✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyyar marigayi Danyaya Nasarawa

“Allah kai ni Madina in mutu can.” Daya daga cikin baitocin wakar da marigayi Alhaji Danyaya Nasarawa ke nan wanda ya rasu ranar 7 ga…

“Allah kai ni Madina in mutu can.”

Daya daga cikin baitocin wakar da marigayi Alhaji Danyaya Nasarawa ke nan wanda ya rasu ranar 7 ga Disamban bana a garin Keffin Jihar Nasarawa.

Asalin sunan Alhaji Danyaya Nasarawa Alhaji Isma’ila Aliyu, kuma shi ne mahaifin fitaccen dan siyasar nan da ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a karkashin Jam’iyyar APC,  Alhaji Ahmad Aliyu Wadada.

Aminiya ta samu zantawa da wani aminin marigayin mai suna Alhaji Abdullahi wanda aka fi sani da  Sankira Ladan  wanda ya ce:

“Sunan mahaifin Danyaya Nasarawa Aliyu Sarkin Kasuwar Nasarawa. Asalinsa shi mutumin Isa ne da ke Jihar Sakkwato. Na san shi kimamin shekara 40 da suka wuce. Asalinsu masu sarauta ne ba maroka ba. Kuma a Nasarawa aka haife shi. Ya fara waka ne da wakar da samari suke yi wa gwauro a watan azumi, amma mahaifinsa ba ya son waka. A da yana waka shi kadai, daga baya ya fara sa kalangu da ganga sannan ya kara da masu amshi.”

“Ni ina yin aski, sannan na bari na fara bin sa. Mun fara zuwa Laminga da ke hanyar Nasarawa muna bin rugar Fulani muna yi musu waka su ba mu bale daya ko biyu, sannan mu sayar kimanin fam uku. Amma abin da ya sa ya bar garin Nasarawa ya koma Keffi shi ne domin yana da wani ubangida dan Sarkin Nasarawa mai suna Malam Zubairu Bamu da suka yi neman sarauta, sai uban gidansa Zubairu ba mu bai samu ba, sai abokin takararsa mai suna Malam Jibrin Mairiga ya samu sarauta. To Danyaya yana yi wa gwaninsa waka a bakandamiyarsa yana cewa:

“Zubairu Bamu,

“Dan Sanda da Hauwa,

“Kunkugurn cikin macizai, (…kuka).

“Da yake yana da hikima, kafin a wulakanta shi, sai ya yi hijira ya taho wurin Sarkin Keffi Ahmadu Mai Kwato, wanda asalinsa Katsina ne shi kuma Danyaya Bagobiri. Da ya fada masa abin da ya koro shi, sai ya ce ai duk da Keffi da Nasarawa uwa daya uba daya ne, sai ya ba shi fili a bayan fada ya ce ya gina kuma a nan ya zauna har rasuwarsa,” inji shi

Ya kara da cewa “Da ya tara kungiya mai yawa sai mu hau mota mu je Kaduna da Kano mu yi wasa, a nan kusa kuma muna hayar keke mu je Umaisha da Loko da Keffi, muna zuwa wurin masu arziki muna waka.

Daga nan ne ya yi auren farko inda ya auri mahaifiyar Aliyu Wadada mai suna Hajiya Iyatu. Ya rasu yana da shekara kimanin dari don ya girme ni.”

“Ni Sankira ina amshi, ina roko, kuma ni ne mai tara kudi in an dawo gida sai ya ce Ladan ina kudi, sai ya raba, sannan ya dauka ya ba ni sannan ya ba ni in je waje in sallami yara. Wanda ya fara yi masa kida shi ne Balale Maiganga,” inji shi.

Ya ce “Daliln da ya sa ya bar kida da wakk shi ne, dansa Alhaj Aliyu Ahmad Wadada ya hana shi domin lokacin ya ce tunda Allah Ya yi masa arziki, kuma ba a daraja mawaka. Shi ya sa ya bari. Wasan da ya je na karshe shi ne bikin nada Janar TY Danjuma sarauta a Lafiyan Bare-bare.”

Haka ma daya daga cikin yaransa mai yi masa amshi kuma wanda Danyaya ya biya masa kujerar Makka, Alhaji Mairiga Usman Andun Galadima Keffi ya ce:

“Mun yi kimanin shekara 40 da marigayin, kuma zama na mutunci da karramawa ba mu ci amanar juna ba har ya rasu, kuma zuriyarsa na kaunarmu. Na zo Keffi Adun Galadima don yin karatu, daga nan na koma bin sa. Halinsa ya sa mahaifina kuma tsohon dan dambe a Keffi Alhaji Usman shi ma ya shiga roko. Shi ya biya min kudin zuwa Makka, kuma muna tare da shi a Madina lokacin da jirgin alhazai ya fadi a Kano. Ya rasu ya bar mata uku, Gimbiya Sodangi da Hajiya Uwa da Hajiya Salamatu Loko.

Danyaya na da da mai suna Aliyu Nakande, sai shi Danyaya, sai Danlami da Kawata. Su hudu ne a gidansu. Kuma daga baya yana son wakar Sardauna. Ba ya siyasa, kowa nasa ne, bai yi NEPU ko NPC ba,” inji shi.

Ya kara da cewa “Kuma da muka je Kano muka yi wa Sarkin Kano Ado Bayero waka, sai ya ba mu fili a Gyadi-Gyadi ya ce Danyaya ya dawo Kano ya zauna, amma ba mu san yadda ka yi da filin ba.

“Mun taba zuwa Ghana muka yi wata uku wurin Salihu Maikankan sannan muka dawo gida. Shi Maikankan Bakano ne asalinsa suka zo Keffi daga nan ya wuce Ghana. Wani abin mamaki kuma shi ne lokacin da Sardauna ya zo Keffi, sai ya ce wa Danyaya idan kana son ganina, ka same ni a Kaduna sai muka bi shi Kaduna har ya ba Danyaya wata riga aska biyu, sai mun daga mun rike masa yake tafiya da ita don girma, amma daga baya ya daina sawa don gudun kada sarakuna su yi fushi, amma ya ce ba zai rabu da rigar ba har sai ya mutu a raba gado da ita,” inji shi.

Ya ce “Abin juyayi da ya faru da mu shi ne muna tafiya za mu bikin nada Sarkin Suleja Alhaji Awwal Ibrahim sai wata mota ta fito daga daji ta sa motarmu ta kife, ni sai da na yi jinya, amma Danyaya da Ladan ba su yi ko kwarzane ba.”

Bugu da kari daya daga cikin ’ya’yan margayin mai suna Alhaji Halilu Wadada ya shaida wa Aminiya cewa, mahaifinsu ya rasu ya bar ’ya’ya 19 wanda Alhaji Aliyu Wadada shi ne babba da jikoki fiye da dari da tattaba kunne fiye da 60.