Search
Subscribe
Ta’aziyar abokan aiki: Kanen Dodo da Malam Shehu da Aisha Agaie

Marigayi Bashir Musa Liman

Ta’aziyar abokan aiki: Kanen Dodo da Malam Shehu da Aisha Agaie

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un

Kowane mai rai mamaci ne

Wannan duniya ba ta kasance gidan zama ba.

Sai dai kawai hanyar tafiya zuwa mazauni ne

Allah Ya jikan Bashir Musa Liman da Malam Shehu Abubakar da A’isha Agaie

Yau dai muna cike da alhinin rashin ’yan uwanmu abokan aikinmu, wato Bashir Musa Liman da Shehu Abubakar da A’isha Agaie. Allah Ya jikansu, Ya gafarta musu. Kuma za mu bijiro da al’amuran da muke ganin muna tunawa da su, a lokacin da suke a raye, har bayan ransu. Kodayake Ita A’isha Agaie, duk da cewa na same ta a wajen aikinmu, babu wani aiki da muka yi, sai dai kawai na san takan rako Hajiya Safiya Dantiye ta kawo mana makala da mukan fassara mu sanya a jaridar Aminiya.

Labarin rasuwar Bashir Musa Liman, wanda mafi yawan abokan aikinmu ke yi wa lakabi da Kanen Dodo ko Karamin Dodo ya yi matukar tayar mini da hankali, domin ba a fi makonni ba muka yi wata muhawara da shi dangane da kalaman da ke kunshe a wakar wata ’yar karamar yarinya, inda muka yi ta kai-kawo a tunani kan abin da mutane ke ganin ba shi da muhimmanci, wato:

Agwagwa tana wanki, Omo ya kare wa zai sawo mata?

Marigayi Bashir Musa Liman shi ya bayar da amsar da ta gamsar da ni fiye da sauran manyan mutane da muka tattauna da su. Domin amsar da ya bayar game da wannan tambaya ita ce, “Mutumin da ya sawo mata na farko ta fara wankin, to shi ne ya kamata ya sake sawo mata.”

Wannan bawan Allah tun farkon haduwarmu da shi, lokacin da aka dauke shi aiki a Kamfanin Media Trust, aka turo shi jaridar Aminiya, kawai wata rana da suka yi kicibis da Mai Rumbun Ilimi, wato Malam Haruna Ibrahim jami’in da ke kula da dakin karatu, sai ya bayyana wa jama’a cewa, “Ga Kanen Dodo ya zo.” Ina kyautata zaton cewa tun daga ranar da al’amarin ya auku mutane da dama suke yi masa lakabi ko kiransa da sunan KANEN DODO ko KARAMIN DODO. Kasancewar muna aiki a sashe guda na wannan kamfani, wadansu duk sun dauki hakan ba tare da sun yi la’akari da cewa sunayenmu da na iyayenmu sun bambanta ba. Haka muka ci gaba da mu’amala ta aiki yana kirana Yaya Dodo, ina ce masa “Kanena MAN-KAZA.”

Wata rana a cikin shekara ta dubu karamin lauje da sili da karamin lauje ya ziyarci birnin Dabo, har ya sanar da ni cewa zai je gidan wata gwaggonsa da ke Unguwar Hotoro, don ana shirin zuwa gidan wani malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda za a gana da iyalan mutumin kan maganar auren ’yarsa da Bashir Musa Liman. Da jin wannan batu sai na garzaya Kasuwar Kofar Wambai ’Yan Kaji na sawo tsuntsun miya, kuma na sanar da Dodanniya cewa Kanen Dodo zai zo gidanmu ta yi mana girki. Cikin ikon Allah wannan al’amari bai tabbata ba, saboda haka na yi masa korafin rashin jin dadin zuwansa gidana. Da ya bayyana mini matsalar da ta faru, sai na yi fatan Allah Ya sanya hakan ya kasance mafi alheri.

Sannan akwai lokutan da idan na ce masa Man-Kaza, shi kuwa sai ya kira sunan ’yata ya ce ‘Asma’u man wadancan ne,” wato ya nuna wasu kananan tsuntsaye da ke tashi daga kan bishiya su hau falwaya. Ni kuwa sai in rika ba shi amsa da cewa, “Ai duk yaro man kaza ne, amma ita Asma’u man rago ce.” Wadansu ma da ke taya mu wannan barkwanci, har suka rika zuga ni da cewa “Ai Dodo man rakumi ne,” wai suna nuni da cewa na sha zuwa birnin Agadas da ke kasar Nijar.

Haka dai muka ci gaba da mu’amala, har lokacin da ya koma Jos da aiki, ni kuma na koma gida. Wata rana, bayan kammala azumin bana da muka yi gaisuwar Sallah, sai ya bayyana mini cewa ya bude wani shafi a shafukan Intanet, inda ya fara tattaunawa da masana da kwararrun masu gudanar da harkoin shirya fina-finai. Sai na ba shi shawara kan ya yi wani abu ko wata sana’a da za ta kawo masa kudi. Shi kuwa ya bayyana mini cewa ya bayar ana yi masa, ta yadda sana’ar ba za ta shafi aikinsa a Jos ba. Sai na ce masa idan harkar da ake gudanar maka ta yi albarka, to ka bayar da hakkin Allah, don dukiya ta yi albarka. Sai ya yi dariya. Haka dai muka rika tattaunawa ta wayar salula daga lokaci zuwa lokaci, har zuwa wannan lokaci da Allah Ya dauki abinSa.

Wannan dan bayanin da na  jero game da dangantakata ta aiki da mu’amalar da muka yi da Bashir Musa Liman, su ne muhimman al’amuran da zan iya tunawa.

A takaice dai, iya sanin da na yi wa Bashir Musa Liman, shi mutum ne da bai dauki duniya da fadi ba, sannan hazikin mutum ne da ke amfani da basirar da Allah Ya ba shi wajen inganta sana’arsa. Bashir dai matashi ne da zan iya kimanta shekarunsa da talatin da doriya, sannan dan jarida duk da kasancewarsa masani mai digiri a fannin nazarin ma’adanan da ake hakowa daga karkarkashin kasa.

…Shehu Abubakar (Mai Sunduki)

Hakika cikin makon nan ne dai muka samu labarin rasuwar Malam Shehu Abubakar, wanda mu ’yan makaranta muka rika yi masa lakabin Mai Sunduki, bisa la’akari da cewa lokacin da ya fara rubuto wa makarantar nan wasika, ofishinsa yana cikin wani katon sundukin tafi-da-gidanka ne, da ake girkewa a wajen ayyukan gine-gine, ko wani sansanin mutane da ke gudanar da wasu muhimman ayyuka ko ma ’yan gudun hijira.

Wannan bawan Allah dai gaba yake da ni a wannan aiki, don haka ba zan iya cewa ga lokacin da ya fara ba. Domin tsawon shekarun da na yi a wannan kamfani, a nan na same shi.

Wannan bawan Allah Ya yi labarai a jaridun Trust, amma iya zamana da shi ya fi shahara da labaran aika miyagun laifuffuka da suka danganci hada-hadar sha da fataucin miyagun kwayoyi, musamman ma ina iya tuna yadda ya rika bayyana yadda jami’an Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) suka rika bankado dabarun fataken. Sannan ya yi labaran aikin gona.

Akwai lokacin da ya kawo mini wani labari kan yadda jami’an Hukumar NDLEA suka bankado yadda ake boye kayan maye da ake safararsu a cikin akwakun agogo mai gwaiwa, kasancewar ni na yi aiki a kan labarin na kuma sanya shi a  jaridar Aminiya, yana fitowa har da ma’aikatanmu aka rika sanar da ni cewa akwai inda za a samu irin wannan agogo mai gwaiwa, wadansu har talla suka yi mini, wai ko zan saya, ko in hada su da mai saya.

Sannan zan iya tuna labarinsa na gonar maciji da ke cikin Jihar Nasarawa, wadda daga bisani aka ce mana ta wani babban soja ce, wanda a halin yanzu shi ne shugaban sojojin kasar nan. Shi ma labarin ya sanya mutane sun yi ta kai-kawo a tunani kan me ake yi da maciji, amma daga bisani mun ji cewa kamfanonin harhada magunguna na duniya ke amfani da dafin macijin.

Uwa-uba ya taba rubuto wa makaranta wasika cewa a irin barkwancinsa ya hadu da ’yan sama jannati sun yi masa waka, wadda ya rera kamar haka:

Edita na Aminiya

Da Malam na Aminiya

Dodo da Dodanniya

Ai duk yaran Malam Shehu ne.

Da na karanta, bayan na sanya a shafinmu na Makarantar Dodorido, sai na ba shi amsa da cewa:

Ko dai ya hadu da ’Yan sama Ja-ni-a-titi?

Allah dai ya jikan Malam Shehu Abubakar

**

Mun kuma samu labarin rasuwar wata tsohuwar Ma’aikaciyar Daily Trust, A’isha Agaie, wadda ta rasu bayan ta haihu, ta yi fama da jinya. Allah Ya jikanta, Ya gafarta mata.

Ina mika ta’aziya ga ’yan uwa da iyaye da abokan aiki. Allah Ya ba mu hakurin wannan rashi. Allah Ya gafarta wa wadanda suka riga mu gidan gaskiya, Ya kyautata makwancinsu; Ya sanya can ta fi nan. Mu kuwa da muka rage a wannan duniya Allah Ya kyauta karshenmu, amin summa amin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin