✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta-zarcen Alpha Conde na jawo rikici

’Yan adawa a kasar Guinea na karawa da jami’an tsaro domin nuna rashin amincewarsu da yunkurin Shugaba Alpha Conde na tsawaita mulkinsa a karo na…

’Yan adawa a kasar Guinea na karawa da jami’an tsaro domin nuna rashin amincewarsu da yunkurin Shugaba Alpha Conde na tsawaita mulkinsa a karo na biyu.

Ma’aikatan lafiya a Guinea sun ce an kashe akalla mutum biyu, inda wadansu kuma suka samu raunuka a yayin wata zanga-zanga da mutanen kasar ke yi don nuna rashin amincewarsu a kan shirin Shugaban na son ya yi ta-zarce.

Jami’an tsaron kasar Guinea sun yi amfani da harsasai na gaske da gurneti mai gigitawa da kuma hayaki mai sa hawaye a kokarin da suka yi na kawar da masu zanga-zangar.

Masu zanga zangar sun kafa shingaye kuma sun rika kona tayoyi a yayin da suka rika jifan jami’an tsaro da duwatsu.

An rufe makarantu da kantuna a babban birnin kasar, kuma an ga wadansu ’yan sanda sun zagaye gidajen wasu jagororin ’yan adawa.

Wa’adin mulkin Shugaba Alpha Conde na biyu kuma na karshe a karkashin tsarin mulkin kasar zai kare ne a badi, amma da alama yana son ya yi ta-zarce.