✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyyar tsohon Shugaban Kenya Daniel Arap Moi

  Tsohon Shugaban Kenya Daniel Arap Moi wanda ya jagoranci kasar daga 1978 zuwa shekarar 2002 ya rasu a ranar Talatar da ta gabata yana…

 

Tsohon Shugaban Kenya Daniel Arap Moi wanda ya jagoranci kasar daga 1978 zuwa shekarar 2002 ya rasu a ranar Talatar da ta gabata yana da shekara 95.

Shugaban Kenya Mista Uhuru Kenyatta  ne ya sanar da rasuwar tsohon Shugaban wanda ya kwashe shekara 24 yana mulkin Kenya, inda ya sanar da zaman makoki har zuwa lokacin da za a yi wa Moi jana’iza.

Daniel Arap Moi wanda malamin makaranta ne shi ne ya gaji wanda ya samar wa Kenya da ’yancin kanta wato Jomo Kenyatta lokacin da ya rasu shekara 42 da suka gabata.

An haifi marigayi Daniel Arap Moi ranar  2 ga  Satumban 1924, kuma ya hau karagar shugabancin Kenya a 1978 bayan rasuwar Shugaban Kasar na farko Jomo Kenyatta.

Wannan ne karon farko da ya soma samun nasara a harkokin siyasa, inda ya yi wa fitattun ’yan siyasar kasar ba-zata wajen zama Shugaban Kasa.

Mista Daniel Moi mutum ne mai shiru-shiru, kuma wannan shiru-shiru nasa ne ya sa ya shafe tsawon lokacin yana mulki.

A farkon shekarun shugabancinsa, mutanen kasar Kenya sun hada hannu da shi domin gina kasar, inda ya yi amfani da wani salo mai taken ‘Nyayo,’’ wanda a harshen Swahili ke nufin “Bin sahu.”

Mista Moi yana da farn jini a tsakanin mutanen Kenya, musamman a wurin mutanen da ke kaunar ci gaba. Sai dai wadansu su zargi marigayin da mulkin kama-karya lokacin da ya jagoranci kasar, yayin da a bangare daya ake yaba masa wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar, a daidai lokacin da kasashe makwabta irin su Rwanda da Burundi da Somaliya ke fama da Yakin Basasa.

Bayan da aka yi masa yunkurin juyin mulki a 1982, Mista Moi ya sauya salo inda ya rika takura wa abokan adawa  wadanda suka rika kiransa da mai mulkin kama-karya. A zamaninsa an kama mutane da dama ba tare da kwakkwaran dalili ba. Daga nan kuma ya soma sanya kabilanaci da take hakkin dan Adam kuma aka zarge shi da kashe masu adawa da mulkinsa.

A 1990 Shugaba Moi ya rikide ya zama cikakken mai kama-karya. Sai dai kasashen duniya sun matsa masa lamba domin ya bar jam’iyya fiye da daya ta taka rawa a harkokin siyasar kasar, sannan suka bukaci ya sanya wa’adi a tsarin mulki kasar.

Amma gwamnatinsa ta yi raddi ga masu zanga-zanga inda ’yan sanda rike da kulake suka rika dukan shugabannin jam’iyyun adawa da magoya bayansu.

Bayan da ya raba kan ’yan adawa ne, ya sake lashe zaben Shugaban Kasa a tsakanin 1992 zuwa 1997.

Gwamnatinsa ta yi fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa, mafi shahara a cikinsu shi ne wanda ya bayar da biliyoyin Dala ga wani kamfanin hakar gwal na boge, inda aka zarge shi da hannu kai-tsaye a cikin batun. Wannan batun ya mamaye lokacin mulkinsa, sakamakon bacewar Dala biliyan daya daga Babban Bankin Kasar wajen fitar da gwal da lu’u lu’u na bogi zuwa kasashen waje.

Sannan cin hanci ya zama ruwan dare a Kenya a zamanin Arap Moi yayin da rashin aiki ya yi katutu.

 

Ya sha musanta zargin

Bayan da wa’adin mulkinsa ya kare a shekarar 2002, Mista Moi ya zabi dan lelensa Uhuru Kenyatta a matsayin mutumin da zai gaje shi.

Mista Uhuru, wanda ake ganin a matsayin mutumin da ba ya da ra’ayi na kansa, ya sha kaye a hannun Mista Mwai Kibaki. Daga nan ne Mista Moi ya yi ritaya daga harkokin siyasa kuma ya fuskanci ihu daga wurin dubban mutanen kasar ranar da ya mika mulki ga Mista Kibaki.

Masu sharhi sun ce ya ci gaba da yin tasiri a sha’anin siyasar Kenya ta bayan fage.

Kuma Mista Moi ya yi sa’ar ganin Uhuru Kenyatta ya zama Shugaban Kasar a shekarar 2013.