✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tagwayen amaren Zamfara sun shiga mako na 3 a hannun masu garkuwa

Yan garkuwar sun ki amsar Naira miliyan 11 don sakinsu Ranar wata Litinin, makonni biyu da suka gabata ne al’ummar garin Dauran, Karamar Hukumar Kauran…

Yan garkuwar sun ki amsar Naira miliyan 11 don sakinsu

Ranar wata Litinin, makonni biyu da suka gabata ne al’ummar garin Dauran, Karamar Hukumar Kauran Namoda a Jihar Zamfara suka wayi gari da alhinin sace wasu ’yan tagwayen budare, Hassana da Hussaina ’ya’yan Bala Dauran da ’yar uwarsu, Sumayya Abubakar; yayin da a daren Lahadi wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane don amsar kudin fansa ne suka shigo garin, suka yi awon gaba da su.

Lamarin ya zama abin tattaunawa a cikin jama’a, ganin cewa wadannan ’yan matan marayu ne da aka sanya ranar aurensu amma suka fada cikin musibar, wadda ba za su taba mantawa da ita ba har karshen rayuwarsu. Haka kuma sun tausaya, ganin cewa a ranar Asabar ma an sace wasu mutanen uku a garin, abin da ya tabbatar da cewa an sace mutane shida ke nan a kwana biyu, maza uku, mata uku.

Aminiya ta ziyarci iyalan wadanda aka yi garkuwa da su domin sanin hakikanin lamarin, inda daya daga cikin wadanda dangin suka aminta ya yi magana da wakilinmu kuma ya nemi a sakaya sunansa; ya bayyana halin da tagwayen suke ciki a hannun masu garkuwar da abin tausayi da zubar da hawaye. Ya ce tagwayen amaren sun bayyana masa cewa suna cikin hali mai muni, inda daya daga cikinsu ma ba ta da lafiya. Suna cikin kunci da rayuwa mara tabbas, sun yi kira ga iyayensu da su karbo su dawo gida haka nan.

Ya ce “Hassana da Hussaina tagwaye ne. Kafin rasuwar babansu, ya haifi ’ya’ya 16, su ne ne na hudu a jerin ’ya’yansa kuma mahaifiyarsu ita ce uwargida, ta rasu a shekarar 2013, shekara biyar da ta gabata. Mahaifin nasu ya yi aikin gwamnati na tsawon shekara 35, inda ya yi ritaya a shekarar 2015 kuma har ya rasu a 2017 ba a biya shi hakkinsa. Wannan dalili ne ya sanya tagwayen suka kawo yanzu ba a yi masu aure ba. Hakkin nasa ne muka jira, domin a yi masu kayan daki na al’ada da aka saba.”

Ya ci gaba da cewa, “Da muka tabbatar wannan kudin ba zai samu ba don Gwamnatin Zamfara ba ta biyan kudin Fansho da Garatitu, sai muka hadu a dangi muka yanke shawarar cewa a ranar 29 ga Disambar bana za mu aurar da yaran, muka fada wa manemansu, inda ta hannuna aka bayar da sadakin daya.

“Aure ya matso, sun fitar da kayan ankonsu, muna nan tare da su a Gusau. Zan tafi Kauran Namoda, babban yayansu ya ce in tafi da su, za su je garin Dauran domin kai ankon Hassana. Haka aka yi kuwa, na tafi da su na sanya su mota. Kwana daya sai na samu labarin cewa an sace ’ya’yan kakansu guda biyu maza, wato Mas’udu Dauran. Na dauki matata mu je can mu yi jaje, bayan mun dawo Lahadi aka ce min ban san ’yan tagwaye na can ba, ya ban dawo da su Gusau ba? Na ce na zaci sun bar can. Karfe biyun daren ranar, DPO na Dauran ya kira ni yake gaya mini cewa barayi sun shiga gidan da yayarsu Sumayya take, sun balle gidan ta hanyar sare kofar da diga, da karfin tsiya suka  tafi da yaran, su uku.

“Wai barayin sun samu labarin yaran sun zo garin, an fada masu cewa ’ya’yan Ministan Tsaro ne, Mansur Dan’ali. Barayin sun yi zaton yaran kamar ’ya’yan wani babban mutum ne saboda Allah Ya ba su zati da sura mai kyau.

“Ina cikin wadanda ke magana da masu garkuwa da su, muna magana ta lalama har yanzu sun fara zagina, na daina magana da su tun jiya (Asabar), domin sun ce mu ba su Naira miliyan 80 sun rage mana Naira miliyan 20, domin da farko Naira miliyan 100 da suka yanke. Halin da ake ciki ke nan, duk wanda ya fada maka cewa an saki yaran ko gwamnati ko wani dan siyasa ya sanya bakinsa a harkar, karya ce yake yi.”

Game da halin da suke ciki kuwa, ya bayyana cewa: “Tagwayen ba su da lafiya, muna hasashen yaran nan ana ajiye da su ne wajen garin Birnin Magaji. Har yanzu ba wani mataki da aka dauka game da kwato yaran su shida da ake rike da su. Yaran dukansu ’yan dangi daya ne, an dauki uku maza a ranar Asabar, aka dawo ranar Lahadi aka dauki uku mata. Alhaji Mas’ud ya ce zai ba su Naira miliyan 3 su sakar masa yaransa sun ki. Mahaifin daya yarinyar ya ce zai ba su Naira miliyan 3, mu kuma za mu hada Naira miliyan 5 su zama Naira miliyan 11 domin fansar Hassana da Hussaina da sauran yara hudu, amma sun ki aminta da hakan. Sun ce sai dai mu ba su Naira miliyan 230, wato Sumayya kan Naira miliyan 100, ’yan tagwaye kan Naira miliyan 80, yaran Mas’ud kuma Naira miliyan 50.

“Ta bangaren jami’an tsaro kuwa, mu ba mu ga wani hobbasa da suke yi kan kwato mana yaranmu ko daukar wani mataki ga abin da ya same mu ba,” inji shi.

Hajiya Sha’awa Usamatu, ita ce kishiyar mahaifiyar ’yan tagwaye. Ita ce ke tarbiyyarsu tun suna ’yan shekara biyu da haihuwa, bayan rasuwar mahaifiyarsu har yanzu da suka kai shekara 19. Ta shaida wa Aminiya cewa: “Yayansu ne ya sanar da ni cewa an sace yaran. Da na ji labarin na rude sosai har sai da na fita hayyacina, na fita gida da gudu sai da aka kamo ni a waje; domin ban san inda za ni ba. Tun san da aka kama su kullum sai na yi magana da masu garkuwa da su, na roke su da su tausaya wa yaran. Na ce marayu ne, su sako su amma ina ba su ji ba. Nakan kuma yi magana da yaran, a lokacin da na fara magana da su na zaci sun gudo ne don sun kira da wata waya da ba ta su ba. Sai suka fada mini cewa lambar ta ’yan garkuwa da mutanen ce. Har yanzu ba wani labari na kubutarsu. Muna fatan gwamnati ta sanya mana hannu ga kubutar yaranmu.”

Abdurrashed Bala dan shekara 28, wanda shi ne babba a gidan su ’yan tagwayen kuma suna zaune a Gusau tare da su, ya kara wa Aminiya bayani game da satar yaran. “Lokacin auren yaran ne ya zo kusa, suna yawon rabon dinkin ankonsu ne suka tafi garin Dauran. Abinka da tsautsayi sai ba su dawo ranar da suka tafi ba, sai suka sauka gidan yayarsu Sumayya, wadda ’yar uwarmu ce a bangaren mahaifinta da mahaifiyarmu. A can suka kwana aka sace su tare. Makwabtansu ne suka kira mu kan abin da ya faru da daren Lahadin da ta gabata.

“Mun sanar da masu garkuwan cewa za mu ba su Naira miliyan biyar sun ki aminta. Ba abin da za mu yi sai addu’a. Don Allah mutane su daina yada jita-jita, suna cewa an sako yaran nan, tun da hakan ba gaskiya ba ne,” a cewar Abdurrashed.

Abdurrazak Hamza, shi ma dan uwansu ne, ya ce a lokacin da aka kira shi aka gaya masa cewa an sace yaran, ya tafi da sauri ya sanar da ’yan sanda domin sanin halin da ake ciki. Ya ce ya shiga damuwa sosai, musamman lokacin sanar da shi cewa Hassana ba ta da lafiya kuma mutanen nan sun ki yarda su karbi abin da suke da shi suka ki kai ’yar uwarmu asibiti. Abin ba dadi.

Shi kuwa Shamsu Mas’ud, shi ne yayan yara biyu maza da aka fara daukewa, wanda sai da ya yi artabu da barayin kafin su sace su, inda abin ya kai ga sai da suka sare shi da kuma kokarin harbinsa, ya gudu.

“Ranar Assabar da karfe 12:30 na dare muna kwance muka ji ana bugun kofar gida da kokarin balle ta. Muka tashi cikin gidanmu gaba daya sai na ce su waye? Aka ki amsawa. Na ce ko barayi ne? Suka ce “eh, ina Alhaji?” Muka ce ba ya nan. A haka suka kalle kofa daya, suka shigo suka tarar da ni a tsaye. Dayan ya rike ni, sauran suka wuce a daya kofa gidan. A haka na samu sa’ar kayar da wanda ya rike ni, ya sare ni amma na tafi da gudu. Ya yi harbi bai same ni ba, ina ji suna fadin Shamsu ne ya gudu.

“Tun da suka shiga gidan sun kira wayar Alhaji suka ji kararta a dakinsa suka shiga suka dauko Hajiya, kawai suka tarar gidan kowa ya gudu, Alhaji da sauran mata biyu da yaran gida. Sun bugi Hajiya sai ta fada masu inda Alhaji yake, ta ce ba ya nan, yana asibiti ba lafiya. A nan ne suka dauki yaran nan guda biyu,

Abdurrahaman Mas’ud da Ibrahim Mas’ud da suka gani hannunta. Ta kasa fita ne ta bi saura don yaran suna barci a lokacin da barayin suka shigo kuma tana jinyar ’yar autan gidan, wadda ke biye da yaran a haihuwa,” a cewar Shamsu.

Ya kara da cewa masu garkuwar akalla sun kai su 10 dauke bindigogi da adduna da guduma da sauran kayan balle kofa. Ya ce sun zo da mota bas, wasu a kan babura. Alhaji Abubakar Yusuf (Abu Asko) shi ne mahaifin Sumayya ’yar shekara 20. Ya ce diyarsa ta daina kwana gidan aurenta saboda mijinta ba ya nan kuma tana tsoron masu garkuwa da mutane. Shi ya sa ta dawo gida amma da wadannan ’yan uwanta suka zo ne ta koma don su kwana tare.

Mutanen sun zo sun balle kofa suka tafi da yaran da karfi. Sun nemi in ba su Naira miliyan 150, na gaya masu cewa ban taba ganin wadannan kudin ba a tsawon rayuwata. Tun da abin ya faru mun kasa barci, muna cikin tashin hankali.

Jami’in hulda da jama’a na hukumarar ’yan sanda a Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu a zantawarsa da Aminiya dangane da al’amarin ya ce: “In kana bibiyar abubuwa, yau fiye da kwana goma muka fitar da takardar bayanan matakin da muke dauka, abin da ya bazu ko’ina. Mun fitar da bayani ko Channel sun yi amfani da shi. Idan ba wani sabon bayani aka samu ba, ba za mu fito mu yi magana ba. In akwai sabon abu, kamar kwato yaran ko kama wasu da ke da alaka da sace yaran, ba wai maganar sace yaran ba; don an wuce maganar satar yaran.”

Har zuwa hada rahoton nan dai ba wani bayani na sakin dukkan wadanda aka yi garkuwa da su, wato mutum shida, uku mata, uku maza.