Aminiya

Ta kashe saurayinta kan bikin ranar haihuwar ‘yarta

Wata mace da ta hau dokin zuciya ta kashe saurayinta a kan ya ki ba ta kudin bikin cikar ’yarsu shekara daya da haihuwa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar Talatar da ta gaba ce jami’an rundunar suka kama matar mai shekara 23 mai suna Stella Peter da ke zaman daduro da saurayinta mai suna Bala Haruna mai shekara 25 sun kuma kwashe shekara uku suna zaune a haka a Unguwar Tejuosho da ke yankin Surulere inda har ta haifa masa ’ya wacce ta cika shekara da haihuwa.

ADVERTISEMENT

Ya ce, lamarin ya kwabe wa saurayi da budurwar ne lokacin da Stella Peter ta bukaci Bala Haruna, ya ba ta kudin yin bikin cikar ’yarsu  shekara daya da haihuwa shi kuma ya ki, nan musu ya kaure a tsakaninsu, ta dauki wuka ta daba masa a baya wanda hakan ya yi ajalinsa.

DSP Bala Elkana, ya ce ana ci gaba da bincikar matar a sashin binciken miyagun laifuffuka na rundunar kafin a gurfanar da ita a kotu.

ADVERTISEMENT

Haka zalika rundunar ’yan sandan ta Legas ta kama wadansu take zargin ’yan fashi da makami da ake nema ruwa a jallo wadanda suka hallaka wani dan sanda.

Ya ce, wadanda ake zargin sun shiga Unguwar Igando ne cikin dare a kan babura uku da zimmar yin fashi, lamarin da ya sa ’yan sandan yankin suka tasar musu suka kama mutum guda a cikinsu mai suna Usaini Waheed a daren Asabar da ta gabata. Kuma an kama shi da karamar bindiga kira gida, “Waheed mai shekara 32 shi ne ya ba mu bayanan sirrin da muka kai ga kama ragowar ’yan fashin da suka tsere a baya. An kama ragowar ’yan fashin a Unguwar Aribisala da ke yankin Egan a ranar Litinin da ta gabata. ’Yan fashi ne da aka dade ana neman su ruwa ajallo domin su ake zargi da kashe wani dan sanda da ke aiki a Amukoko lokacin da suka je yin fashi a baya. Ana ci gaba da bincike a kansu kafin a gurfanar da su a kotu,” inji DSP Bala Elkana.

Haka zalika rundunar ’yan sandan ta Legas ta kama wadansu da ake zargin barayi ne da suka kware a satar motoci inda aka same su da wata mota kirar Honda da suka sace. Sun bayyana yadda suke sace motar da aka aje da yadda suke kwace mota da karfin tsiya ta hanyar amfani da bindiga. Bugu da kari rundunar ta kama motar bas cike da tabar wiwi a yankin Itafaji a garin Legas ta kuma kama direban motar mai suna Usman Adeyemi mai shekara 27.