✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta nemi saki saboda mijinta ya auro tsohuwa

Shugaban Kotun Gargajiya ta Oja Oba/Mapo da ke Ibadan, Cif Ademola Odunade ya raba auren Fausat Inaolaja da mijinta Ahmed Inaolaja saboda auro  amarya mai…

Shugaban Kotun Gargajiya ta Oja Oba/Mapo da ke Ibadan, Cif Ademola Odunade ya raba auren Fausat Inaolaja da mijinta Ahmed Inaolaja saboda auro  amarya mai yawan shekaru fiye da uwargida da mijin ya yi.

Uwargida Fausat ce ta shigar da kara a kotun inda ta roki kotun ta raba auren nasu saboda mijinta Ahmed ya auro amaryar da ta girme ta. Cikin bayanin da ta yi wa kotun, Fausat ta ce, “Yau shekara 9 ke nan da muke zaune tare da Ahmed a matsayin miji da mata kuma Allah Ya wadata mu da haihuwar ’ya’ya 2. Ni ce nake zuwa wajen mahaifiyata ina karbo kudi da kayan abinci da nake ciyar da mijin nawa da ’ya’yanmu da ni kaina da sauran dawainiyar yau da gobe. Amma maimakon ya saka mini da abin farin ciki sai kawai ya saka mini da auren wata mata da ta girme ni.”

Matar ta ci gaba da cewa, “Na gwammace in ci gaba da zama ba  miji, maimakon zuwa wurin mahaifiyata a kullum domin karbar abubuwan cefanen gida da bukatun karatun ’ya’yanmu da lura da lafiyarmu.

Na shigar da wannan kara ce domin rokon kotu ta raba auren namu saboda mijin nawa ya kasa sauke hakkin aure. Shi ne ya yi sanadin ficewar da na yi da ’ya’yana daga cikin kangon gidan da muke zaune muka koma wurin mahaifiyata da take daukar dawainiyarmu.”

Matar, wacce ta rika kuka da hawaye ta yi wa kotun dogon bayanin da ya danganci gazawar mijinta a kan matsalolin da take ciki. Ta ce, “Na gaji da zama tare da wannan mutum, shi ne ya sa nake rokon kotu ta raba auren kuma a kyale ni in ci gaba da rikon wadannan yara.”

Da yake kare kansa, Ahmed Inaolaja ya shaida wa kotun cewa “Surukata, wato mahaifiyar matata ita ce ummul-haba’isin rashin jituwar da ke tsakanina da Fausat, domin komai kyawon abin da na yi wa matar tawa ba ya fitowa a fuskar surukar tawa.  Fausat ta fadi iyakar abin da take so, amma ta manta ba ta ambaci batun jarin da na mika mata domin hada-hadar kasuwanci ba.”

“A kan batun amarya da na aura, gaskiya ne sai dai amaryar tana zaune ne a wani gida daban kuma karya take yi cewa amarya ta girme ta a yawan shekaru. Na aure ta ce saboda tana da kiba kuma irin matan da nake so ke nan. Amma tunda ta nemi kotu ta raba auren namu, to ni ma na amince,” inji Ahmed Inaolaja.

Shugaban kotun ya raba auren tare da umartar Ahmed ya rika kawo Naira dubu 10 a kowane wata ta hannun kotu wanda Fausat za ta rika amfani da su wajen daukar nauyin makarantar ’ya’yansu biyu da abincinsu.