Search
Subscribe
Ta’aziyya : Haduwata da  Barista Yahaya Mahmood

Ta’aziyya : Haduwata da Barista Yahaya Mahmood

Marigayi Malam Yahya MahmoodRanar Juma’a 15 ga watan Nuwamba, al’ummar Arewa, musamman a Jihar Kaduna, suka wayi gari da bakin ciki da kunci, sakamakon rasuwar Babban Lauya, Malam Yahaya Mahmood.
Na samu labarin rasuwarsa da misalin karfe bakwai da rabi na yamma, bayan na dawo daga sallar Isha’i, na kunna Radiyon Tarayya na Kaduna, sai na ji sanarwar za a yi jana’izarsa a masallacin Almannar da karfe tara na safiyar Asabar 16 ga watan Nuwamba.
Na yi istirja’i, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”, na zauna cikin damuwa domin na tabbatar Musulmi da Arewa da ma Najeriya baki daya, mun yi babban rashi.
Daga nan sai na buga wa wasu abokan aikina waya don jin sanadin rasuwarsa, duk kuwa da na san ya dan yi fama da rashin lafiya a ’yan kwanakin baya har ta kai ga ya tafi Dubai domin a duba lafiyarsa, sai na ji ya rasu ne cikin ofishinsa, bayan ya dan kishingida a kujerarsa domin ya huta, sai ta Allah ta kasance a kansa da misalin karfe uku da rabi zuwa la’asar.
Wannan ya sanya na tuna da wannan ayar dake a cikin al’kurani kuma wacce a duk sanda na ji an ankaranta ko na karanta raina yakan sosu. Kulli nafisin zalikatil mau’t ( duk wani mai rai mamaci ne)
A safiyar Asabar, kodayake Allah bai sa na samu jana’izar ba, sai dai na raka shi zuwa makabartar titin Dawaki a Unguwar Sarki inda aka binne shi, na ga jama’a, daga wadanda ke cikin motoci zuwa masu tafiya da kafa daga masallacin Almannar da ke a titin Tafawa balewa, unguwar Rimi zuwa makabartar, kai ka ce sallar Juma’a ce.
Ganin haka ya sa na kara samun karfin zuciya tare fatan cewa lallai bawan Allah kuma mutumin kirki ne ya rasu, musamman ganin masu mulki da malaman addini da masu hannu-da-shuni daban-daban a tsakanin talakawan da suka hallara, makabarta ta cika.  Daga abin da na fahimta, wadansu ma ko saninsa ba su taba yi ba, sai dai jin sunansa da matsayinsa na mutumin jama’a kuma mai kishin Arewa da ma Najeriya baki daya. Allahu akbar!!
Lauya Yahaya ko Malam Yahaya Mahmood, kamar yadda akasarin mutane ke kiransa, mutum ne mai saukin kai. Duk wanda ya samu damar yin hulda da shi ko kuma ya samu damar sauraronsa a duk inda yake bayani a lokacin rayuwarsa, zai tabbatar da wannan.
Farkon haduwata da wannan bawan Allah, kimanin shekaru uku ke nan a lokacin da Editana, Malam Balarabe Ladan, ya nemi in jiyo ra’ayinsa a kan lamarin Almustapha   da ya ki ci ya ki cinyewa,  na buga masa waya na gabatar da kaina, sai ya yi min kwatancen ofishinsa. Da isa ta, sai ya ce, cikiin fara’a, “Kai ne daga Jaridar Aminiya”? Na amsa, sai ya ce, “Amma yaya na ganka cikin kananan kaya irin na ’yan boko? Na dauka zan ganka cikin dogayen kaya da hula, amma sai na ganka dan gaye”, sai muka yi dariya.
Tun daga wancan lokaci, sai na zama dan gida, kuma idan har bukatar jin ra’ayinsa, musamman kan wata dambarwar shari’a  da ta shafi kundin tsarin mulki ta taso da zarar na kira shi zai saurare ni.
Wani abin sha’awa ga wannan bawan Allah, a duk lokacin da ka kira shi a waya, zai dauka ba tare da bata lokaci ba ko ya san lambar ko bai sani ba. Ba kamar sauran manyan mutane ba da ke tsoron daukar lambar wayar da ba su sani ba.
Wannan na daya daga cikin halayen da ya yi fice a cikin sauran fitattun mutanen kasar nan, musamman ma dai irin hakurin da yakan bayar idan bai biya maka wata bukatarka ba, idan ayyukansa suka hana shi.
A watan Oktoban nan, a waya muka yi ganawar karshe da shi, yayin da na kai masa wata jarida da ya nema, amma ban sadu da shi ba, sai na ba masinjansa, sai ya turo min sakon tes me ya sa ban shiga mun gaisa da shi ba, na ce masa ba na son damunsa.  Sai ya ce in neme shi idan ya dawo daga Abuja a karshen mako, amma ban samu zuwa ba, sai dai bakin labarin rasuwarsa da na ji. Allah Ya gafarta masa, amin.
Gaskiya Malam Yahaya aboki ne ga kowa, musamman talakawa da kuma mu ’yan jarida. Za a dade ana tunawa da irin gudunmuwar da ya baiwa sashen shari’a na kasar nan.
A nan Arewa yana daya daga cikin lauyoyin da suka yi fice kuma suke da martaba a idanun jama’a. Saboda yadda ya rike mutucinsa wajen gudanar da aikinsa cikin gaskiya. Ga shi da mutunta duk wani dan Adam, saboda ba shi da girman kai. Kowa nasa ne!
Marigayi Malam Yahaya Mahmood ya rasu ya bar matarsa daya da ’ya’ya biyar. Allah Ya jikansa, Ya yafe masa duk kurakuransa wadanda ya sani da wadanda bai sani ba. Muna kuma yi masa kyakkyawar fata da addu’ar Allah Ya ba shi gidan Aljannar Firdausi, amin summa amin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin