✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta rataye kanta saboda gaza biyan bashin banki da ta tsaya  wa kawarta

Wata matar aure mai suna Shakirat Rasheed mai shekara 41 ta rataye kanta a dalilin kasa biyan bashin banki da ta tsaya wa kararta wadda…

Wata matar aure mai suna Shakirat Rasheed mai shekara 41 ta rataye kanta a dalilin kasa biyan bashin banki da ta tsaya wa kararta wadda ta yi layar zana.  Al’amarin ya auku ne da misalin karfe 1 na ranar Juma’a da ta gabata a Unguwar Apete da ke birnin Ibadan.

Wata majiya ta kusa da  marigayiya Shakirat ta shaida wa Aminiya cewa, ana zargin ta kashe kanta ne saboda matsawar da jami’an wani bankin ba da rance ga kananan ’yan kasuwa da aka fi sani da LAPO suka yi mata a kan ta biya bashin da ta tsaya wa wata kawarta ta karba daga bankin.

Majiyar ba ta bayyana yawan kudin da kawar marigayiyar ta karba ba, sai dai ta tabbatar da cewa marigayiya Shakirat ta tsaya wa kawarta aka ba ta bashin kudin da ake tsawala ruwa, inda matar da ta karbi bashin ta yi layar zana kuma jami’an bankin suka rika neman marigayiya Shakirat ta biya su kudin kamar yadda doka ta tanada.

Majiyar ta ce ganin ta kasa gano inda kawarta ta shiga ita kuma ba za ta iya biyan kudin ba ne, sai ta yanke shawarar kashe kanta ta hanyar rataye kanta da igiya a cikin dakin da suke zaune da mijinta Rasheed wanda shi ne ya fara gano gawarta a rataye.

A daidai wannan lokaci ne mijin nata ya garzaya zuwa ofishin ’yan sanda na Apete ya yi musu bayanin halin da ake ciki.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Oyo Mista Shina Olukolu

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce tun daga ranar da al’amarin ya auku suka fara bincike domin gano dalilin mutuwar matar.

A wani bincike da Aminiya ta gudanar ta gano cewa, wata mata da aka sakaya sunanta da suka rabu da mijinta ta yi yunkurin rataye kanta bayan ta kasa biyan irin wannan bashi da ta karba daga irin wannan banki da ke Ibadan. Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa, matar da ke zaune da ’ya’yanta 5 a cikin gidan iyayenta a Ibadan ta karbi bashin Naira dubu 700 ne daga bankin Micro Finance ta fara hada-hadar dafa abinci amma sai al’amarin ya gurgunce ta kasa ci gaba da kasuwancin saboda yawan hasarar da ta rika samu.

Da farko ta fara biyan bashin Naira dubu 5,500 a kowane mako amma bayan gurguncewar kasuwancin tare da sayar da kadarorin da ta mallaka, sai ta fara boyewa a dalilin yawan tuntubarta da jami’an bankin suke yi, inda a karshe ta yi yunkurin kashe kanta ta hanyar rataye kanta a cikin dakinta. Wata yayarta ce ta ceto ta lokacin da ta leka cikin dakin ta hango abin da ke faruwa inda ta kubutar da ita. Bayanai sun ce yanzu haka wadansu ’yan uwan matar sun kulla yarjejeniya da jami’an bankin inda suka yi alkawarin biyan sauran kudin da ke kanta.