✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tafkin Gwakuru: Rafin da ke da dimbin kifin da ba a ci

Rafin Gwakuru wani karamin tafki ne ko kududdufi da ke yankin Kagarko ta Kudu a Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna. Takfin wanda yake da…

Rafin Gwakuru wani karamin tafki ne ko kududdufi da ke yankin Kagarko ta Kudu a Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.

Takfin wanda yake da tsohon tarihi da abubuwan al’ajabi iri-iri, shi ne ke shayar da mutanen Kagarko ruwa kuma bai taba konewa ba, rani da damina, kamar yadda magadan rafin suka shaida wa Aminiya. Kuma Aminiya ta gano babu ta inda ruwan  tafkin yake da wata mahada da wani rafi.

Ruwan yana kewaye ne da wasu bishiyoyi manya, kuma da damina wurin gwanin ban sha’awa, inda gefensa kan yi wasu ’yan ciyayi da sukan yi sunkuru, ruwansa kuma tar-tar yake, wanda ya sanya ake iya ganin abubuwan da ke karkashin ruwan. Sai dai idan an yi ruwan sama ruwan yakan jirkice ya zama ja, kamar yadda idan an tashi aikin yasarsa, yakan koma kamar turbaya.

Akwai macizai da kifaye a cikin tafkin

Akwai kifaye iri-iri masu ban sha’awa da kuma wasu macizai launi-launi da za ka yi ta ganinsu suna ta watayawa a cikin ruwan tafkin, kuma a haka mutanen yankin ke yin harkokinsu a wurin tare da dibar ruwa ba tare da wadannan macizai sun cutar da su ba.

A kowace shekara mutanen garin sukan ware wata rana guda da sukan yi bikin yashe ruwan, inda mata da maza, yara da manyan kan halarci bakin rafin don kallon wadannan halittu da yadda ake gudanar da yasar.

Aminiya ta halarci bikin yasar na bana wanda ya gudana a ranar Asabar da ta gabata.

‘Kifaye da macizan duk iskokai ne’

Da yake bayyana wa Aminiya tarihin rafin, daya daga cikin magada wannan rafi, Sarkin Leman Sarkin Kagarko, Malam Sa’idu Madauci, ya yi amanna cewa dukkan kifaye da macizan da ke ciki, asalinsu iskokai ne wadanda suka gada tun iyaye da kakanni.

Ya ce a duk ranar da za su yi yasar, sai sun zo cikin dare da misalin karfe daya sun zuba wasu magunguna kafin washegari su sha magani su hallara don aikin yasar.

“Maganin da muke zubawa a wajen cikin dare shi ke sa duk wani maciji da ba na wajen ba ya tashi a daren, sannan manyan macizan wajen su boye su bar kananan ta yadda ko an zo ba za a gan su ba sai dai kananan ciki,” inji shi.

Sa’idu Madauci, wanda shi ne ke kula da wadannan kifaye da macizan da duk abin da ya shafi takfin, ya shaida wa Aminiya cewa Malam Sa’idu Ibrahim wanda shi ne babbansu shi ne Sarkin Rafin yanzu, amma saboda lalura, Madaucin ne yake gudanar da sauran ayyuka. Ya ce sun gaji wannan sarauta ce daga wajen kakanninsu fiye da shekara 200, inda ya ce sarautar ta samo asali ne daga wata mata da ta zauna a wajen wacce ake kira Ya Sabulu. Ita dai wannan mata, kamar yadda ya ce, ba ta taba haihuwa ba, sai dai wani yaro da aka ba ta rikonsa, wanda a karshe shi kuma ya gaje ta, bayan ta nuna masa duk abubuwan da suka jibanci tafkin da abubuwan da suke cikinsa.

‘Duk wanda ya ci ko ya kashe kifi ko maciji zai mutu’

  Wani yanki na tafkin
Wani yanki na tafkin

Magajin Rafin wanda kuma ya fito daga wannan tsatso, ya ci gaba da cewa, “Babu wani da zai taba maciji ko kifin da ke cikin tafkin da sunan kashewa ko dafawa face ya mutu a wannan rana.’’ Ya  ce, duk wanda ya debi wannan ruwa sannan ya zo wajensa ya ba shi wasu magunguna to insha Allahu ko mece ce matsalarsa za ta kau.

Madaucin Kagarko, wanda ke kula da bada magunguna ga wadanda ke aikin yasar, ya ce, “Duk kifayen da ka gani ba a cin su,” inda ya bada misalin wata ’yar kabilar Ibo mai suna Ngozi da ta zo wajen don diban ruwa, to da ta ga kifayen sai kawai ta kama guda daya ta je gida ta yayyanka shi gunduwa-gunduwa, bayan an fada mata cewa ba a cin kifin, amma ta yi ganganci ta dora a kan wuta domin ta dafa ta ci.   “Zuwa can bayan wani lokaci da ta je ta bude tukunyar sai ta ga kifin ya koma ya hade kamar yadda ta dauko shi daga rafin. In takaita maka labari, a wannan ranar dai matar nan ba ta kwana da rai ba,’” inji shi.

Ya kara da cewa, “Akwai matar Sarkin Fawa ma wadda ita a cikin rashin sani ta kama kifin da niyyar ta ci amma da ta je ta dora a wuta bayan ta yayyanka sai ta ga kifi ya ki mutuwa, inda ganin haka bayan an fada mata sai ta yi sauri ta dawo da shi cikin ruwan ta ajiye shi, sai dai an yi sa’a saboda rashin sani da dawo da kifin da ta yi cikin ruwa, ya sa ba ta mutu ba.”

‘Za a iya samun kudin shiga a tafkin’

Sarkin Ruwan, Malam Sa’idu Ibrahim, wanda bai halarci bikin ba saboda lalura, ya zanta da Aminiya a gidansa, inda ya tabbatar da duk abubuwan da aka fada game da ruwan, sannan ya ce mutane daga nesa kan zo musamman don dibar wannan ruwan don yin magani da shi.

Sarkin Rafin ya yi kira ga Karamar Hukumar Kagarko da Gwamnatin  Jihar  Kaduna da ta tarayya su waiwayi tafkin su gyara shi, saboda tarihin da ke cike da tafkin don samar da kudin shiga. Ya ce wurin ziyara ne da ke samun maziyarta daga ciki da wajen Najeriya cikin har da Turawa.

Ya bukaci gwamnati ta gyara ta kuma killace wajen tare da sanya kofa ta shiga don ci gaba da jawo hankalin ’yan yawon bude-ido da kan ziyarci wajen a koyaushe.

Sarkin Ruwan, da sauran ’yan uwansa magada rafin sun nanata kiransu ga karamar hukumar kan bukatar kula da wajen, inda suka ce sun sha kai kukansu a baya amma har yanzu ba a waiwaye su ba.