwa

Wata mata mai suna Nas Hadiza da ta shafe shekara 17 ba haihuwa ta haifi ’yan hudu, a Asibitin Jumai Babangida Aliyu da ke Minna.…

Wata mata mai suna Nas Hadiza da ta shafe shekara 17 ba haihuwa ta haifi ’yan hudu, a Asibitin Jumai Babangida Aliyu da ke Minna.

An yi wa Hadiza dashen kwayayen haihuwa ne bayan ta shafe shekaru babu haihuwa, lamarin da ya ba ta damar daukar ciki da haihuwa, inda ta haifi maza biyu da mace biyu, sai dai daga bisani daya daga cikin matan da ta haifa ta mutu nan take.

Wakilinmu ya gano cewa Hadiza ta kwanta a asibitin tsawon wata bakwai, inda aka rika kula da lafiyarta. “Kodayake shekara 10 da ta wuce na dauki ciki da kaina, inda na haifi bakwaini bayan makonni 28, sai jaririn ya mutu bayan wasu kwanaki,” kamar yadda ta bayyana wa ’yan jarida a asibitin cikin makon nan.

Hadiza, wadda ta kasance mata ta biyu a wajen mijinta, ta ce: “An yi mani dashen kwayayen haihuwa, saboda na yi fama da rashin haihuwa tsawon shekara 17. Kuma nan da ranar 28 ga Disambar bana na cika shekara 17 da aure.

Ta ce da ta gaya wa ’yan uwanta cewa akwai yiwuwar za ta je asibiti don haihuwar ’yan hudu sai suka dauka wasa take yi.

“Rashin guda da na yi wannan nufi ne na Allah,” kamar yadda ta yi nuni cikin fara’a da ta baibaye fuskarta. “Akwai dimbin kalubale ga ma’auratan da suka shafe shekara 17 ba tare da haihuwa ba, al’amarin tamkar tsiraici ne. Hakuri ba abu ba ne mai sauki, saboda akwai abubuwan da ba za ka iya dauka ba, har ta kai ga ka mayar da martani.”

Maigidanta Alfa Mahmood, wanda ke cike da farin ciki kan haihuwar jariran cewa ya yi, shekaru 17 na juriya da hakuri da addu’a sun biya.

Wata ma’aikaciya a asibitin Jumai Babangida Aliyu na masu juna biyu, Malamar jinya Comfort Tsado cewa ta yi haihuwar ’yan hudu wannan shi ne karo na farko da aka yi a asibitin duk da cewa guda ya mutu.