✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kona hannun dan kishiyarta saboda ruwan wanka

Wata mata mai suna Misis Aminot Otun da ke zaune a unguwar Surulere da ke jihar Legas ta kona hannun dan kishiyartsa mai suna Awwal…

Awwal yana nuna hannunsa da kishiyar mahaifiyarsa ta konaWata mata mai suna Misis Aminot Otun da ke zaune a unguwar Surulere da ke jihar Legas ta kona hannun dan kishiyartsa mai suna Awwal da wutar risho don ya kara maganin Dettol a ruwan wankansa.
Lamarin ya tayar da hankalin makwabtansu inda suka sanar da shugabar kungiyar kare ’yancin yara mai zaman kanta don kai wa yaron dauki.
Shugabar kungiyar ta ‘Child to Child Network’, Ngozi Ekwerike Okoro da ke makwabtaka da su a gida mai lamba 59, Titin Suenu a Surulere, Legas ta kai yaron, dan kimanin shekara bakwai, wani asibiti mai suna ‘Randel Genaral Hospital Mother and Child’ a Unguwar Gbaja, daga bisani ta sanar da ’yan sanda.
Ngozi ta ce, “Awwal ya samu mummunan rauni daga kunar da kishiyar mahaifiyarsa ta yi masa. Da muka kai shi asibitin muka yi musu bayani, sai likitan ta ce sai dai mu tafi babban asibitin gwamnati na Ikeja, saboda nasu asibitin ba shi da isassun kayan aikin da zai yi wa yaron magani. Daga bisani sai muka kai shi wani asibiti mai zaman kansa a unguwar Mushin inda aka duba shi aka yi masa magani. A yanzu yana sashin lura da kananan yara na ’yan sanda da ke yankin Alakara ana ci gaba da kula da shi.”
Awwal ya shaida wa Aminiya cewa ya kara ruwan maganin Izal a ruwan wankansa ne sai kawai kishiyar ta rufe shi da duka, har ta kone hannunsa a risho, inda sai bayan yini hudu ne da faruwar lamarin makwabatansu suka kai shi asibiti.
Daga bisani ’yan sanda sun yi awon gaba da Aminot suka mika ta sashin binciken manyan laifuffuka.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Ngozi Braide ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana cewa za su gurfanar da matar a kotu bayan sun kammala bincike.