✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta rasa ido bayan yi mata zanen tattoo

Wata ’yar kasar Poland mai shekara 25, ta  rasa idonta garin gyarar gira inda ta makance a idonta na dama ta kuma samu matsalar gani…

Wata ’yar kasar Poland mai shekara 25, ta  rasa idonta garin gyarar gira inda ta makance a idonta na dama ta kuma samu matsalar gani a idonta na hagu bayan ta kai kanta, a yi mata zanen tattoo a gefen girarta da nufin neman suna.

Matar mai suna Aleksandra Sadowska, ’yar asalin garin Wroclaw a yammacin kasar Poland ta fara fuskantar matsala ce shekara hudu da suka gabata lokacin da aka yi mata zanen a karon farko.

An ruwaito cewa, ta bincika shafukan sadarwar Intanet domin samun wanda zai yi mata zanen, inda ta ci karo da wani mai zanen tattoo dan asalin garin Warsaw babban birnin kasar.

Kafafen yada labarai na Poland, sun ruwaito mai zanen, mai suna Piotr A. ana zargin bai san tsarin gudanar da zanen ba dalilin hakan ne ya sa aikin ya cabe. Matar ta koka kan tsananin radadin da ta ji, bayan kammala aikin amma mai zanen ya fada mata cewa, ciwon na dan lokaci ne inda ya ba ta magungunan rage radadin ciwo.

A wata mukala da jaridar Fakt ta Poland ta wallafa a shekarar 2015, ta ce, mai zanen ya danna allurar zanen har cikin kwayar idon matar kuma abin da ya jawo makancewarta ke nan.

Kwanakin  baya jaridar Daily Mail ta Ingila ta wallafa bayanan likitoci cewa, ba a san me zai iya faruwa da idonta ba nan gaba.

Matar ta ce, “Abin takaicin shi ne, likitoci ba su bayyana fata mai kyau game da abin da ka iya faruwa da ni ba. Matsalar da ta same ni ta kai matuka. Ina tsoron zan iya makancewa baki daya.”

A shekarar 2015 kawai, an yi wa Aleksandra tiyata da yawa a kokarin gyaran idonta na bangaren dama. Duk da kokarin da suka yi, likitocin ba su tabbatar da za ta iya warkewa gaba daya ba.

Jaridar ta Daily Mail, ta ruwaito cewa mai zanen ya yi amfani da tawadar zane na fatar jiki wajen zane a idon matar inda jaridar ta ce, matar ta yi kokarin kwaikwayon wani mawaki ne dan kasar Poland mai suna Popek.

Aleksandra dai tuni ta kai wanda ya yi zanen kotu, inda yanzu yake zaman kaso na shekara uku a kan laifin kassara matar kamar yadda kotun ta yanke masa hukunci. Duk da cewa ta samu matsala a idonta, Aleksandra Sadowska ta bayyana cewa ba ta yi nadamar abin da ta yi ba. Ta ce, ta dai yi da-na-sanin zaben mutumin da bai iya aikinsa ba, wajen yi mata adon.

 

Daga www.odditycentral.com