✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta Yi Auren Mut’a

Sunan Littafi: Ta Yi Auren Mut’aSunan Marubuci: Madu IroKamfanin Wallafa: Policy Communications LimitedShekarar Wallafa: 2013Yawan Shafuka: 97Farashi: N500 Littafin Ta Yi Auren Mut’a – Sabon…

Sunan Littafi: Ta Yi Auren Mut’a
Sunan Marubuci: Madu Iro
Kamfanin Wallafa: Policy Communications Limited
Shekarar Wallafa: 2013
Yawan Shafuka: 97
Farashi: N500

Littafin Ta Yi Auren Mut’a – Sabon labari, sabon salo, sabon al’amari, musamman a Adabin Hausa da al’ummar Hausawa.
Kamar yadda aka tsakuro makunshiyar labarin a bangon littafin: “Ta Yi Auren Mutu’a, littafi ne da ke ba da labarin wata yarinya ma’abuciyar karance-karancen littafin labaran sha’awa. Tana da digiri na biyu a fannin Turanci. Tana aiki a kamfanin sadarwa na TNM. Ta kai shekaru 30 a duniya ba ta samu miji ba. Sai a cikon na 30 din ne ta samu mijin, amma auren ya ki dadi. Wata takwas bayan auren ta rabu da mijin. Ta dawo ga rayuwarta ta kadaici da sha’awa.
“Saurayin farko da ya bayyana gare ta shi ne wanda ya neme ta da auren mut’a. Ba ta san me ake nufi da auren ba, amma tana son saurayin saboda hankalinsa da iya maganarsa.
“Shin za ta amince wa wannan saurayi ne da bukatarsa ta mut’a ko kuwa za ta hakura ne ta ci gaba da rayuwarta ta kadaici?”
Bisa doron wannan labari na Raliya ne aka warware jigo da kunshiyar littafin. Tashi guda za a iya cewa jigon littafin nan soyayya ne, musamman wacce aka dora bisa maudu’in nan mai wuyar sha’ani, wanda kuma ya dade yana haifar da cece-kuce tsakanin mabiya akidun Shi’a da Ahlussunnah – auren mutu’a.
A kokarinsa na kare salon auren na mut’a, marubucin ya bijiro da tarin matsalolin da ke cunkushe cikin al’ummarmu, musamman ma Musulmi. Wadannan matsaloli kuwa sun hada da jahiltar addinin shi kansa da rashin hakuri da juna. Haka kuma, ya bijiro da yadda al’umma, musamman matasa suka jahilci shi kansa addinin na Musulunci da yadda suka takarkare suna kwaikwayon rayuwar Yahudu da Nasara.
A misali, takin sakar soyayya da ke faruwa tsakanin Raliya da Isa, ita ta nuna yadda ake samun sabanin fahimta tsakanin matasa. A yayin da ita ta kasance mai sha’awar rayuwar Turawa, shi Isa ya kasance mai tsananin riko da addini – babban bambancin da ya haifar da matsala a tsakaninsu duk kuwa da cewa ’yan uwan juna ne. Wannan bambanci da sabanin halaye ne suka haddasa aurensu ya rabu tun ba a je ko’ina ba.
Yaya ake auren mut’a, me ke dadinsa da fa’idarsa kuma me ke matsalolinsa? Marubucin nan ya warware wadannan mas’aloli a littafin, duk kuwa da cewa labarin kirkirarre ne. Mun ga amsoshin wadannan tambayoyi a yanayin rayuwar soyayyar Kafayat da Mukhtar, wadda ta kai su ga auren mut’a; auren da ya kare cikin takaitaccen lokaci bayan da aka yi masa canjin wurin aiki daga Ikko zuwa Abuja.
Wani maudu’i da marubucin ya bijiro da shi a littafin, shi ne yadda wasu matasanmu suka kasance masu kishin addini amma tare da jahilci. Dubi dai yadda Mahmud Isyaku ya kasance mai kishin addini amma kuma bai tanadi ilimin da zai taimaka masa wajen bauta ba kamar yadda ka’idar addinin ta bukata. Sai dai an sassaita tunanin matasa, aka ja hankalinsu da su tashi tsaye su nemi ilimi, kuma duk abin da za su yi, su kasance suna da gamsassar hujja. Wannan darasi ya fito ne a sakamakon munazarar da aka tafka tsakanin Malam Yahuza da kuma limamin babban masallacin jami’ar da Mahmud ke karatu.
Haka kuma, wani darasi da littafin nan ya sake ankarar da mutane game da shi, shi ne cewa lallai ga duk mai son yin wa’azi ko tunatarwa ko gyara ga dan uwansa, to ya bi al’amarin da hikima da hakuri da kuma tausasawa. Kada mutum ya kasance mai zafafawa ko yin karfa-karfa, sai dai ya kasance mai taushi-taushi kuma mai kakkarfar niyya da iya jan hankali. Misalin haka ya fito a dangantakar da ta kullu tsakanin Mukhtar da Raliya. A sakamakon yadda ya rika kokarin gyara mata dabi’a cikin hikima, shi ya sa soyayyarsu ta ginu kuma ta yi karko.
“Tana jin dadin salon Mukhtar na cusa mata ra’ayi, saboda yana yi ne ta hanyar nuna mata hikima ko illar abu, daga nan kuma in ya ga da halin haka sai ya janyo mata aya ko hadisi ba masu yawa ba. Kazalika, bai da irin fariyar nan ta nuna shi tsarkakakke ne. Yakan bi ta ne a hankali har ta fahimci abin da yake so ta fahimta, ba kamar Isa tsohon mijinta ba da zai dirar mata da janyo ayoyi da hadisai. Ko shakka ba ta yi, wadannan halayen ne suka tunzurar da zuciyarta ga son Mukhtar matuka.” – Shafi na 90 zuwa 91.
Madu Iro (Muhammad Ibrahim), ya rubuta littafin nan cikin ingantattar Hausa, sannan ya kasance mai zaben kalmomin da suka dace da shedarorin da ya gina zubin labarin. Ya bijiro da hikima wajen warware rikitaccen maudu’i cikin salon da zai kama zuciyar mai karatu. Wannan ya nuna irin yadda ya sako sabon salon aika sako mai tsauri ta hanyar kirkirarren labari.
Duk da cewa an yi kokari sosai wajen kauce wa kura-kurai wajen rubuta littafin nan, amma kasancewar hannun marubuci makaho ne, makarancin kwakwaf ba zai rasa gano wasu daga cikin kura-kurai ba a littafin. Misali, tun daga farkon littafin har zuwa karshensa, marubucin ya rika raba wasu bakake cikin kalmomi, alhali hada su ya kamata ya yi. Misali, kalmar ‘musu’ sai ya rika rubuta ta a rabe: ‘mu su.’ Sauran kalmomin da suka fito a haka sun hada da ‘mu ku’ maimakon ‘muku’ da ‘ya kan’ maimakon ‘yakan’ da ‘ya yin da’ maimakon ‘yayin da’ da sauransu.
Haka kuma, wasu wurare yakan yi amfani da lamirin namiji a macen kalma. Misali a shafi na 91 ya rubuta: ‘wancan magana’ maimakon ‘waccan magana.’ Wasu kalmomin kuma, yakan rubuta su ba daidai yadda ake ambata su ba. Misali, yakan rubuta kalmar ‘kariso’ maimakon ‘karaso.’
Idan ka debe wadannan ’yan kananan matsaloli, zubi da tsarin littafin nan babu makusa sai dai yabo. Haka kuma a ganina, farashin littafin ya yi yawa, musamman idan muka yi la’akari da yawan shafukansa (97), duk kuwa da cewa an yi masa wallafa mai inganci. Ina shawartar marubucin, ko kuma kamfanin wallafar da su duba yiwuwar sauko da farashin zuwa Naira 300 ko 250, ta yadda masu sha’awa za su samu damar saye.