✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta zama ’yar Arewa ta farko da ta zama Janar a Sojan-Ruwa

A Litinin da ta gabata, Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya ta yi bikin kara wa Kyaftin ta Sojan Ruwa, Jamila Malafa mukami zuwa Kwamanda ta…

A Litinin da ta gabata, Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya ta yi bikin kara wa Kyaftin ta Sojan Ruwa, Jamila Malafa mukami zuwa Kwamanda ta Sojan Ruwa, mukamin da ya yi daidai da Birgediya-Janar a Sojan kasa; wanda haka kuma ya sanya ta zama mace ta farko daga Arewacin Najeriya da ta samu wannan babban mukami.  

Shugaban bangaren Mulki da Tsare-Tsare na Hedikwatar Sojan Ruwa, Abuja, Riya-Adimiral Henry Babalola ya bayyana cewa wannan abin alfahari ne, ganin cewa mata kalilan ne suka taba samun irin wannan daukaka.

Ya kara da cewa, kafin ta samu wannan babban mukami, sai da Hukumar Sojan Ruwa ta aika ta zuwa kwasa-kwasai masu yawa da na kwarewar aiki daban-daban, kafin daga bisani ta samu madaukakiyar shahadar MNI.

Haka kuma ya ce wannan karin girma wata ishara ce ga mata sojoji, domin su kara himma a fagagensu, domin kuwa babu wata iyaka da aka gindaya masu na samun daukaka zuwa kowane mataki.

A nata bangaren, Kwamanda Jamila Malafa ta ce ita ce mace ta farko daga Arewacin Najeriya da ta fara samun wannan mukami na Janar a gidan Sojan Ruwa. Ta ce wannan karin girma da ta samu, zai kara mata azama da jajircewa wajen gudanar da ayyukanta ga Rundunar Sojan Ruwa da kuma Najeriya gaba daya.

Aminiya ta kalato cewa, an haifi Jamila ne a karamar Hukumar Gombi, Jihar Adamawa a shekarar 1965. Ta shiga aikin Sojan Ruwa a shekarar 1988, inda ta samu karin girma zuwa Jami’ar Sojan Ruwa a 1990.