✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddama tsakanin Gwamna da shugabannin kananan hukumomin Oyo ta kazanta

Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON), reshen Jihar Oyo ta ce, ba za ta saurari kwamitin binciken da Gwamnatin Jihar ta kafa kwanan baya…

Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ta Kasa (ALGON), reshen Jihar Oyo ta ce, ba za ta saurari kwamitin binciken da Gwamnatin Jihar ta kafa kwanan baya ba, domin bincikar asusun ajiyar kananan hukumomi 33 da Yankunan Raya Kasa (LCDA) na jihar ba.

Kungiyar ta umarci dukkan shugabanni da sakatarori da kansiloli da masu lura da ayyuka a kananan hukumomin jihar su yi watsi da gayyatar da kwamiti zai yi musu domin aikin Ofishin Babban Mai Binciken Kudi na Jihar ne ya yi wannan bincike ba haramtaccen  kwamiti da aka kafa don cimma burin siyasa ba.

Bayanin haka na kunshe ne a  wata takardar sanarwa dauke da sanya hannun Shugaban Kungiyar ALGON, Cif Abass Alesinloye da aka raba wa ’yan jarida a ranar Lahadi da ta gabata. Kungiyar ta yi tir da rusa Hukumar Zabe ta Jihar (OYSIEC) da Gwamnatin Jihar ta yi inda ta ce, alama ce ta rashin adalci.

Da yake kare matakin Gwamnati kan wannan lamari Babban Sakataren Labarai na Gwamnan Jihar, Mista Taiwo Adisa ya ce, Gwamna Seyi Makinde ya yi aiki bisa dokar kasa ce wajen kafa kwamitin. Ya ce Gwamna ya ja kunnen Kungiyar ALGON ta daina kirkirar abubuwan da za su iya janyo koma-bayan al’amuran ci gaba a jihar “Domin tabbas doka za ta yi aiki a kan duk wanda ya kawo hargirtsi ga ayyukan wannan kwamiti,” iniji shi.

A ranar 1 ga Yuli ne Gwamna Makinde ya kafa kwamitin mai wakilai 7 a karkashin Shugabancin Mai shari’a S. L. Popoola (mai ritaya), inda Gwamnan ya umarci kwamitin ya binciki asusun ajiyar kananan hukumomi 33 da yankunan raya kasa (LCDA) 35 daga watan Janairu zuwa Mayun bana domin kwato kudade da kadarori daga hannun duk wani jami’i ko mutum da ya yi awon gaba da su.