✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe mijinta da ‘ya’ya uku ta kuma kashe kanta

Hukumar ‘Yan Sanda a Jihar Binuwai ta tabbatar da kisan da wata matar aure mai suna Rachael Adetsab ta yi wa mijinta mai suna Nicholas…

Hukumar ‘Yan Sanda a Jihar Binuwai ta tabbatar da kisan da wata matar aure mai suna Rachael Adetsab ta yi wa mijinta mai suna Nicholas Adetsab da ‘ya’yansu uku masu suna Ngwuabese da Seneter da Joshua, sannan daga bisani ta kashe kanta.

Bayan matar ta hallaka zuriyar gidan, sai ta fito a guje zuwa kofar gidan, ta lalata motar mijin nata sannan ta koma ta kulle kanta a cikin gidan a inda ta yanyanka kirjinta da wuka ta mutu.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar, Mista Moses Yamu ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Asabar da ta gabata, cewa a cikin daren ranar Juma’a ne Mista Nicholas Adetsab dake aiki a Karamar Hukmar Makurdi da ‘ya’yan nasa suka gamu da ajalinsu.

“Mun tabbatar cewa matar tasa ita ce da alhakin kisan mutane hudu tare da kashe kanta” inji Kakakin ‘Yan Sandan wanda ya kara da cewa, “tabbatattun labaran da suka iso gare mu sun nuna cewa akwai matsaloli a tsakanin wannan mata da mijinta da ake kyautata zaton hakan ne ya haifar da wannan al’amari marar dadin ji.”

Yamu ya ce kafin mutuwarsu, ma’auratan suna zaune ne a kan Titin Bandeikya dake kallo Cocin NKST. Kuma dukkansu (miji da matar) suna aiki ne a Karamar Hukumar Makurdi.

“An dade ana samun sabani a tsakaninsu har zuwa ranar Juma’ar da lamarin ya faru, inda aka hango matar rike da tabarya tana kokarin lalata motar mijinta. Babu wanda ya san dalilin fadan nasu” inji shi.

Ya ce, a lokacin da ‘yan sanda suka isa cikin gidan sun taras da mutumin kumfa na fitowa daga bakinsa su kuma kananan yaran da wannan mata sun riga sun mutu da wuka a hannunta.

“Al’amarin ya auku ne da misalin karfe 8 da rabi na ranar Juma’ar da ta gabata. Daga bayanan da muka samu an tabbatar da cewa ma’auratan sukan yi fada a tsakaninsu a kollu yaumin” inji shi.

Makwabciyarsu mai suna Sandra Kaso da ta yi magana da wata Jarida ta bayyana cewa, akwai alamar mahaifiyar wadannan yara uku ta fara kwadawa mijin nata tabarya ne a kansa, bayan faduwa a sume ba tare da sanin halin da yake ciki ba ta yanke makogwaronsa, sannan ta yanyanka ‘ya’yan nasu uku.

Makwabciyar ta kara da cewa, “a lokacin da muka ji kururuwa sai muka fito waje da muka ga matar ta fasa gilashin motar ta koma cikin gida ta kulle kofa. Mun yi kokarin ganin ta bude kofar amma ta ki. A wannan lokaci da fadan nasu ya yi tsami ne muka tuntubi mutumin da gidan nasu yake hannunsa, domin ya sanar da ‘yan sanda, amma sai ya gaya mana cewa idan muka kasa sasanta matsalar, to za a dora mana alhakin aukuwar lamarin.”

Sandra ta ce, “amma a lokacin da muka kira ‘yan sanda da karfe 9 na dare, ta riga ta kashe su baki daya. A yayin da ‘Yan Sandan suka balla kofar gidan suka shiga sun taras da dukkansu kwance jinjina.”

Mazauna unguwar da suka fito domin ganewa idanunsu abun da ke faruwa, sun yi wa wannan mata shaidar cewa mafadaciya ce da ta taba dabawa daya daga cikin makwabtan wuka da yanzu haka batun yana gaban kotu.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan ma’aurata ya ganewa idanunsa jini faca-faca a cikin mazaunin ma’auratan. Wata abokiyar aikin Nicholas mai suna Janet Iorpab ta ce “marigayi Nicholas mutum ne mai hakuri. Na san shi tun kafin ya yi aure mutum ne mai haba-haba da jama’a, amma rayuwarsa ta canja a lokacin da ya yi aure.”

Ta kara da cewa, “dukkanmu a cikin ofis mun yi wa wannan mata shaidar fitinanniya ce, dake iya yin amfani da komai a hannunta wajen maka wa duk wanda ya fuskance ta. Babu wanda ya isa ya tunkare ta da fada saboda cewa take yi za ta kashe mutum.”

Kakakin ‘Yan Sanda Yamu ya ce suna ci gaba da bincike domin gano musabbabin wannan kisa na kunar bakin wake. Ya ce, an kwashe gawarwakin zuwa sashen ajiyar gawa na Asibitin Catholic na St. Theresa’s dake Makurdi.

Shugabar Karamar Hukumar Makurdi Uwargida Akange Audu ta tabbatar da cewa mamatan (miji da matar) duk ma’aikata ne dake aiki a karkkashin hukumarta. “Mijin yana aiki ne a sashen kudi na hukumar a yayin da matar ta shi take aiki a sashen gona.”

Ita ma ta tabbatar da cewa ma’auratan sun sha yi fada a tsakaninsu, a inda matar take yi wa makwabtansu gargadin cewa su janye jikinsu daga sabgar tasu, domin babu ruwansu.”

Cincirindon makwabtan mamatan da Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya (NAN) ya zanta da su sun ce a baya an sha samun kaurewar fada a tsakanin ma’auratan. Sun ce sun fara fadan ne da tsakiyar ranar Juma’a amma babu wanda zai iya yin bayanin dalilin fadan. Daya daga cikin makwabtan ta ce ta daina shiga domin sasanta tsakaninsu ne saboda wannan mata ta taba fuskantarta da wuka a hannu a lokacin wani fada da suka taba yi a baya.