✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddama ta kaure kan hana shan taba a fina-finan Faransawa

An gabatar da bukatar neman a han sshan taba a fina-finan Faransawa, inda aka tafka takaddama kan hotunan da ake nunawa na masu bankar hayakin…

An gabatar da bukatar neman a han sshan taba a fina-finan Faransawa, inda aka tafka takaddama kan hotunan da ake nunawa na masu bankar hayakin taba a tsakanin taurarin ’yan wasan da ake nunawa a alllunan silma.

Wannan manufa ta yunkurin hana Faransawa shan tabar wani dan majalisar dattijai ne ya gabatar da ita, wato nadne grelet Certenas, a wani zaman majaisar inda aka tafka muhawara kan yadda za a taimaka wa Faransawa su daina zukar taba.

Da aka bijiro da wani bincike, wanda ya nuna cewa kashi 70 cikin 100 na sababbin fina-finan Faransawa kan nuna akallla tauraron dan wasa guda na zukkar sigari, shi ya sa dan majalisar dattijan ya zargi masu shirya fina-finan da kawata shan taba a matsayin dabi’a mai kyau.

 “Suna nuna cewa shan taba ba komai ba ne, har ma ta kai ga sun kanbama taba a matsayin kyakkyawan abu, musamman a wajen kananan yara da matsa ’yan shekara sha wwani abu, wadanda suka fi kallon wadannan fina-finai a shafukan intanet,” kamar yadda ta jajirce a kan hakan.

Ita kuwa minister Lafiya Agnees Buzyn, kwararriyar likita, wadda ta sha fafutikar kara frashin taba daga Yuro bakwai zuwa 10 wato daidai da Dala 11 da senti 80 (Naira 4,248) cewa ta yi, “ta bayar da cikakken ggoyon baya” ga sanata.

“Ban fahimci muhimmancin taba sigari a fina-finan Faransawa ba,” a cewarta, inda ta yi rantsuwar daukar “tsauraran matakai” don kawo karshen “rashin nuna illar taba a shafukan zumunta da fina-finai.”

‘Kyutata tarbiyya’

Tsawon lokaci an dade an danganta yaduwar cututttukan da za a iya shawo kansu, sanadiyyar baza shan taba a silmar Faransawa da ke jan hankalin matasan kasar.

A shekarun baya-bayan nan gwamnatoci da suka gabata sun fara ne da haramta shan taba a bainar jama’a, sannan aka fito da kwalayen taba dauke da sakonni.

“Da fina-finai za su daina nuna mutane na zukkar gtaba, sai kawai muhimmatu wajen kawar da miyagun laifuka kamar fyade da sace-sace da kwayoyi da sauran dabi’un fandarewa ta yadda za mu samu zaman lumana a wannan duniya,” kamar yadda yake kunshee a ra’ayin  jaridar La Republikue des Pyrenees.

Shi kuwa masanin Falsafa mai sharhi a kan al’amura Raphael Enthwoen sukar lamiri tsarin ya yi, oinda ya ce “cussa tarbiyya a silma tamkar zuba lemun kwalbar Coca-Cola ne a giyar mai kimar daraja a faransa ta  Chateau-Lafite.”

Wani dan siyasa, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Florian Philippot na jam’iyyar ’yan kishin kasa ta National Front, shi ma auna lamarin ya yi, tare da cewa, manufar kwace karan sigari da jaruman fina-finai na nuni da cewa al’ummar Faransa “na kara kaimin tursasar matsin lamba.”

Sauran masu sharhi kuwa bijiro da tambaya suka yi kan ko za a haramta shan tabar a sauran fina-finan kasashen waje, ta yadda gwamnati za ta samu damar kawar da sha’awar zukar tabar dungurunggum, har ma a kundin tarihin fina-finan.

Saboda nuna damuwa kan wannan takadddama da muwarar haramta taba a fina-finai ta haifar, wani gidan rediyo a Faransa ya baje hotunan jiga-jigan jaruman fina-finan Faransa rike da taba a tsakanin yatssunsu. Jaruman da suka fito a matsayin kabusu sun hada da Jean-Luc Godard a fim dinsa na black-and-white New Wabe classic Breathless, wanda ya yi tashe, sai kabusu Jean-Paul Belmondo  a majiginsa na  breakout , inda ya fito a matsayin babban mai laifi, da kuma Alain Delon, tsohon jigo a fim din Le Cercle Rouge.

Indiya wadda ta fi kowace kasa a duniya hada-hadar shirya fina-finai ta fito da tsarin yaki da shan taba, inda take fito da sakonnin gargadi a kowane lokaci jarumi ya kunna taba.