✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tagwaye sun rasu a daidai rana da yanayin da aka haife su a Jos

Wadansu tagwaye masu suna Isah Muhammad da Dauda Muhammad masu shekara 22 da suke zaune a garin Jos fadar Jihar Filato, sun yi mutuwar da…

Wadansu tagwaye masu suna Isah Muhammad da Dauda Muhammad masu shekara 22 da suke zaune a garin Jos fadar Jihar Filato, sun yi mutuwar da ta bai wa kowa mamaki da dare ranar Litinin  da ta wuce. Tagwaye da suke zaune a Unguwar Rikkos a garin Jos, sun rasu ne a daidai ranar da aka haife su da kuma fasalin yadda aka haife su a kuma daidai lokacin da aka haifes u, ba tare da wata doguwar jinya ba.

Da yake yi wa Aminiya bayani kan lamarin, yayan tagwayen, Alhaji Musa Yaro Rikkos ya ce, wannan rasuwa ta tagwayen ta zo da abin al’ajabi. Domin kusan yadda Allah Ya kawo su duniya haka Allah Ya karbi abinSa.

Ya ce,  lokacin da aka haifi tagwayen shekara 22 da suka gabata, an fara haihuwar Muhammad Isah ne a gida, sai haihuwar ta rikice aka nemo mota aka dauki mahaifiyarsu zuwa asibiti, kafin a isa asibitin, sai aka haifi na  biyun Muhammad Dauda.

Ya ce, da Allah Ya tashi karbarsu wanda aka fara haifa Muhammad Isah, babu dogon rashin lafiya a ranar Litinin din sai jikinsa ya canja sai aka kira likiti don  ya kara masa ruwa a gida.

Ya ce, an fara kara masa ruwan ke nan ba a dade ba, sai Allah Ya karbi abinsa, ya rasu da misalin karfe 8:30 na dare.

“Da na fito na samu  dan uwan tagwaicinsa  Muhammad Dauda a waje tare da abokansa sai na ce musu ya kamata mutuwa ta zamo darasi a gare ku. Ana gaya maku kuna kin yarda saboda kuruciya, ga wane Allah Ya yi masa rasuwa. Sai na tafi gida na kwanta. Muhammad Dauda yana  nan a waje har karfe 10:30  na dare, sai ya ce bari ya je ya kwanta. Ya shiga daki ya kwanta, ba a dade ba, sai wadanda suke kwana tare da shi suka ji numfashinsa ya fara sama-sama, suka je suka taso ni. Na zo na dauko mota a guje na dauke shi zuwa asibiti da misalin karfe 11:00 na dare kafin in karasa asibitin Allah Ya yi masa rasuwa, muka shiga ciki likita ya tabbatar da rasuwarsa,” inji shi.

Ya ce, abin mamaki tagwayen  an haife su ne a ranar Litinin shekara 22 da suka gabata, kuma suka rasu a ranar Litinin a daidai lokacin da aka haife su. Kuma wanda aka haifa a gida, ya rasu a gida, dayan da aka haifa a hanyar asibiti shi ma ya rasu a kan hanyar zuwa asibiti.

Ya ce, babu abin da za su ce kan wannan al’amari, domin sun san kowanne mai rai mamaci ne,  idan lokaci ya yi. Don haka sai ya yi addu’ar Allah Ya jikansu Ya gafarta masu kura-kurensu.