✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tafiya mabudin ilimi: Sallama da Brunei

Daga A’ishatu Mumina Usman Kafin mu bar Brunei, mun halarci ban-kwana da gawar wata yarinya Lizza, ’yar shekara tara, mutuniyar Holland. Ta hadu da ajalinta…

Daga A’ishatu Mumina Usman

Kafin mu bar Brunei, mun halarci ban-kwana da gawar wata yarinya Lizza, ’yar shekara tara, mutuniyar Holland. Ta hadu da ajalinta ne a gabar ruwa [beach]. Tana zaune da yara da iyayenta a kan wani icce, sai ambaliyar ruwa ta koro wata karyayyar katuwar bishiya daga ruwan, wadda ta buge ta a kai. Kafin a je asibiti, an gama. An gayyaci dukkan iyayen yara na Tera¬¬ja, don taya su alhini. Yara sun rubuta kyawawan halayen yarinyar a takarda, sun kai. Ko za a saka ne a cikin akwatin gawar, ta tafi da shaidarta, oho!
Muna nan aka tafi da gawar a bakar mota da take tsakiyar jerin motoci. A bayan motar gawar, sai motar iyayen yarinyar, a bayanta kuma akwai motar kakanni su uku, a bayansu kuma `yan uwan iyaye da sauransu. A gaban motar gawar, akwai abokan aikin iyayen da abokai da sauransu.
Ban ga matsanancin kuka ba, watakila don mun je ban-kwana da sati daya da mutuwar. Hakika mutuwa ba dadi a gun kowa. Dukkan iyayen yaran Teraja, kowa ka ga fuskarsa, akwai alhini. Na ji ana rade-radin cewa za a kone gawar, a dure a kwalba, a tafi da ita Holland. Wasu kuma sun ce za a tafi da gawar ne, hakika, kuma tana gurinsu.
Mun yi wata uku a Brunei ban taba ganin kai gawa makabarta ba, watakila don ba a cikin gari muke ba. Watakila kuma suna da saukin mace-mace, amma mun ga makabartu na musulmi da ’yan buddha. Makabartar musulmi da na gani a gundumar Kuala Belet ne, katuwa ce, kuma an kewaye ta da katuwar katanga mai fenti fari da adon fitilu, ciki da waje. kabrukansu suna sumuncewa ne tare da kafa alluna don shaida kuma akwai fulawowi sosai-sosai, don haka wurin yana da kyan gani da kuma ni`ima. Allah Ya sa can ma haka, amin. Kuma mukan ga motoci, watakila masu ziyara ne.
kabrukan ’yan buddha a unguwar Syria na ga ba a kewaye ta da tsawo ba kuma kabarin yana kama da kujera, amma tana da bisa {kamar ta dakin cin abinci}. Sannan girma-girma ne, ba kamar na musulmi ba, wanda yake aune kuma a kwance. Girman kabarin ko ya danganta da ilmi ne ko arziki ne ko mulki ne? Oho. A misalin inda za ka zauna a kan kujera, a nan kuma kasa, za ka hango har da ciyayi, don haka nake tsammanin suna binne gawar ne a tsaye, kuma ban taba ganin maziyarta ba.
A hanyar gundumar Tutong na ga  wata  makabartarsu a kan tudun badalar garin, domin Brunei tana da tudun tarin kasa da yawa, kamar badala, don haka za ka yi tsammanin dutse ne, amma ba haka ba ne, su basu ma da duwatsu. A garin Jeridong na ga makabartar musulmi tana da girman gaske kuma kewayenta ba shi da tsawo, don haka kana hango (cikin)ta sosai. Ita ma tana da fulawowi, amma ban ga akuya ko jaki a ciki ba, kuma ba a buga kwallo a ciki. Ina kyautata zaton ba a yanke kawuna da sassan jiki. Ban ga makabartar kiristoci ba, watakila ba su da yawa ne domin cocinsu ma daya muka gani a cikin wata makaranta (St Johnson) kuma karami ne sosai.
Mun bar Panaga:
Mun daure kayanmu, babbar jaka da karamar jaka (hand luggage) tare da auna shi a kan sikeli na mutane, don kada mu haura nauyin kilo ashirin, idan ya haura da daya ko biyu za su kau-da-kai. Amma idan ya haura fiye da haka, ko ka biya harajinsa, ko ka bude ka rage, su zuba a shara, don su ba su da bukatarsa, ba kamar Najeriya ba ne. Mun yi sallar La’asr (kasr) muka hadu muka yi addu’a, muka fita aka rufe gidan. Mun bar mai aikinsu mai suna Hajja Julma Hamza ’yar kasar Filifin. Muka yi sallama da ita, na ce mata, ‘sai kuma (kila) a lahira’.
Mun bar Panaga karfe biyar na yamma ranar Juma’a 25-03-2013, mun isa filin jirgin saman kasar Bandar Seri Begawan da karfe 06 :30 na yamma. Muka je aka auna mana babban kayanmu, a nan kuma muka tashi, sai a Lagos.
kasashe uku (3) da muka sauka ciki – Hadaddiyar Daular Larabawa (U.A.E) da Brunei da Malesiya, suna da matsanancin tsaro da bincike, amma na Brunei ya fi na sauran. Madakatar binciken Brunei ta kai bakwai (7). A madakata ta shida (6) na ga wani allo da aka rubuta, ‘idan ka shige nan ba a buga maka hatimi ba, to za ka yi jarun na shekara biyar da tara, wani kuma babu tara’, kuma na san za a aikata, domin mun yi niyyar zuwa Malesiya mu bakwai (7) ranar 18-02-2013, sai aka sami banbancin lamba (figure) wallahi, sai dawowa muka yi, tikitin ya tafi a banza a wofi, shi ne sai ranar 01-03-2013 muka koma. Madakata ta bakwai ita ce jami’ar za ta kalle ka, a ilimi irin na saninta, sannan ta shafe ka, sannan kake da damar shigewa. Amma a Malesiya da Dubai suna da madakata hudu ko biyar, na mance hakika.
Mun tashi daga Brunei 08:30 na dare, muka isa 02:30 na dare, sannan muka fita 06:30 na asuba, don wurin da nisa kuma tafiyar kafa ce, tafiyar jirgin kasan ba ta da yawa. Mun rabu da Zatu a madakata ta daya, domin ita kadai ta rako mu, sai muka karasa sauran. Muna jiran lokaci, sai na ji ana kiran A’ishatu Muminaa Usman!!!, a amsa kuwwa, na mike a cikin darurruka, cikin  tsoro (don ma ba ni da gigita) na hau ‘lift’ na koma madakata ta daya, sai na ga Zatu, ta ce ai ta manta da ‘boarding pass’ ne a jakarta, na karba muka yi sallama na koma. Wallahi, mun yi sa’a da wahalar da muka sha a farko (Dubai) da mun maimaita irin ta.
Tsokaci
Yayunmu iyayen yara; da ’ya’yanmu iyayen yara; da jikokinmu iyayen yara, duk suna kokari a kan makarantar yara kamar: Biyan kudin makaranta da litattafai. Kai su makaranta. Kula da karin karatunsu. Da kuma tarbiyya. Don haka nake son yaran duk su dage a kan karatun da kuma juya Turanci a baki, domin ni kam na leka, na kuma hanga, ban ga wata kasa a fadin duniya da take ji da kanta don: karfin arzikinta, ko karfin fada-a-ji da makamanta, ko karfin yawan jama’arta da za ta kawo harshen ta ya firgita Turanci (sannu Turanci).
Dosowa gida Najeriya : Mun bar Dubai 26-03-2013 ranar Asabar da karfe 08:30 na safe kuma za mu sauka Lagos 12:45 na rana. Zaman jirgi yana da takura sosai, saboda awowin sun yi yawa kuma kujerarka kadai ka mallaka, don haka sai kana kai-komo a ciki ko kuma ka mike a tsaye. A yawon da na yi a jirgi, na ga abin mamaki iri biyu: Na ga wata Bayaraba tana sallar azahar da la’asar kuma kasaru, to a ina ta samo kiblar? Na ga lokaci ake yi wa sallah, mun baro Dubai lokacin walha, za mu iso Najeriya farkon azahar, to a wannan tsakanin ina lokacin sallar? Kuma kamar an ce ba a sallah a sama, sai lokacin jihadi!
Abu na biyu kuma shi ne, na ga wasu mata biyu a dakin masu rabon abinci (air hostess) suna rokon wani abu, amma ba sa son na sani, watakila suna zaton ni ’yar jarida ce. Matan, watakila suna rokon ragowar abincin jirgi ne. Tambaya nake, don Allah wannan wulakanta kai ne ko hadama ce ko kwadayi ne? Kwa taimaka min da amsa.
A wasu lokatan kuma ina lura da yanayin tafiyar jirgin ta na’urar da nake kallo (tb screen). Na’urar tana nuna yanayi irin na masu ilimin yanayin kasa (geography), tsula gudun da jirgin yake yi, amma mu da muke ciki, kamar ba ya tafiya sosai kuma da nisan tafiyar a samaniya da keta ko haura tozayen gajimare. Na’urar tana nuna inda jirgin ya taso da inda yake da kuma inda ya dosa, duk kuma kilomitocin da awowin a kididdige. Nazarin yana da ban sha’awa, ko don ina son sanin yanayi ne, tafiyar jirgi a sama wata babbar kudura ce, ba da dare ba ko da rana.
Mun sauka a babbar kasarmu Najeriya da 12:45 na rana, mun tafi daukar babbar jakarmu tare da Alhaji Matawalle, abokin Mustapha Aminu, amma ba mu samu ba saboda mun yi ‘checking’ kayanmu a Brunei. Don haka ba su iso ba, sai bayan kwana uku Alhaji Matawalle ya turo su Kano ‘airport’.
Tasi ta zo ta dauke mu da wani yaro babba, ta hannun ransa ya dade (Mustapha). Mun koma karamin filin jirgin da zai kai mu Kano. Sun ce za mu tashi 02:30 na rana, amma ba mu taso ba sai 07:00 na magariba. Najeriya ke nan! A nan kuma na ga Yarabawa sun mana wayo sosai, domin ‘airport’ dinsu ta yi kamanceceniya da ta inda duk muka sauka. Allah Ya kawo canji!!
Mun shigo jirgin Kano karfe 07:00 na magriba. An ba mu dunkulallen burodi da kwalin ‘boost’. ba kamar sauran tafiyar ba da muke cin kwalan da makulashe har sai mun bar shi, ko don yawa ko don jagwalgwalonsu. Hajiya Fatima Muhammad (Sabuwa) ba ta cika cin wannan jagwalgwalon ba, domin ta fi ni kyama. Masu tarye sun iso, mun yiwo tafiya sosai daga filin jirgin zuwa ga masu tarye, ba kamar Lagos ba da sauran wuraren da muka je, inda ake hada mafitar jirgin da dakin da za ka shigo na masu tarye. Mun shigo mota tare da haske a kan titi. Na shiga gida (cikin) duhu kirin tare da yara ’yan tarye da yawa. Na shiga wajen Nene, sai na ga ba ta tsufa ba, amma ta kankance.
Dukkanin gidan mun hadu mun yi hamdala. Inda tafiya ta fi mutuwa ke nan!
Ina fatan Allah Ya hada mu a kowace irin tafiya da ’yar uwata Hajiya Fatima Muhammad (Sabuwa). Da ma bambancin shekarunmu kadan ne, kuma tare muka taso da yarinta a Wudil kuma mun yi ’yan matanci a Kano tare.
Jirage: Jiragen da muka hau sun kai takwas (8), zuwanmu da dawowarmu, su ne: Kano-Lagos, Lagos-Dubai, Dubai-Brunei, Brunei-Malaysia, Malaysia-Brunei, Brunei-Dubai, Dubai-Lagos da kuma Lagos-Kano. Mun gode Allah.
Tanadi: Duk bakon matafiyi ya tabbatar yana dan gwada oga Turanci, kuma da ma na san sai lafiyayye, don tafiyar da gajiya.
Matafiyi ya yi tanadin alewa ko cingam ko kuma ya yi ta kakaro hamma, don wani irin ciwon kunne. Yara suna kuka sosai don ciwon da suke ji.
kima: Ko da lalacewar Najeriya ta bangaren miyagun halayenmu ; da arzikin mai da ba a mora ba ; da dimbin albarkatun kasar da ba a tono ba ; da yalwar kasar da ba a noma ba ; da kuma dimbin yawan mutanen da ba su san kimarsu ba, duk da haka Najeriya tana da ragowar kima a Afirka da sauran wasu sassa na duniya, musamman ma Brunei da take wani loko a boye. Idan suka tambaye mu ‘daga ina?’ Muka ce daga Najeriya, yanda suke nuna kauna da kima, kamar lokacin su Tafawa. Watakila ba su san cikakken labarin danyen aikinmu na assha ba.
Godiya: Alhamdulillahi! Muna godiya ga Allah da Ya ba mu sanadin tafiyar da kuma lafiyar. Allah Ka yi dadin tsira ga Annabinmu da aka cika duniyar kasa da sunansa, aka cika duniyar Mala’iku da ambatonsa kuma aka yi ado da sunansa a Aljanna. Allah Ka sa ya kirawo mu, mu ji shi, mu amsa, kuma mu bi shi, domin kowa ya san sai da shi zai tsira. Na dada jin tsoron binciken lahira, saboda binciken kasar Asiya.
Malama A’ishatu (08132526301)