Da Dumi Dumi

Takaddama kan kwallo ta ci ran matashi

Marigayi Nuhu Adam
Marigayi Nuhu Adam

Takaddama kan ra’ayin wasan kwallon kafa a tsakanin unguwanni biyu, ya yi sanadiyar kashe wani matashi a garin Madalla na Jihar Neja yayin da aka jikkata mutum biyu.

Lamarin ya faru ne bayan dadaddiyar adawa kan lamarin a tsakanin matasan Unguwar Fada inda yawancin mazauna wurin ’yan asalin garin ne da na Unguwar Liman, inda ake daukar mafiya yawan mazauna wuri a matsayin baki.

Wani dan uwan wanda aka kashe mai suna Lawan Adam, ya ce marigayi dan uwan nasa Nuhu Adam mai shekara 21, ya rasa ransa ne bayan wani matashi mai suna Rabi’u wanda yanzu haka ba a san inda yake ba ya auka masa a kan wani titi da ya raba unguwannin biyu. Ya ce dan uwansa ya je wani shago ne don karbar wayar mahaifiyarsa da ya bada caji, sai kawai ya ji an riko kafadarsa daga baya, kuma bayan ya juya don ganin wane ne, sai wanda ake zargin ya daba masa wani makami a kirji ya gudu.

“Dan uwana ya yi kokarin gudowa gida don tsira da ransa, amma sai ya fadi kasa a hanya saboda raunin ya riga ya jikkata shi, wadansu sun kai shi wani asibiti a can ne aka tabbatar musu cewa ya rasu,” inji shi.

Aminiya ta zanta da daya daga cikin wadanda aka raunata mai suna Adamu Abdulhamid, wanda bangarorin biyu suka tabbatar da cewa ba ya cikin rigimar, illa dai akasi aka samu kasancewar ya fito ne daga unguwa daya da wanda ake zargin ya aikata kisan.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “A ranar da aka yi rigimar na dawo gari bayan Sallar Isha’i ban san abin da ya faru ba. Sai kawai na hadu da wadansu matasan Unguwar Liman lokacin da na ratso ta wurin. Da farko sun kai min sara a kai da adda, ina kan shafa wajen sai wani ya yi yunkurin daba min kwalba a ciki, tarewar da na yi ne, na yanke a hannu.

“Na gudu amma sai suka yi ta bi na ina ta fadi-tashi har karfina ya kare na fadi a wani waje. Ganin yadda jini ya malala a wajen ne suka dauka na mutu, sai suka koma tattaka ni da wani ya haska su da fitala sai suka gudu, a nan ne Allah Ya ba ni ikon tashi na shiga wani gida, daga wajen aka kai ni wani asibti aka yi min magani,” inji shi.

Da aka tuntubi Babban Jami’in ’yan sandan garin Madalla CSP Adamu Danjuma, ya tabbatar da faruwan lamarin, ya ce an fara bincike tare da neman wadanda ake zargi da hannu a lamarin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya