Ta sayar da mijinta Naira dubu 6 ta sayi sutura

Wata matar aure ’yar kasar Kenya mai suna Edna Mukwana a karshen bara, ta yanke shawarar sayar da mijinta kan kudin kasar Kenya Shilling (Ksh) 1,700 (daidai da Naira dubu 6), don saya wa ’ya’yansu sutura.

Wani mutumin Zambiya ya ce, Edna ta yanke shawarar sayar da mijinta ne don saya wa ’ya’yansu kayan bikin sabuwar shekarar da muka shiga

Edna Mukwana, ta yanke wannan hukuncin ne, bayan ta kama mijin nata da wata mata daban, yayin da ya yi kwana bakwai  bai dawo gidansu ba.

Edna ta ce, “Mijina ya kasance a koyaushe yana kwankwadar giya da bin karuwai. Don haka na umarci karuwar da yake bi da ta turo min kudin kasar Kenya Shilling 2000 (daidai da Naira dubu 7 da 145), amma sai ta turo min Shilling 1,700 (daidai da Naira dubu 6). Ni kuma na yi amfani da duk kudaden wajen saya wa ’ya’yanmu kayan sabuwar shekara.

Idan har wanda yake bi tana bukatar zamansu tare da mijina, shi ke nan,” inji Edna Mukwana.

ADVERTISEMENT

Da aka tambayi Edna, ko nan gaba za ta iya sauya ra’ayinta ta koma wajen mijinta bayan ta sayar wa wata? Sai ta ce sam ba zai yiwu ta sake karbarsa a matsayin mijin aure ba, saboda ba ta son ta ci gaba da shiga cikin kuncin rayuwa a bana, kamar yadda ta samu kanta a bara.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya