✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddamar fili tsakanin Jami’ar Jos da mutanen Narakuta  ta tayar da hankali

Takaddama kan mallakar fili a tsakanin Jami’ar Jos da al’ummar Narakuta da ke makwabtaka da jami’ar, ta jawo tashin hankali a garin Jos, tare da…

Takaddama kan mallakar fili a tsakanin Jami’ar Jos da al’ummar Narakuta da ke makwabtaka da jami’ar, ta jawo tashin hankali a garin Jos, tare da yin sanadin rasa ran mutum daya  mai suna Babangida Saudi Adam, tare da kona gidaje hudu da mota daya a ranar Lahadin da ta gabata.

Rikici ya taso ne lokacin da ma’aikatan da Hukumar Jami’ar Jos, ta tura suke aikin fitar da iyakar filin sai matasan garin suka fito, suka nuna rashin amincewarsu. A wannan hali ne wani jami’in tsaro ya harbi Babangida Saudi Adam, inda rasa ransa.

Wannan abu da ya faru ya tayar da hankalin matasan garin. Sai da jami’an tsaro suka yi iyakar kokarinsu, kafin su shawo kan lamarin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ASP Ubah Gabriel ya tabbatar da faruwar rikicin, kuma ya tabbatar da rasuwar mutum daya tare da kona gida 4 da mota daya a rikicin. Amma ya ce tuni an shawo kan rikicin.

Wakilinmu ya gano cewa filin, asalinsa na wani kamfanin yin jan bulo ne, mai suna Nigerian Bricks and Clay Products Limited da ke karkashin tsohon kamfanin hakar kuza na Najeriya.

A wata sanarwar da jami’ar ta fitar dauke da sa hannun Mataimakin Babban Magatakardar Jami’ar, Wilson Yale ta ce jami’ar  ta sayi filin ne daga kamfanin yin jan bulo ta hannun Hukumar Sayar da Kadarorin Gwamnati (BPE).

“A matsayinmu na masu bin doka da oda sai muka kai wannan magana ga Gwamnatin Jihar Filato. Kuma gwamnatin ta kafa kwamiti na mutum 10 don duba wannan lamari, bayan da kwamitin ya kammala aikinsa ya mika rahoto ga gwamnatin, ta fitar da takardar hukuma da ta tabbatar da cewa wannan fili, mallakar Jami’ar Jos ne,” inji sanarwar.

A bangaren Kungiyar Ci-Gaban Al’ummar Narkuta-Babale Bayan Doka, ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Filato da Hukumar Jami’ar Jos, su tsaya su duba maganganun da suke kan wannan fili, kafin jami’ar ta cigaba da aikin fitar da iyakar filin.

Kungiyar ta yi kiran ne a wata sanarwa da ta raba wa ’yan jarida dauke da sanya hannun shugabanta, Alhaji Ibrahim Shu’aibu Muhammad.

Sanarwar ta yi kukan cewa a matsayinsu na makwabtan jami’ar, jami’ar ta yi watsi da su kuma ta datse wa al’ummar garin hanyar samun ruwan sha. Kuma ba ta daukar ’ya’yansu su yi karatu ko ba su aiki.