Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ta kashe kanta a kan mutuwar auren mahaifanta

Marigaya Sadiya Shehu
Marigaya Sadiya Shehu

Wata budurwa  ’yar kimanin shekara 17  mai suna Sadiya Shehu da ke Unguwar Tudun Murtala  a Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano  ta kashe kanta saboda rashin fahimtar da ta shiga tsakanin mahaifiyarta da mahaifinta wanda ya yi sanadiyar rabuwarsu.

Budurwar ta rasu ne bayan da ta kwankwadi madarar fiya-fiya  da aka ajiye a dakin mahaifiyarta don kashe sauro da sauran kwari.

ADVERTISEMENT

A lokacin da Aminiya ta ziyarci gidan su yarinyar a Unguwar Tudun Murtala ta iske mutane suna shiga gidan don jajenta wa iyalan marigayiyar.

Malam Shehu Lawan shi ne mahaifin marigayiya Sadiya ya ce marigayiyar ta kashe kanta ne a kan ‘kankanuwar matsala’ da ta auku tsakaninsa da mahaifiyarta wadda kuma daga baya suka warware matsalar.

ADVERTISEMENT

“Ina da matsala da mahaifiyarta wanda hakan ya jawo ba ta yi farin ciki da lamarin ba, domin ta yi ta kuka a kan hakan daga baya na  gaya mata cewa abin ya wuce. Da sassafe na tashi na fita na bar Sadiya da sauran ’yan uwanta lafiya. Ni dai ina wurin aikina sai aka yi mini waya cewa an  kai ta asibiti. Likitoci sun yi iyakar kokarnsu amma da yake Allah Ya kaddara sai ga shi ta riga mu gidan gaskiya,” inji shi.

Da Aminiya ta tambaye shi ko an yi wa Sadiya miji, mahaiin nata ya bayyana cewa tana da manemi “Domin lokaci na karshe da na yi magana da shi ya yi alkawarin zai turo magabatansa da zarar mahaifinsa ya dawo daga Saudiyya don su zo  a yanke maganar aure. Sai dai da yake kaddara ta riga fata auren ba zai yiwu ba saboda amaryar ta tafi. Ya zama dole in bayyana cewa duk cikin ’ya’yana babu wacce nake kauna kamar Mama (Sadiya). Sai dai a matsyain na Musulmi na dauki wannan lamari a matsyain kaddara. Ina yi mata addu’ar Alah Ya sa Aljanar Firdausi ce makomarta,” inji shi.

Mahaifiyar marigayiyar Malama Amina Shehu ta shaida wa Aminiya cewa  fada ne ya faru tsakanin wata yarinya mai suna Maryam wadda ’yar mijinta ne, sai ya samu kanin marigayiyar ya yi masa dukan tsiya. “Bayan Maryam ta shigo sai ta fara fada da dana Daddy cewa  ya yi mata zagin cin mutunci.Lokacin da babansa ya fito daga ban-daki sai ya fara dukan yaron ba ji-ba-gani. Hakan ya sa na kasa hakuri na nuna wa mijina cewa horon da ya yi wa yaron ya yi yawa koda da gaske ne ya yi laifin da ake zargin ya yi wa yarinyar. Sai mijina ya umarce ni da in yi shiru ni kuma na gaya masa cewa ba zan iya ba. Domin ko zagin da aka ce ya yi  wa yarinyar a wurin ’yan uwansa ya koya,” inji ta

Mahaifiyar ta kara da cewa daga wannan magana sai mijin nata ya yi fushi har ya furta cewa ya sake ta a gaban marigayiyar. “Lokacin da ya gaya mini cewa in tafi ya sake ni sai marigayiyar ta durkusa ta roke shi cewa kada ya kore ni saboda za su shiga wani hali idan na tafi.

Washegari da nake hada kayana na kula marigayiyar tana cikin halin damuwa. A lokacin da nake gaya mata cewa in har don wannan matsala ce kada ta damu kanta domin ni ta bangarena ma magana ta riga ta wuce. Amma abin takaici sai ga shi ta tafi daki ta dauki fiya-fiya ta sha ta mutu,” inji ta.

Tuni dai aka yi jana’izar marigayiya Sadiya kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Yayin da aka tuntubi Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta bakin Kakakinta ASP Abdullahi Haruna ta bayyana cewa har zuwa yanzu ba ta samu wani labari a kan faruwar lamarin ba.