Search
Subscribe
Ta roki kotu ta raba aurensu saboda mijinta na shan giya

Ta roki kotu ta raba aurensu saboda mijinta na shan giya

Wata matar aure mai suna Olaitan Abass ta roki Kotun Ile Tuntun da ke Mapo a Ibadan ta raba aurensu na shekara 4 da mijinta Ibrahim Abass saboda mijinta da mahaifiyarsa suna kwankwadar giya ba kakkautawa.

Olaitan ta ce, bayan sun mayar da giya kamar ruwan sha, dan da suka haifa da mijinta ma sun koya masa kwankwadar giyar inda suke zuba masa kofi yana sha duk lokacin da ya ci abincin safe da na rana da na dare.

Matar ta ce yanzu ta gane kuskurenta, inda  take takaicin auren mijin nata wanda ta shaida wa kotun cewa “Sai ya bugu da giya yake iya kwanciya. Hakan ya sa yana damuna da warin giya da kuma yawan amai a kan gado,” inji ta.

Olaitan ta shaida wa kotun  cewa abu na biyu shi ne, yadda mijinta da mahaifiyarsa suka hada mata maganin zubar da ciki cikin lemon kwalba har sau biyu tana sha ciki yana zubewa ba tare da ta sani ba. Haka kuma “Mahaifiyata ce, take daukar dawainiyar abincina da wannan yaro a kowane wata saboda halin ko in kula na mijina. Babu wata hanyar da zan iya kula da tarbiyyar wannan yaro a cikin irin wannan mummunan hali da na samu kaina. Saboda haka nake rokon wannan kotu ta raba aurenmu kuma a kyale min wannan yaro ya ci gaba da zama tare da ni domin ya samu kyakkyawar tarbiyya,” inji ta.

Da yake kare kansa Ibrahim Abass bai musanta batun shan giya ba, sai dai ya ce, karya matarsa ta yi da ta ce shi da mahaifiyarsa suna koya wa dansu wanda bai wuce shekara hudu ba shan giya. “Kuma karya ta fadi cewa ni da mahaifiya ta mun zubar mata da ciki sau biyu,” inji shi.

Ya kara shaida wa kotun cewa tun shekara biyu da suka wuce ya yi kokarin rabuwa da matar tasa a dalilin wasu muhimman abubuwa biyu. “Na farko fitinanniyar mace ce mara hakuri da ta saba yin fada da makwabta kuma tana fita daga cikin gidan da muke zaune da sassafe zuwa shagon da take sayar da kaya tare da dawowa gida cikin dare. Abu na biyu shi ne, na sha ziyartar shagon da take kasuwanci a nan Ibadan, inda nake samunta da maza suna tadin soyayya. Sau da yawa na sha jan kunnenta amma ta ki dainawa. Saboda haka ni ma ina rokon kotu ta raba auren namu,” inji shi.

Bayan sauraron bangarori biyu, Shugaban Kotun Cif Olasunkanmi Agbaje ya ce, akwai bukatar karin shaidu da kotun take so a gabatar mata daga kowane bangare kafin a yanke hukunci.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin