Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Ta’aziyyar marigayi Hosni Mubarak

Marigayi Hosni Mubarak, tsohon Shugaban Qasar Masar

Ta’aziyyar marigayi Hosni Mubarak

Marigayi Shugaban Masar Hosni Mubarak yana daya daga cikin shugabannin Afirka da suka ja zarensu na dogon lokaci suna mulki. An haifi marigayi Hosni Mubarak ne a kauyen Kafr Al Musayihah da ke kusa da Kogin Nilu ranar 4 ga Mayun 1928. Sai dai mulkinsa ya bar mummunan tarihi saboda yadda ake kallon mulkinsa wanda ke cike da cin hanci da musguna wa jama’a daga ’yan sanda da danne ’yancin siyasa tare da haifar da matsalolin tattalin arziki.

Sai dai ya sha musanta cewa shi dan-kama-karya ne, inda ya ce tarihi zai ne kawai zai wanke shi a matsayin shugaba dan kishn kasa da ya bauta wa kasarsa ba tare da son rai ba.

Ya shiga makarantar horar da sojin sama ta Masar ac 1949, inda ya zama matukin jirgi bayan ya shekara guda. Daga nan ne likkfarsa ta yi gaba har sai da ya zama Babban Kwamandan Mayakan Saman Kasar a  1972.

Shekara guda bayan nan ne, Mubarak ya zama wani jarumi a kasar sakamakon yadda rahotanni suka nuna mayakan saman Masar din sun yi wa dakarun Isra’ila mahangurba a yankin Sinai lokacin Yakin Yom Kippur.

Ya kuma bada gagarumar gudunmawa a sasantawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu. Hosnin Mubarak, yana Mataimakin Shugaban Kasar Masar a ranar 14 ga watan Oktoban 1981 aka yi wa maigidansa, Shugaba Anwar Sadat kisan gilla  lokacin da yake duba faretin soji.

Mubarak wanda a lokacin ke zaune kusa da Sadat, ya tsira da karamin rauni a hannu lokacin da ’yan bindigar suka bude wuta kan motar duba faretin. Kwana takwas bayan nan, sai aka rantsar da tsohon Kwamandan Mayakan Saman a matsayin Shugaban Kasa, tare inda ya yi alkawarin dorawa daga inda wanda ya gada ya tsaya.

Mummunar matsayarsa ta fuskar tsaro ta ba shi damar ci gaba da wanzuwar yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A lokacin mulkinsa, Masar ta kasance babbar kawa ga Amurka a yankin, inda kasar ke samun tallafin soji na Dala biliyan 1.3 kowace shekara daga Amurka har zuwa shekarar 2011 lokacin da zanga-zanga ta jawo aka yi waje da shi daga kan mulki.

An yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai a shekarar 2012 kan laifin hada baki wajen kashe masu zanga-zanga 239 lokacin tarzomar bijirewa gwamnati na kwana 18. Sai dai Kotun Daukaka Kara ta Kasar ta bayar da umarnin a  sake  yi masa shari’a, inda daga bisani aka wanke shi tare da manyan hadiman gwamnatinsa. Daga karshe aka sallame shi a shekarar 2017.

A shekarar 2015 tare da ’ya’yansa biyu an same su da laifin karkatar da dukiyar kasar tare da  amfani da kudaden wajen inganta gidaje da kayayyakin alatun iyalinsa.  An yanke musu hukuncin daurin shekara uku. Tun bayan kama shi a watan Afrilun 2011, Mubarak ya shafe kusan shekara shida na daurin a gadon asibiti.

Bayan da aka sako shi, an sauya masa matsuguni zuwa unguwar Heliopolis da ke birnin Alkahira. Galibin mutanen Masar da suka yi rayuwa lokacin mulkinsa, suna yi wa gwamnatinsa kallo “ta danniya kuma mai matsnancin Jari-Hujja”.

Hambare gwamnatinsa ya haifar da yin zabe a karon farko a kasar, wanda ya kawo gwamnatin marigayi Shugaba Mohammed Morsi.

Sai dai Morsi ya shafe sheakara daya ce kawai a gadon mulki sai mummunar zanga-zanga a shekarar 2013 ta yi awon gaba da mulkinsa, inda babban hafsan sojin kasar na lokacin Janar Abdel Fattah el-Sisi, ya hambare gwamnatinsa, kuma har yanzu shi ne Shugaban Kasa.

Jiga-jigan gwamnatin Mubarak dai an rika wanke su daya bayan daya daga tuhumce-tuhumce, kuma dokokin takaita ’yancin siyasa suna haifar da fargabar a zukatan masu rajin sauyi cewa bakon da aka raka yana neman dawowa.

Dan uwar mai dakinsa, Janar Mounir Sabet, ya fada wa Kamfanin Dillanicin Labarai na AFP cewa Mubarak ya rasu ne a Asibitin Sojoji na Galaa da ke birnin Alkahira.

A karshen watan Janairu ne aka yi wa Mubarak tiyata. A ranar Asabar da ta gabata ce dansa, Alaa ya ce yana bangaren kula da marasa lafiya na  musamman a asibitin.

Fadar Shugaban Masar ta fadi a cikin wata sanarwa cewa tana alhinin rasuwar Mubarak kasancewarsa “Shugaban soji kuma sadaukin yaki” ta kuma mika ta’aziyyarta ga iyalan Mubarak.

An yi masa jana’iza ta girmamawa ta soji, kamar yadda wata majiyar sojin ta tabbatar wa Kamfanin  Dillancin Labarai na Reuters.

Mubarak ya shafe shekara 30 a kan mulki kafin juyin juy- halin Masar ya yi awon gaba da gwamnatinsa a wata tarzoma da ta barke a wasu kasashen Larabawa a shekarar 2011.