✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta tunkudo mijinta daga saman bene

Wata kotu a Ibadan ta raba auren wani magidanci mai suna Nurudeen Ayodeji da matarsa Adijar Ayodeji da suka shafe shekara 32 suna aure, kafin…

Wata kotu a Ibadan ta raba auren wani magidanci mai suna Nurudeen Ayodeji da matarsa Adijar Ayodeji da suka shafe shekara 32 suna aure, kafin kotu ta raba su.

Nurudeen shi ne ya shigar da kara gaban kotun Oja Oba/Mapo a inda ya nemi a raba auren su saboda ya gaji da fitinar matar tasa wacce ta taba tunkudo shi daga saman bene hawa daya ya fado kasa da karayar hannu da wasu raunuka a jikinsa.

Da yake gabatar da shaida a gaban kotun a kan dalilin da yasa yake so a raba auren nasu da Adijat, Nurudeen ya ce, “wannan mata fitinanniya ce wacce a kowane lokaci aka samu rashin jituwa tsakaninta da ni kaina da makwabtana sai ta tube suturun jikinta ta yi tsirara tana ihu kamar mahaukaciya.

Iyayenmu sun sasanta tsakaninmu bayan ta tunkudo ni daga saman bene da aka garzaya dani zuwa Asibiti da na yi jinyar karayar hannu amma bayan sasantawar, wannan mata ta ci gaba da aikata miyagun halayenta. Hakan ne yasa dukkan makwabtanmu suka fice daga cikin wannan gidan haya.”

“Ganin haka ne yasa na yanke shawarar auro mata amarya amma a maimakon samun saukin fitinarta sai karuwar kishi ta ruruta wutar fitina. Idan wani abu ya shiga tsakaninta da amarya ko tsakaninta da makwabta sai ta fito kofar gida tsirara tana jifarsu da duwatsu. Wannan abun kunya ne gare ni, shi ne yasa nake so kotu ta raba auren kwata-kwata kowa ya huta,” inji shi.

Da take kare kanta, Adijat ta musanta dukkan bayanan da mijin nata ya yi a gaban kotu. Ta ce “karya ya fadi cewa na tunkudo shi daga saman bene. Abun da ya auku a wannan rana an samu rashin jituwa ne tsakani na da shi, a inda ya hau bene yana kwasar kaya na yana watso su kasa sai yayi tuntube ya fado kasa ya karya hannu. Amaryar da ya auro ita ce fitinanniya domin ta sha shiga cikin dakina tana yaga min sutura da lalata min kaya amma mijin namu ya ki hukumta ta,” inji matar.

Bayan sauraron bangarorin biyu ne Alkalin Kotun, Cif Ademola Odunade ya ce ya lura babu sauran soyayyar juna a tsakaninsu, saboda haka ya raba auren tare da bayar da umarnin Nurudeen ya rike ‘ya’ya 4 da suka haifa a tare da shi, kuma ya biya tsohuwar matar ta shi Naira dubu 3 na kwasar kayanta daga cikin gidansa.