Categories
Manyan Labarai Saurari Shirye-Shiryenmu

Kwarya-Kwaryar Kasafin Kudin 2021: Wa Zai Amfana?


Gwamnatin Tarayya ta ce kwarya-kwaryar kasafin kudin 2021 da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a ranar Litinin zai fara aiki nan take.

Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari a kan wadanda za su amfana da kasafin na sama da Naira biliyan 900.

Categories
Kananan Labarai

COVID-19: An samu karin samfurin Delta guda 10 a Najeriya —NCDC

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce an samu bullar sabuwar samfurin kwayar COVID-19 ta Delta a jikin kusan mutum 10 a Najeriya.

Babban Daraktan hukumar, Dokta Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake yi wa Ministan Lafiya karin bayani a kan inda aka kwana a yaki da cutar a ranar Litinin.

A cewarsa, “Kawo yanzu mun sami rahoton nau’in samfurin cutar har guda 10. Abin da muke yi shi ne gwajin matafiya da ke shigowa Najeriya. Yawancin wadanda aka samu da ita sun shigo ne ta Legas da Abuja.

“Alamominta sun sha bamban da na wacce muka saba gani, dalilin ke nan da muke bukatar mu kara lura sosai,” inji shi.

Ihekweazu, wanda ya sami wakilcin Daraktan Sashen Sa’ido a kan Cututtuka na Hukumar ya ce yawan masu kamuwa da cutar ya karu da kaso 24 cikin 100, idan aka kwatanta da alkaluman da aka rika samu a ’yan makonnin baya.

Ya ce ya zuwa 22 ga watan Yulin 2021, Najeriya ta tabbatar da kamuwar mutum 22,130 da cutar Kwalara, yayin da 526 daga ciki suka mutu a cikin jihohi 18 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Da yake jawabi, Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire ya ce duniya ta fuskanci karuwar masu kamuwa da cutar a kasashe cikin sa’a 24 da suka gabata sakamakon yaduwar nau’in cutar na Delta.

Ya ce babbar barazanar a yanzu ba ta wuce ta shigo wa Najeriya da cutar daga kasashen da aka fi zuwa daga kasar ba irin su Burtaniya da Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa da Faransa da kuma Turkiyya.

Ministan ya ce lamarin abin damuwa ne matuka kasancewar cutar ta sake bulla a karo na uku, amma duk da haka jama’a na ci gaba da nuna halin halin ko-in-kula da matakan kariyar da ma’aikatan lafiya suke bayarwa.

Categories
Kananan Labarai

Buhari ya sanya hannu kan karamin kasafin N982bn

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan karamin kasafin 2021 na Naira biliyan 892 domin sayen makamai da kuma rigakafin cutar COVID-19.

Ya sanya hannu a kan karamin kasafin ne a ranar Litinin a wani zama da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da sauran manyan hadimansa suka halarta a Fadar Shugaban Kasa.

Sanarwar da kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar ta ce daga cikin karamin kasafin, an ware biliyan N859.3 a matsayin karin a kason da aka ware wa manyan ayyuka a kasafin 2021.

Naira miliyan 123.3 kuma za a yi amfani da su ne domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

Buhari ya jinjina wa Majalisar Tarayya bisa saurin da ta yi wajen kammala aiki tare da amincewa da daftarin karamin kasafin na 2021 da ya aike mata.

Ya kuma yi alkawari cewa bangaren zartarwa zai tabbatar da kammala manyan ayyukan da aka yi kasafin dominsu.

A yayin zaman, Buhari ya kuma rattaba hannu kan sabuwar dokar Hukumar Kula da Asibitocin Kashi na Kasa ta 2021.

Dokar ta 2004 ta amince da kafa asibitin kashi a Jos, Jihar Filato, karkashin kulawar Jami’ar Jos.

Categories
Manyan Labarai

COVID-19: China ta tallafa wa Najeriya da rigakafi 470,000

Gwamnatin China ta tallafa wa Najeriya da allurar rigakafin COVID-19 samfurin Sinopharm har kimanin 470,000.

Jakadan kasar a Najeriya, Cui Jianchun ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, lokacin da ya ziyarci Ministan Lafiya, Osagie Ehanire a Abuja.

Ya ce ana sa ran allurorin rigakafin su karaso Najeriya nan ba da jimawa ba.

Mista Cui ya ce sun ba da tallafin ne don taimaka wa kokarin Najeriya na yaki da cutar COVID-19 da kuma yaukaka dankon dangantaka tsakanin kasashen biyu.

”Wannan kyakkyawan misali ne kan irin alaka me kyau da take tsakanin kasashen biyu,” inji shi.

Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire cewa ya yi Najeriya na maraba da tallafin, musamman kasancewar rigakafin kasar ya yanke tun ranar takwas ga watan Yulin 2021.

Ya ce kasar China na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya, yana mai cewa, “Wannan dangantaka ce mai kama da ta ’yan uwantaka, za mu ci gaba da ririta ta.”

“Bugu da kari, tallafin ba kawai zai taimaka mana ba ne wajen cike gibin da muke fama da shi a bangaren lafiya, har ma da sauran bangarori,” inji Ministan.

Tun daga watan Maris na 2021 zuwa yanzu, Najeriya ta yi wa kusan mutum miliyan hudu rigakafin COVID-19.

Categories
Kiwon Lafiya Kurmi

COVID-19 ta hallaka mutum 10 a Jami’ar Ibadan

Mukaddashin Shugaban Jami’ar Ibadan da ke Jihar Oyo, Farfesa Adebola Ekanola ya sanar cewa akalla mutum 10 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a Jami’ar, a yayin da mutane ke nuna halin ko-in-kula ga matakan kare yaduwar cutar.

Farfesa Adebola Ekanola ya bayyana haka ne a ranar Juma’a 23 ga Yuli, 2021 a lokacin da yake jawabi a taron bidiyo da sashen yaki da COVID-19 na Jami’ar ya shirya wa manyyan jami’anta.

Ya ce ko da yake cutar ba ta yiwa Jami’ar ta Ibadan illa ba, akwai bukatar dalibai da malama su rika daukar kwararan matakan kare yaduwarta a Jami’ar, kasancewar illar cutar ta fi kamari a yanzu fiye idan aka kwatanta da farkon zangon karatu a Jami’ar.

Ya kara da cewa an kafa kwamitin hadin guiwa da za ta tabbatar da ganin dalibai da malaman Jami’ar na bin ka’idojin kare yaduwar cutar ta hanyar wanke hannaye da sanya takunkumi da kuma bayar da tazara.

Ko a makon jiya, mahukuntan Jami’ar Legas sun ba da umarnin rufe dakunan kwanan dalibai da ke karatun digiri na farko, suka kuma umarce da su koma gida bayan gano bullar cutar ta COVID-19 a Jami’ar.

Categories
Manyan Labarai

An soke hawan Sallah a Kano saboda fargabar COVID-19

Gwamnatin Kano ta soke hawan Sallah da dukkan wasu bukukuwa da aka shirya gudanarwa a Jihar yayin bikin Babbar Sallar bana.

Matakin na zuwa ne kusan mako daya bayan Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da COVID-19 ya yi gargadin cewa jihohi shida, ciki har da Kano na cikin barazanar annobar da ta sake barkewarta a karo na uku.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba, a cikin wata sanarwa ranar Litinin ya ce sai dai za a gudanar da Sallar Idi kamar yadda aka saba a dukkan masallatan da ke fadin jihar.

Ya ce daukar matakin na daya daga cikin hobbasar da Najeriya ke yi kamar sauran takwarorinta na Afirka wajen dakile sabon nau’in cutar da ake kira da Delta mai saurin yaduwa.

Garba ya ce hakan ne ya sa hukumomi a jJihohin da aka yi wa gargadin suka yanke shawarar takaita cunkoson jama’a, musamman yayin hawan sallah.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga al’umma ka su ci gaba da kiyaye matakan kariya daga cutar kamar sanya takunkumi da wanke hannuwa a-kai-a-kai da kuma bayar da tazara a lokacin Sallar Idin.

Categories
Kananan Labarai

Babbar Sallah: Jihohi 6 na fuskantar barazanar COVID-19

Gwamnatin Tarayya ta sanya jihohi shida a cikin shirin ko-ta-kwana a wani yunkuri na hana yaduwar cutar COVID-19 a yayin da al’ummar Musulmi suke shirin bukukuwan Babbar Sallah.

Kwamitin yaki da cutar na kasa ne ya sanar da hakan a yammacin Asabar tare da shawartar jihohin da su gudanar da sallolin idi a fili, su takaita tarukan jama’a, su kuma dakatar da shagulgula da hawan sallah.

Shugabanta kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce jihohin Kano da Kaduna da Legas da Filato da Oyo da Ribas da kuma Birnin Tarayya na fuskantar barazanar bazuwar cutar wadda a halin yanzu ake fadi-tashin yakar samfurinta na Delta.

Boss Mustapha ya bayyana cewa “Kwamitin ya sanya jihohin shida da Birnin Tarayya a shirin ko-ta-kwana a matsayin wani bangare na matakan kariya daga yaduwar cutar a karo na uku.”

Ya ce saboda haka, “Ya kamata duk jihohin su inganta yanayin shirinsu kuma su ci gaba da aiwatar da duk wasu matakai da aka tsara.

“Wadannan matakan suna da mahimmanci yayin da muka fara ganin alamun farko na masu kamuwa da cutar a Najeriya”.

Kakakinsa, Willy Bassey ya ce “gargadin” yana nuna cewa ya kamata jihohi su “yi amfani da dukkannin matakan kariyar COVID-19” tare da kara “yin gwaji, ganowa, magani da kuma killace wadanda suka kamu.”

A makon jiya ne NCDC ta ce ta gano wani nau’in kwayar cutar ta Delta mai saurin yaduwa, tare da sanya jami’ai a cikin shirin ko-ta-kwana game da yaduwar cutar.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta ce zuwa ranar Asabar, mutum kusan 169,000 sun kamu da cutar da kuma mutuwar 2,126.

Categories
Rahoto

Halin da maniyyata ke ciki bayan alhazai sun dau harama

A yayin da alhazan wannan shekara suke isa Mina a ci gaba a ayyukan ibada na sauke faran aikin Hajjin bana, maniyyata sun bayyana takaicinsu bisa matakin da kasar Saudiyya ta dauka na takaita aikin Hajjin bana ga iya mazauna kasar.

A ranar Litinin alhazan wannan shekara su kimanin 60,000 za su yi hawan Arfa; A halin yanzu suna riga suka yi Umrah a Haramin Makkah, inda daga bisani za su wuce zuwa Mina kafin su garzaya zuwa filin Arfa —Tara ga watan Zhul-Hijjah.

Tun daga lokacin da hukumomin Saudiyya suka sanar da daukar matakin sake takaita aikin Hajji zuwa mazauna kasar saboda cutar COVID-19 ake ta maganganu game da matakin.

Yawancin maniyyata da suka biya kudinsu a Jihar aknao sun bayyana rashin jin dadinsu da cewa kai tsaye matakin na Saudiyya ya hana su cika burinsu na son sauke farali.

Takaicin maniyyata

Wani maniyyaci wanda bai taba zuwa aikin Hajji ba, Malam Umar Sani, ya bayyana takaicinsa game da hana mazauna kasashen waje aikin Hajji a bana.

Ya ce, “Ai a yi batun rashin jin dadi ma bai taso ba. Dole ne wanda ya yi niyyar yin wannan ibada, in ya samu wannan labarin ransa ya baci. Amma kasancewar mutum babu abin da zai iya yi dole ya hakura.”

Ita ma wata maniyyaciya, Malama Rukayya Abubakar, ta ce lamarin ya sanya ta cikin damuwa saboda shekara biyu ke nan take biyan kudinta na Hajji amma ba ta samun damar tafiya.

“A gaskiya ban ji dadin lamarin ba, domin bara mun biya aka yi batun cutar COVID-19 wanda a lokacin mun san akwi cutar.

“Bana muna ta murna har mun fara shirye-shiryen tafiya domin har an yi mana bita; Sai kawai muka ji wanan bakin labarin.”

Mayar da kudin maniyyata

Bayan sanarwar ta Saudiyya ce Hukumar Jin dadin Alahazai ta Jihar Kano ta kafa kwamiti don fara shirye-shiryen mayar wa maniyyatan kudadensu, kamar yadda shugaban Hukumar, Abba Dambatta ya shaida wa ’yan jarida.

Ya ce za a mayar wa maniyyatan kudinsu ne ta banki da zarar kwamitin ya kammala aikin nasa.

Dambatta ya kara da cewa kwamitin ya kunshi masu ruwa da tsaki daga jami’an Hukumar da kuma jami’an tsaro da kuma wakilai daga Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Hana Cin Hanzi da Rashawa ta Jihar Kano don gudanar da aikin cikin nasara.

Karbar kudi ko jiran badi

Malama Rukayya Abubakar, ta biya kudin Hajji ta hannun Hukumar, amma ta ce ta dauki lamarin a matsayin kaddara, don haka za ta ci gaba da barin kudinta a hannunan Hukumar zuwa badi.

“A gaskiya ba zan karbi kudin nan ba domin idan na karba ma babu abin da zan iya yi da su; Za mu ci gaba da jira zuwa badi mu ga abin da Allah zai yi,” inji ta.

Malam Umar kuma ya ce, “Ni dai kudina zan karba na juya na sa su a wani kasuwancin, ban san abin da zan samu kafin shekarar ba.

“Muna dai fatan badi mu samu mu gudanar da wanann ibada insha Allah.”

Amma wata maniyyaciya mai suna Malama Rabi Ali, ta ce duk da cewa abu ne na rashin jin dadi, amma ta mayar da lamarin ga Allah.

“To dan Adam duk abin da yake yi akwai kaddara. Da ma tun farko Allah Bai yi za mu yi wanann ibada a bana ba.”

Game da batun kudi kuma, Malama Rabi ta ce za ta karba ba domin tana da burin zuwa a badi domin ta samu shiga a sahun farko.

“Kin san yawanci idan za a fara shirye-shiryen tafiyar badi to da mutanen da suka bar kudinsu za a fara.

“Don haka ba zan karbi kudina ba, zan bar su a hannun Hukumar Alhazai har sai Allah Ya kai mu badin mu sake gwadawa.”

Za a yarda da matakin Saudiyya ba?

Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel, ya shaida wa Aminiya cewa ba dole ne a yarda da dalilan da Saudiyya ta bayar na daukar matakin hana baki zuwa aikin Hajjin ba.

Amma ya bayyana cewa wajibi ne a yi wa dokar biyayya.

Sheik Ibrahim Khaleel ya ce, “Duk da cewa ana ci gaba da taruka a duniya na su kwallon kafa da sauransu amma Saudiyyar ta dauki wanann mataki, to wajibi ne a yi wa dokokinta biyayya.

“Kasancewar a kasarta ake gudanar da Aikin Hajjin, ita ce mai ruwa da tsaki a harkar aikin Hajji.

“Abin da ake duba shi ne biyayya da kuma hadin kai don kada a samu baraka. Wannan shi ne tsari na Addinin Musulunci.”

Maniyyatan da COVID-19 ta hana sauke farali

Game da hukuncin maniyyatan da hakan ta faru da su malamin ya bayayan cewa “Dukkaninsu suna da ladan Aikin Hajji matukar ba su yi zage-zage a kan lamarin ba.

Wannan radadin da suke ji na hana sun da aka yi Allah zai ba su lada. Ga ladan aikin Hajji ga kuma ladan hakuri.”

Malamin ya kuma yi kira gare su da su rungumi kaddara, “Su yi hakuri, wani lokaci zai so nan gaba da za su yi. Abin zai wuce.”

Shi ma Limamin Masallacin Juma’a na Masallacin Juma’a na Triumph, Malam Lawan Abubakar, ya bayyana cewa ko ma wane dalili ne ya sanya kasar Saudiyya ta hana baki zuwa aikin Hajji to babu abin da Musulmi zai yi sai hakuri.

Ya bayyana cewa maniyyata za su sami ladan aikin Hajji.

Sunnar Manzon Allah ce

“Manzon Allah SAW ya bayyana cewa wanda ya yi niyyar aikin Hajji, ya tafi hanya aka tare shi, aka hana shi shiga kasar, to ya yanka abin yankansa ya kuma yi aski; Zai zama yana da lada kamar wanda ya yi aikin Hajji.

“Hakan ta faru ga Manzon Allah (SAW). Ya daura niyyar aikin Hajji har ya kusa shigowa Makka sai kafirai suka hana shi shiga; Don haka ya tsaya a wanann wuri ya yanka abin yankansa ya kuma yi aski.”

Har ila yau Malamin ya yi kira ga maniyyatan da hakan ta faru gare su da su yi hakuri kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya yi a wancan lokaci.

“Babu abin da mutum zai yi sai ya yi hakuri domin shi ne abin da Manzon Allah (SAW) ya yi a wancan lokaci da kafirai suka hana shi gudanar da aikin Hajji.

Malamin ya bayyana cewa, “Da Allah Ya ce ya yi hakuri a kan abin da aka yi masa, ba wai Allah yana goyon bayan abin da kafiran suka yi ba [ne], sai dai yana yi ne don a hakurkurtar da Manzon Allah (SAW) a kan abin da ya same shi na rashin jin dadi.”

Yadda masu zirga-zirgar aikin Hajji suka ji

Alhaji Abdurrazak Ibrahim shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Harkar zirga-zirgar Aikin Hajji da Umara, shiyyar Arewacin Najeriya, kuma Shugaban Kamfanin zirga-zirga na Muslima Travel Agency.

Ya bayyana rashin jin dadinsu kan matakin na Saudiyya duba da cewa hakan kai tsaye ya taba kasuwancin ’ya’yan kungiyar.

“Duk da cewa ba mu ji dadin abin ba amma babu yadda za mu yi sai hakuri.

“Saboda harkokin cin abincinmu sun tabu. Sai dai mu yi fatan Allah Ya kai mu badi, kuma mu yi fatan kada wani abu ya sake zuwa ya zame mana matsala.

“Domin idan an duba da farko ai Saudiyyan ta amince da za a yi aikin Hajjin, daga baya ta ce dole sai duk maniyayta sun karbi alluransu zagaye na farko da na biyun da aka tsara; Sai ya kasance wasu kasashen ma yanzu suke karbar allurar ta farko.

“Kuma sun yi lissafi wasu ba za a gama karba ba har lokacin aikin Hajji ya yi, don haka suka dauki wanann mataki.

“To ko ma dai mene ne, muna addu’ar Allah Ya kawo mana karshen wanann matsala,” inji shi.

Wannan dai shi ne karo na biyua jere da maniyyatan suke kudurta zuwa aikin Hajji amma hakan bai yiwu ba.

A shekarar 2020 Saudiyya ta taikata gudanar da Aikin Hajjin ga maniyyata 10,000 da ke cikin kasar sakamakon barkewar cutar COVID-19.

Categories
Manyan Labarai

An fara shirye-shiryen Aikin Hajjin bana a yanayin COVID-19

Maniyyata sun fara shiga birnin Makkah na kasar Saudiyya domin fara shirye-shiryen ibadar Aikin Hajjin bana.

Wannan dai shine karo na biyu da ake takaita yawan masu gudanar da ibadar saboda kaucewa yaduwar annobar COVID-19.

A bana dai mutum 60,000 wadanda aka yi wa cikakkiyar rigakafin cutar kuma mazauna kasar ne za a kyale su yi aikin, cikin fatan da take yi na ganin cewa an sami nasarar rashin samun wanda ya kamu da ita kamar a bara.

Wani maniyyaci a Masallaci Harami na Makkah
Wani maniyyaci a Masallaci Harami na Makkah

A bana dai an zabi mutanen da zasu gudanar da ibadar ne ta hanyar yin kuri’a, yayin da Musulmai da dama daga kasashen waje aka sake haramta musu zuwa.

Bayan dibarsu a manyan motocin safa-safa, an kai maniyyatan Masallacin Harami, tuni suka fara Dawafi a dakin Ka’aba.

Mafi yawa daga cikinsu dai suna amfani da laima don kare kansu daga zafin rana.

Wata maniyyaciya tana amfani da laima don kare kanta daga zafin rana.
Wata maniyyaciya tana amfani da laima don kare kanta daga zafin rana.

“Duk bayan sa’a uku, mutum 6,000 suna shiga su yi Dawafi idan suka zo,” kamar yadda Kakakin Ma’aikatar Aikin Hajjin Saudiyya ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Aikin Hajji dai na daya daga cikin ibadu mafi tara mutane masu yawa a duniya, inda ko a 2019 mahajjata miliyan biyu da rabi ne suka gudanar da aikin.

Wani maniyyaci tsaye a kusa da Dutsen Arafat yana addu'a
Wani maniyyaci tsaye a kusa da Dutsen Arafat yana addu’a

Ibadar kuma na daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar da ake bukatar kowanne Musulmi mai hali ya yi, akalla sau daya a rayuwarsa.

An tsaurara matakan kariya a bana

An dai zabi mutum 60,000 din ne daga cikin kimanin 558,000 da suka nemi gudanar da aikin bayan yin kuri’a, kuma wadanda aka yi wa cikakkiyar rigakafin ’yan tsakanin shekara 18 zuwa 65 ne kawai za su yi aikin.

Wasu jami'an tsaro na gadin masu ibadar.
Wasu jami’an tsaro na gadin masu ibadar.

“An raba maniyyatan ne zuwa rukuni-rukuni, inda kowanne rukuni ya kunshi mutum 20 kacal, domin takaita yawan cudanyar mutane,” inji Mohammed Albijawi, Sakataren Ma’aikatar Aikin Hajjin.

Ya zuwa yanzu dai, sama da mutum 507,000 ne suka kamu da cutar a kasar inda 8,000 daga ciki kuma suka rasu.

An kuma yi wa sama da mutum miliyan 20 rigakafi a kasar da take da mutane miliyan 34.

Aikin Hajjin bara dai na daya daga cikin mafiya karancin mutane da aka taba gudanarwa a cikin shekaru masu yawa, inda mutum 10,000 ne kacal suka yi ibadar.

Ba a dai samu rahoton kamuwa da cutar a sanadiyyar aikin ba a bara, kasancewar hukumomi sun dauki matakan kariya iri-iri.

Babban kalubalen aikin a bana dai shine yadda za a kammala ibadar ba tare da an sami sabbin kamuwa da cutar ba. (AFP).

Categories
Kasashen Waje

Gobara ta kashe mutum 64 a wurin killace masu COVID-19

Akalla mutum 64 ne suka mutu bayan wata gobara ta tashi a wurin killace masu cutar COVID-19 a Kudancin kasar Iraki, kamar yadda gwamnatin kasar suka sanar a ranar Talata.

Kazalika, Sashen Lafiya na gundumar Dhi Qar ya tabbatar da jikkatar mutum 50 sanadiyyar gobarar.

  1. Buhari zai gana da duk Sanatoci 109 a daren Talata
  2. Hisbah ta kama mutum biyar da ake zargi da Luwadi a Kano

Gobarar dai ta tashi ne a ranar Litinin a asibitin Al-Hussein da ke birnin Nasiriyah a yankin Dhi Qar, mai tazarar kilomita 375 daga babban birnin kasar, Bagadaza.

Ma’aikatan asibitin sun tabbatar da gobarar ta ritsa da majinyata da kuma ma’aikatan asibitin sama 60.

Sun ce gobarar ta kone dakin jinyar marasa lafiyar da ka iya daukar majinyata 100.

Tuni dai Firaministan kasar, Mustafa Al-Kahdimi ya ba da umarnin gudanar a bincike tare da gano musababbin tashin wutar.

Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa ko binciken da ya gano abin da ya haifar da gobarar.

Ko a  watan Afrilu ma an sami irin wannan gobarar, da ta tashi a babban birnin kasar na Bagadaza wacce ta kashe sama da mutum 80.

Shugaban kasar, Barham Salih ya bayyana gobarar a matsayin wata ‘mummunar kaddara’. (NAN).