✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyyar Marafan Sakkwato Alhaji Umaru Shinkafi

Na  dade  ina jin  labarinka, na  kuma  karanta  wasu  daga cikin   rubuce-rubucen  da ya shafe ka, ka  dade  kana burge ni,  musamman yadda  na ga …

Na  dade  ina jin  labarinka, na  kuma  karanta  wasu  daga cikin   rubuce-rubucen  da ya shafe ka, ka  dade  kana burge ni,  musamman yadda  na ga  kana girmama  na gaba   da kai,  kamar  yadda  na ga  a gabana  kana yi wa  marigayi  Alhaji  MD Yusufu,  Tsohon  Sufeto  Janar na  ’yan sanda.
Ban matsa kusa da kai  ba sai  lokacin  da  shirye -shiryen kaddamar  da  littafin   rayuwar  MD Yusufu na  Hausa ya  taso,   wanda  kai ne  mataimakin shugaban  shirye -shiryen,  ni  kuma ne na zama sakatare yayin da  Alhaji   [Dokta]  Ibrahim  Coomasie,  Shugaban  kungiyar  Tuntuba ta Arewa. [ACF]  ya kasance shugaba.
Mun rika  tattaunawa  da  kuma  waya  a kan yadda  taron ya kamata  ya kasance.  Wannann  ya  kulla  dangantakarmu   da kai, har  lokacin da  Allah ya sa  ka bar   duniya.  Wanda  kafin  rasuwarka  mun  shaku  shakuwar  da  ta kai ga har  akwai  lokacin  da ka  ce   ina  ma  mun  san  juna  tsawon lokaci,  saboda  yadda  muka  fahimci  za mu  iya amfanar  juna.
Na  sanka  a  matsayin  wanda  komai  kake  son ganin  an yi  shi  tsaf  yadda  yake, kuma  yadda  ya  dace. Kuma  kana  son  a  samu  kusan kashi  casa’in  da doriyar na makin  din  duk  abin  da aka  sanya   a gaba.  Kana  kuma  da  takatsantsan   ga duk  abin  da za ka  yi..
Ka  taba  rike ni  awa  uku ana  bugawa  da gyara  wata  takarda mai  shafi  uku kacal.  Don kana  son lallai kafin  ta fita sai  ta  samu  tabbacin inganci. Ina iya tunawa  na zo  gidanka a Abuja  daga  gidan MD Yusufu da  niyyar  ka duba  takardar,  kuma ka sa mata hannu daga  gidanka  niyyata  in wuce  Kaduna.
’Yan  gidanka suka shaida mini  cewa, in dai  har na zo  da takarda in soke maganar  barin   Abuja  yau. Tabbas abin  da  ya faru  ke nan.  Sai  da na yi  awa  uku  zuwa  hudu.
Kana  da    sha’awar  a magana  a rika bambance maka tsakanin ra’ayi da fahimta da   sharhi  da  kuma gaskiyar  labari.   Me  ya faru,  ya aka yi  ya faru?   Ya  faru  yadda  ya faru. Kafin  mai  bayar da  labari  ya yi   nazarin  duk   abin da  zai   fada  a karin  bayaninsa.
Kana sauraren magana atsanake, kuma  in za ka yi  tambaya. Tambaya  ce.  Wadda  amsarta   za ta  kasance  dole ka  fadi  gaskiya. In ma ka yi  wa  gaskiyar  kwaskwarima  to  za ka  gane  mutum.  Wani  lokaci  kana mayar da  tambaya ga duk amsar  da  ka samu.
Idan mutum  ya fahimci  abu  ba daidai ba, ka kan gyara masa. Ka ce  a’a,  ba haka  yake  ba,  sai ka fada  masa  gaskiyar  yadda  abin  yake. In kuma  ka ga bai  cancanta  ya sani  ba  sai  ka ce, abin da ka sani  ba  haka ba ne.
Kana  da taka tsantsan  wajen yarda  da  kowa. Kodayake ka taba  fada  mini  wata magana da na ji  dadinta. Ka ce  na  yarda  da  kai ne  saboda  wanda  yarda da  kai  nasan  bai yarda  da  mutumin   banza, shi ne  MD Yusufu. Na  tuna muna yin  wata  magana ne da ta  shafi  kasar  da   halin  da  take  ciki. Ka  fada mini. Wasu  zantuttuka  da ka ga    na yi  mamakin  da ka  yarda  ka  shaida  mini  su.  Sai  ka ce  ka da ka yi  mamaki.   Malam   kamar  yadda  kake  kiran  MD Yusufu ya yarda   da  kai, nima  shi ya sa na yarda  da  kai.
Ina  mamakin  yadda  kake  da  kokarin  mayar da  amsar  duk  wani  sakon waya da  ya  shigo  wayarka.  Za ka  karanta  kuma  za ka  bayar da  amsa.  Daka  buda  waya  kamar  yadda  naga  kana yi  a gaba na . duk  wani  sakon waya  sai  ka karanta  shi.  kuma  duk  wani  kiran  da  ba ka   amsa ba, sai ka  duba shi,  wani  ka  kira,wanda ba ka  gane  mai  kiran ba, kuma ka kyale.
Ba ka  wasa  da  addini,  ba ka kuma  wasa  da  hakkin  mutum. Ka taba  bugo  mini  waya  karfe  daya  na  dare. Ka ce  in bai wa  wani da ya yi  mana  wani  aiki kudinsa,  kafin  tara na rana:”Ka  kira   shi  ka biya  shi  cikin  iko  ka yi  maganar.’’  Da  wajen biyu na rana kuma in ga  sakon ka a waya  ka rubuta  cewa,  ‘ka yi  abin  da na ce.  Kuma  na gode.’
Hirarka  ta  karshe  da  ka yi da  jarida, ni na   roke  ka. Kuma  ka amince. Bayan ka yi  mini tambayoyi  na ba ka amsa.  Daga  baya  ka  ce.  To  kar tattaunawa  ta  wuce   a kan  Marigayi  Sardauana. Ita ce    hirar  da  aka yi,  kuma   aka  buga  a jaridar  BLUEPRINT. Da  hirar  ta fito  ka  shaida mini  cewa. lallai ka ji  dadi  ba inda  aka  samu matsala a wajen  rubuta  rahoton.
Allah  sarki.  Yanzu  ba zan kara  jin  wayarka ba,  wadda  ka kan bugo mini  cikin dare, wadda  dana  ganta  zan  sa ruwan  shayi  da lifton na  san   hira kake  bukata wani  lokaci. In mun  gama  sai  dai in dasa  da  sallar  dare  zuwa  asuba, sai  safe, har  na  saba al’amarin da ya zamar mini  jiki.
Kana  Ingila  kana son ka bugo  mini ka ji  me  kasarka  ke  ciki.  Wata  waya  da  ka bugo  ka ce  cikin   bacin  rai,  ‘wai   Alhaji  danjuma  da  gaske ne an kashe  mutane  da   yawa  a Zariya?’ Kafin in ba ka  amsa ka ce  ina  son ka je  Zariya ka  samo mini tabbacin  haka. Tunda   ka ce  kai kana  Katsina..  kana  magana  cikin mamaki.  A  maganarka   ka rika yin nazarin tsaro  a kan wannan al  amarin.
Na  rika karfafa  maka  gwiwar  ka rubuta  tarihin  rayuwarka ko na  kasar nan,   na daga  abin da  ka  sani  a tarihinta. Ka  taba  shaida mini  cewa  komai naka  yana  a  rubuce  a  tsanake. Don haka  ka da in damu, in  lokaci  ya yi  cikin  lokaci  kankane  za ka  iya  fitar   da shi  ga  al’umma  don su  karu  da  ilmin  da ka taskance.
Abubakar   Ado  mijinyawa, ya  shaida mini katafaren  mallakin  dakin karatunka, wanda  Allah  bai  sa  na samu  ziyarta  ba. Ya  fada  mini  cewa  gida ne, wanda  wasu  dakunan  cike suke da littafai,  inda  wani  masanin   ilmin   dakin karatu  ke  kula  da su.   Wasu  dakunan   kuwa  duk   jawabai ne naka,  wadanda ka  yi,  tare  da  rubutunka  tun kana   dan makaranta. Har   zuwa  lokacin  suna  a  tsare  a  ciki.
Wani   dakin kuma  kyaututtuka  ne da aka taba  ba ka.  Duk  an  tsara su an jera  da   rubutun  shekara  da   lokaci  da  wanda  ya ba ka.  Wani kuma  dakin kaya ne. na  tarihi, wadanda  suka shafi  rayuwarka. Hula da riga da takalmi  da   zobe da sauransu.
Allahu  Akbar;  wannan  ya sa   na gane   dalilin da  ya  sanya  ka   damu. Kuma ka so ka ga  an yi  da   kammala  aikin  ginin   dakin karatu  da ajiye kayan tarihi na MD Yusufu. Ka sha fada  mini cewa   in aka  gama  shi.za ku  mayar da wajen  abin  misali  da kuma  zuwa  a yi  bincike a duniya.
Kwana  uku  kafin  ka  bar   duniya, na  kira  waya  in yi  gaisuwa, sai  daya  daga  cikin masu  jinyarka, ya  dauka,  ya ce  kana   barci, ya ce  ina   cikin  ’yan kadan  da  ka bayar da  umurnin in  na  bugo  a  dauka, an fada  mini  cewa  kana  samun sauki.
Na je  Sakkwato  ta  aziyyarka. Na  kuma  ziyarci  kabarin ka. Ka ji  dadi,  an  rufe ka  kusa  da  mutanen  ne da ke  kyautatta  zaton  na kirki  ne  a  wajen  Allah. Makabarta  wadda  ke  samun maziyarta  sosai. kuma ana yi wa wadanda  ke kwance  addu’a, wato  Hubbaren  Shehu  Usman dan  Fodiyo, Alhaji  Umaru  shinkafi Allah ya  jikanka. Allah ya dayyaba zuriyarka. Amin.
Danjuma Katsina  . marubuci / dan jarida.    Shi ne  Sakataren Cibiyar Bincike da Tattara bayanai ta  MD Yusufu, (MD Yusuf  Research  and Decumentation  centre).  08035904408. Email. [email protected].