Da Dumi Dumi

Tagwayen da aka haifa a manne suna samun kula a Asibitin ABUTH

Tagwayen da aka haifa manne a Unguwar Hayin Kadage da ke Tudun Wadan Soba a Jihar Kaduna sun fara samun kula a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Mahaifin tagwayen Malam Muhammad Bashir wanda aka fi sani da Gambo, ya ce ’yan uwa da abokan arziki ne suka ba da shawara cewa su kai yaran asibitin don haka suka kai su wannan asibiti, kuma sakamakon buga labarin a jarida sai dan majalisarsu na wakilai ya tura wakilansa asibitin don a ga yadda za a taimaka. “Haka shugaban Karamar Hukumar Soba ya turo wadansu jami’an asibiti domin ganin yadda za a yi da sauran mutane wadansu ma ban sansu ba duk suna zuwa suna ganawa da jami’an asibitin, don haka tun da muka zo babu abin da aka ce mu bayar tsawon wannan lokacin sai dai kawai abinci da muke saya amma ba ma sayen komai, kuma yaran suna samun kula sosai,” inji shi.

Babbar ma’aikaciya mai kula da dakin kwanciyar jarirai, (Metron), wadda ta bayyana sunanta da Misis Abdulmumini, ta ce mahaifin yaran shi ne ya kawo tagwayen asibiti da kansa, ganin yadda suke a manne sai asibitin ya rike su don kula da su da kuma shirin taimaka musu.

“Daya daga cikin manyan likitocinmu kuma kwararre a kan aikin fida Dokta Shola Doye ne shugaban kula da wadannan tagwaye da suke manne, kuma yanzu haka jami’an sun hada duk wani bayanai na shirin ba su taimako,” inji ta.

Kakakin Asibitin, Musa Mu’azu, ya ce babu wanda zai iya yin bayanin kan wani shiri sai shugaban kula da tagwayen don haka a yi hakuri ya kammala shirinsa nan da dan lokaci kadan.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya