Da Dumi Dumi

Takaddama tsakanin Majalisa da Fulani kan dokar kiwo a Oyo na kara zafi

Sarkin Fulanin Jihar Oyo Alhaji Saliu Kadiri yana yi wa daruruwan makiyaya jawabi a wajen babban taron da suka yi a ranar Talata a garin Igangan
Sarkin Fulanin Jihar Oyo Alhaji Saliu Kadiri yana yi wa daruruwan makiyaya jawabi a wajen babban taron da suka yi a ranar Talata a garin Igangan

A yayin da Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta dage kan kafa sabuwar dokar kiwon dabbobi a jihar don kawo karshen rikicin manoma da makiyaya, su kuwa Fulani a jihar sun nuna rashin amincewa da dokar ce inda suka yi barazanar zuwa kotu don hana majalisar kafa ta, saboda sun ce takurawa ce gare su, kuma lokacin zamanantar da kiwo irin na kasashen da suka ci gaba bai yi ba.

Fulanin sun kin amincewa da sabuwar dokar ce a wajen wani babban taro da suka yi a garin Igangan a ranar Talata da ta gabata. Sarakunan Fulani da daruruwan jama’arsu daga sassan Jihar Oyo ne suka halarci taron na Igangan.

Da yake yi wa manema labarai bayanin sakamakon taron Sarkin Fulanin Jihar Oyo Alhaji Saliu Kadiri, ya ce, “Mun yanke shawarar zuwa kotu idan aka tilasta kafa wannan doka mai dauke da biyan harajin ba gaira ba dalili ga makiyaya da tarar dimbin kudi ga dabbobin da suka lalata amfanin gona. Idan da gaske ake yi to kuwa su ma manoma sai a tilasta musu kange gonakinsu, idan tura ta kai bango babu abin da za mu yi sai zuwa kotu domin ta hana Majalisar Dokokin kafa dokar da za ta takura mana. A matsayinmu na ’yan Najeriya masu biyayya ga dokokin kasa kuma a matsayin Fulani da muke kan gaba wajen yawan kuri’ar zabe a Jihar Oyo, muna kira ga gwamnatin jihar ta samar da rugagen kiwon dabbobi maimakon kafa irin wannan doka da sunan zamanantar da kiwo a jihar,” inji shi.

Ya ce sun lura cewa, gwamnati tana nemansu ne kawai a lokacin zabe. Saboda haka suke rokon gwamnati ta sanya su cikin jerin ’yan kasuwa su rika samun rancen kudi da hakkokinsu da kula da lafiyar dabbobinsu da karatun ’ya’yansu. Kuma suna so a sanya ido sosai a kan bakin makiyaya da suke kwararowa daga wajen kasa.

An fara takaddamar ce mako uku da suka gabata lokacin da Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta kira taron masu ruwa-da-tsaki kan kafa sabuwar dokar kiwo a jihar inda shugabannin kungiyoyin Fulani a Kudu maso Yamma karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Gan-Allah ta Kasa, Alhaji Sale Bayari suka fice daga zauren taron domin nuna rashin amincewa da dokar.

ADVERTISEMENT

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Mista Debo Ogundoyin, ne ya shugabanci zaman taron a wancan lokaci inda masana daga jami’o’i  da sarakuna da kungiyoyin manoma suka halarta.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya