✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta nemi mijinta ya sake ta saboda yadda yake nuna mata ‘tsananin kauna’

Allah daya gari bamban! A yayin da a wasu wuraren mata ke korafin tursasawa da duka da zagi da rashin kyautatawa da rashin nuna kauna…

Allah daya gari bamban! A yayin da a wasu wuraren mata ke korafin tursasawa da duka da zagi da rashin kyautatawa da rashin nuna kauna daga mazansu, a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, wata mata (an sakaya sunanta) ta kai mijinta kotu tana neman ya sake ta, saboda ba ta jin dadin yadda yake nuna mata tsananin kauna, musamman yadda yake ba ta kyaututtuka da suka wuce hankali da kuma yadda a kullum yake share gidansu kal-kal ba tare da gajiyawa ba.

Matar ta shaida wa Kotun Shari’a a Hadaddiyar Daular Larabawa cewa mijinta yana nuna mata matsananciyar kauna, ba ya yin musu ko gardama da ita, ba ya yi mata tsawa ko kadan, maimakon haka sai dai ya yi ta nuna mata kauna da tausayi, ga shi kuma kirkinsa ya wuce misali gare ta. Ta ce wadannan halaye da mijinta yake nuna mata, su suka sanya a kullum take jin bakin ciki da damuwa, don haka tana son kotu ta raba auren su, domin ba za ta iya jure zama da mijin ba.

Matar ta shaida wa jaridar Khaleej Times cewa, “Kaunar da yake nuna mini da irin tsananin jinkansa da kirkinsa gare ni sun wuce iyaka, don haka ina son kotu ta raba aurenmu.”

Ta kara da cewa “Nakan ji bakin ciki iya wuya dangane da irin kaunar da yake nuna mini. Yakan taimaka mini da share-share a gida koda ban nemi ya taimaka ba.” Ta ce ko sau daya bai taba kyararta ko ya yi mata musun wata magana ba, ga shi bai taba daga mata murya ba da sunan fada a tsawon aurensu na shekara daya.

Ta ce akwai lokacin da ta lura cewa kibarsa ta fara yawa, sai ta yi masa korafi, inda nan da nan ya fara daukar matakan rage kibar, ya rika cin abinci da magunguna na musamman na rage kiba, sannan ya rika yin atisaye, kuma wurin yin hakan har ya karye a kafa.

Matar ta ce, duk da cewa ya karye a kafa ya ci gaba da kyautata mata, abin bai yi mata dadi ba, domin ta yi ta kokarin ganin koda sau daya ne sun yi sabani ko cacar baki, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba. A cewarta, a duk lokacin da ta saba masa, shi ne zai yi ta lallashinta, yana ba ta hakuri, yana cewa ya yafe mata, sannnan ya biyo bayan haka da wata kyauta ta mamaki gare ta.

“Ni ina matukar bukatar cacar baki da sabanin ra’ayi, amma ba rayuwar salin-alin ba,” inji matar, kamar yadda ta shaida wa ’yan jarida.

Da kotun ta tuntubi mijin dangane da bukatar matarsa ta raba aure, sai ya ce shi dai yana kaunar matarsa. Ya roki kotun da kata ta raba auren. Ya ce, “Ba daidai ba ne a ce za a raba auren da aka daura tsawon shekara daya kawai. Akwai sauran lokaci da ma’aurata za su ci gaba da zama, suna gyaran zama daga kura-kuransu. Ni dai a kullum kokarina shi ne in ga na kyautata wa matata, in ga na zama mai kirki da tausayi da kauna a gare ta.”

Alkalin kotun ya dage shari’ar, sannan ya umarci ma’auratan su koma gida su sasanta da juna.