✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe saurayinta mai mata biyu kan Naira 3000

Wani magidanci mai suna Usman Ibrahim Magara, ya gamu da ajalinsa a ranar Juma’ar makon jiya bayan da budurwarsa ta daba masa wuka a kirji…

Wani magidanci mai suna Usman Ibrahim Magara, ya gamu da ajalinsa a ranar Juma’ar makon jiya bayan da budurwarsa ta daba masa wuka a kirji sannan ta daba masa a gefen hannunsa bayan takaddamar da suka yi da ita a kan Naira dubu uku a dakinsa da ke garin Shagamu a Jihar Ogun.

Malam Abdullahi Alkwatanawi, mazaunin garin Shagamu ne ya shaida wa Aminiya faruwar lamarin inda ya ce, marigayin Usman Magara dan asalin garin Boko a Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara ce,  yana kuma  sana’ar acaba ne a garin Shagamu, sannan ya dade yana tare da yarinyar mai suna Idowu Abosede  da ake kira Olosho, wadda take zuwa dakinsa wani lokacin har da kanwarta. Ya ce suna zuwa wajen marigayin ne daga wasu ƙauyukan da ke gefen garin Shagamu. “A ranar da lamarin ya faru an ce cikin dare gardama ta kaure a tsakanin marigayin da yarinyar, inda ta bukaci ya ba ta Naira dubu hudu, shi kuma ya ce dubu daya zai ba ta, to wadansu na cewa, ta ga ya yi wata harka yana da Naira dubu 70 sai ta bari bayan ya yi barci cikin dare ta daba masa wuka a kirji da hannunsa, inda ya fito daga gidan yana ihu yana kururuwar a kai masa dauki, a jikin benen gidan ne jini ya kwashe shi ya fadi ya mutu,” inji shi.

Sarkin Hausawan Shagamu Alhaji Inuwa Sarki, ya shaida wa Aminiya cewa sun yi wa matashin sutura sun kuma binne gawarsa a garin Shagamu, ya ce lamarin abin takaici ne. “Bayan da yarinyar ta kashe shi sai ta tsallake ta shiga dakin wani abokin aikinsa wanda shi ma acaba yake, can ta kwanta abinta a cikin gidan, ka duba irin wannan abu, don haka a kowane lokaci muke jan kunnen matasanmu da ke zuwa daga Arewa cewa su rika kare mutuncinsu su guji shiga sabgogin banza,” inji shi.

Sarkin Hausawan, ya ce idan ka kula za ka ga yarinyar da ake zargi da hallaka magidancin yarinya ce karama da ba ta wuce shekara 14 ba, haka suke kwaso yaran Yarbawa suna kwana da su a dakinsu. Akwai lokacin da mai gidan da yake haya ya kira shi ya fada masa, yake nuna masa illar aje kananan yara mata a dakinsa.

Ya ce, masa idan iyayensu suka kama shi ba zai ji da dadi ba, mai gidan ya shaida min a wannan lokacin in ya ga yaran yakan kore su daga gidan, bai san yadda aka yi suka dawo ba har wannan abu ya faru. “Ka ga mutum da matansa biyu da ’ya’ya shida a kauyensu ya zo neman na abinci ya buge da shiririta har karamar yarinya ta hallaka shi a kan Naira dubu uku wannan abin takaici ne,” inji shi.

Ya ce,  “A lokacin da aka kamo yarinyar a dakin abokin sana’ar wanda ta kashe mutanen sun fara dukanta, nan aka ji tsoron kada ita ma a kashe ta aka kawo ta fadata, nan na sa aka tsare ta a wani waje aka kulle ta, saboda kada mutane su yi mata lahani. Daga nan na kira ’yan sanda na mika musu ita, daga bisani suka je suka dauko gawarsa, an kuma bai wa ’yan uwansa gawar mun yi masa sutura, kuma ’yan uwan nasa sun ce sun bar wa Allah su ba za su yi shari’a da kowa ba.”

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yarinyar da ake zargi da kashe saurayinta kan Naira dubu uku na hannun jami’ansu kuma suna gudanar da bincike. Ya ce, matakin da dangin marigayin suka dauka ba zai hana su gurfanar da wacce ake zargi a gaban kotu ba, domin ta fuskanci hukunci.

Ko a kwanakin baya ma, wata mace ’yar asalin Jihar Benuwai ta kashe saurayinta da wuka a Unguwar Yaba kuma shi ma dan Arewa ne da ke sana’ar cajin waya a Legas.