✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe jikanta saboda kin mahaifinsa

A makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta yi kama wata mata mai shekara 42 mai suna Temitope Akinola da ke zaune a…

A makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta yi kama wata mata mai shekara 42 mai suna Temitope Akinola da ke zaune a garin Shagamu bayan da ta dura wa jikanta mai kwana biyu a duniya gubar kashe kwari da ta yi sanadiyar mutuwarsa.

Kakakin Rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa matar ta tabbatar musu cewa ta kashe jikanta ne saboda kiyayyar da take yi wa ubansa domin ba ta so ya auri ’yarta, kuma ta yi yunkurin zubar da cikin da ’yar ta samu tun daga fari amma limamin cocin da take zuwa ya hana ta tare da nuna mata illar yin haka.

Ya ce hakan ne ya sa ta hakura har ’yar ta haife yaron, sannan ta kashe shi kwana biyu da haihuwarsa  lokacin da mahaifiyarsa ta kwantar da shi domin zuwa wanka. “Yanzu haka tana hannun hukuma an kuma kai gawar jaririn dakin ajjiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Olabisi Onibanjo domin gudanar da bincike,” inji DSP Abimbola Oyeyemi

Abin da aka fi sani ne a al’adar Yarbawa sau tari ma’aurata kan yi aure ne bayan sun samu haihuwar fari wannan ne ya sanya matar da ake zargin ta kashe jikan  don  rusa auren ’yarta da saurayinta.